Dokta Hauwa Musa: Burina a samu wadatattun likitoci mata
Dokta Hauwa Abdullahi Musa kwararriyar likitar mata ce da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, sannan malama ce a Jami’ar Bayero ta Kano, inda take koyarwa a bangaren aikin likita. A yanzu haka ita ce Shugabar Asibitin Get-well da ke Jihar Kano. Ta ce babban burinta shi ne an samu wadatattun likitoci […]
Dokta Hauwa Abdullahi Musa kwararriyar likitar mata ce da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, sannan malama ce a Jami’ar Bayero ta Kano, inda take koyarwa a bangaren aikin likita. A yanzu haka ita ce Shugabar Asibitin Get-well da ke Jihar Kano. Ta ce babban burinta shi ne an samu wadatattun likitoci mata ’yan Jihar Kano.
Tarihin Rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Dakta Hauwa Musa Abdullahi. An haife ni a unguwar Durumin Iya cikin birnin Kano cikin shekarar 1968. Na fara karatun firamare a Makarantar Firamaren Shahuci, inda na karasa a Firamaren Gidan Galadima a shekarar 1987. Daga nan na tafi sakandiren a Makarantar ’Yan mata ta Jogana. Bayan na kammala sai na sami shiga Jami’ar Bayero inda na karanta fannin likitanci, sai dai na karasa wannan karatun nawa a Jami’ar Jos. Daga baya na koma na yi karatun digirina na biyu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano daga shekarar 2005 zuwa 2010. Lokacin da na kammala digirin farko a shekarar 1995 sai na fara aiki a Asibitin kwararru na Murtala Mohammad a matsayin guduu (House manship). Da shekara ta kewayo sai na yi aikin hidimar kasa a wannan dai asibiti na Murtala. Ina nan ina aiki sai na zama likita mai kula da mata. Sai a shekarar 1998 aka ba ni rikon asibitin kula da masu cutar yoyon fitsari da ke Titin Gidan Zoo. Na zauna a wannan asibiti na yoyon fitsari tsawon shekara guda, daga bisani aka sake mayar da ni Asibitin Murtala. Bayan na karo karatu a matakin digiri na biyu a shekarar 2010 sai aka mayar da ni Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano a matsayin kwararriyar likitar mata, inda nake aiki a can har zuwa wannan lokaci, haka kuma ina koyarwa a Jami’ar Bayero.
Nasarori
Alhamdulillah ina ganin shi kansa karatun likita da na yi a matsayina na mace kuma Bahaushiya a matsayin nasara gagaruma, duk da cewar na samu goyon bayan mahaifina wanda shi ya zama wuka da nama a harkar karatuna, kasancewar yana da ra’ayin karatun ya sa ya toshe kunnuwansa a kan abin da mutane ke fadi, a kan karatun ‘ya mace. Kin san a wancan lokaci ba a waye da barin ’yan mata su ci gaba da karatu zuwa jami’a ba, domin ina iya tunawa mu biyu ne muka ci gaba da karatu bayan mun gama sakandire.
Haka na samu nasara inda har na rike asibitin masu yoyon fitsari sukutun. Haka na zamanto likitar matar Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso. Har ila yau a sha’anin aikina na samu ziyarar kasashe da dama da suka hada da Ingila da Afrika ta Kudu da Senegal da Saudiyya. Ina shirye-shiryen zuwa kasar Medico. A yanzu kuma ga shi har Allah Ya taimake mu mun bude namu asibitin mai zaman kansa a cikin birnin Kano.
kalubale
Dama ita rayuwa cike take da kalubale musamman ga ma’aikaciya mace, saboda yanayin aiki da kuma hulda da jama’a; ga kula da gida ga kuma yara, sannan a gefe guda ga fita aiki, aiki mai wahala irin na likitanci. Idan kika dauki farkon farawa aikin mutum har kwana muke yi ko kuma mu yini a asibiti. Babu shakka mazajenmu sun yi hakuri da mu kwarai da gaske.
A wasu lokuta za ki ga abokan aiki maza suna nuna mana irin halin nan na nuna cewa mu mata ne, ba za mu iya aikin ba, ba wai don ba mu iya aikin ba sai don kasancewarmu mata. Kai tun lokacin da nake karatun likita nake fuskantar kalubale saboda kasancewata mace a cikin ajinmu, amma da yake Allah Ya nufa sai ga shi mun yi mun gama cikin nasara.
Iyali
Tun ina jami’a na yi aure a shekarar 1988. Sunan maigidana Alhaji Musa Mamman. Ina da ‘ya’ya hudu. Babban cikinsu yanzu ya kammala digirinsa ya yi bautar kasa, sannan na biyun yana jami’a. Ita ma ta ukun tana karatu a Jami’ar Bayero. Sai ta hudun ita ce a halin yanzu take a matakin karatu na sakandire. Alhamdulillah da taimako tare da gudummawar maigidana na samu nasarar kulawa da iyalina, sai dai fatan Allah Ya kara taimaka mana Ya kuma sa mu gama da duniya lafiya.
Buri
Babban burina a yanzu shi ne, na ga na zama farfesa. Haka kuma ina so na ga mun samu wadatattun likitoci mata a Jihar Kano, kasancewar muna da karancinsu kwarai da gaske. Hakan ya sa a bangarenmu na kungiyar likitoci mata muke ziyartar makarantun ’yan mata, inda muke wayar musu da kai a kan muhimmancin aikin likita tare da nuna musu irin darassa da za su fi dagewa da yin kokari a cikinsu, wato darussan kimiyya don ganin sun kai ga samun cin jararrabawa. Haka kuma a gefe guda mukan nuna musu irin romon ladan da za su samu a wannan aiki, kasancewarsa na aikin ceton rai.
Abin da take son a tuna ta da shi
Ina so a duk lokacin da aka tashi tunawa da ni a tuna ni a wata da ta taimaka wa al’ummarta. A kullum ina fata na ga mutum ya zo da bukatarsa ko wata matsalarsa na ga na yi masa maganinta. A kullum ina gaya wa duk wanda nake tare da shi cewa kada mutum ya zama ya ki taimaka wa duk wanda zai iya taimakawa.
Shawara ga mata
Ina shawartar ’yan uwana mata da su tsaya wajen kula da karatun ’ya’yansu, musamman ma ’ya’ya mata wadanda kullum muke burin su fito su karanci aikin likita. Za ki samu mutane sun kai matansu asibiti sai su ce ba sa son likitoci maza su duba matan nasu, ga shi kuma muna da karancin likitoci mata. Kin ga ashe idan har muna son magance wannan matsala to sai mun bar ’ya’yanmu mata sun yi karatun likita. Haka muna kira ga gwamnati da masu hali a cikin al’umma da su rika tallafa wa dalibai masu karatun likita, kasancewar wadansu na son yin karatun sai dai kuma iyayensu ba su da karfin da za su dauki nauyin karatun nasu.
Ina shawartar mata da zarar sun ji alamun wasu cututtuka su rika gaggawar zuwa asibiti domin neman magani ba wai sai ciwo ya ci ya cinye mutum ba. Misali idan kika dauki cutar dajin mama ko na bakin mahaifa abu ne da ya kamata mata su rika zuwa asibiti tun farko-farkon ciwon kafin ya zama ya fi karfin magani. Ga shi a yanzu Alhamdulillah gwamnatin Jihar Kano ta samar da hanyoyi masu sauki na gwaje-gwajen ciwon dajin. Haka ita ma matsalar haihuwa kamata ya yi ma’auratan da ke da wannan matsalar su rika zuwa asibiti don neman hanyoyin da za a bi a shawo kan matsalar. A nan ina so na wayar da kan ma’aurata cewa rashin haihuwa ba matsalar mace ce ita kadai ba, a wasu lokutan matsalar daga maza take, amma sai ki ga an dauki laifi kacokan an dora a kan matar ba tare da zuwa asibiti an gano inda matsalar take ba.