Dokta Mariya Bunkure: Fafutuka wajen sama wa mata ilimi tun daga tushe

Tauraruwar tamu ta yau kwararriyar likita ce da ta samu kwarewa a didiginta na daya da na biyu duka a fannin

Dokta Mariya Bunkure: Fafutuka wajen sama wa mata ilimi tun daga tushe

Dokta Mariya Mahmoud Bunkure

Watakila la’akari da irin nasarorin da ta samu a rayuwarta, za a iya cewa Dokta Mariya Mahmoud Bunkure ta ciri tuta musamman a tsakanin takwarorinta mata, kai har ma da mazan.

Tauraruwar tamu ta yau kwararriyar likita ce da ta samu kwarewa a didiginta na daya da na biyu duka a fannin likitanci.

A matsayinta na mai fafutukar samar wa mata da ’yan mata ilimi a yankin da ta fito, Dokta Mariya ta taka rawa iri-iri wajen ganin an samu sauyi a adadin matan da suke samun ilimi.

Watakila ma wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ga dacewarta da zama Kwamishina a Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Jihar.

Cikin shekarun da ba su wuce uku ba, Dokta Mariya ta yi kokari wajen kawo sauye-sauye na ci gaba a manyan makarantun Jihar.

Karatu da gwagwarmayarta

Dokta Mariya ta samu digirinta na farko ne a bangaren aikin likitanci (MBBS), da kuma na biyu a kan Lafiyar Al’umma (Public Health), duk daga Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).

Ta halarci tarukan kara wa juna sani da dama, kuma mamba ce a kungiyoyin likitoci da dama, ciki har da Kungiyar Ma’aikatan Jinya ta Afirka ta Yamma (WACP) da Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) Kungiyar Mata Likitoci ta Najeriya (MWAN) da sauransu.

La’akari da irin gudunmawarta a harkokin ci gaban al’umma, Tauraruwar tamu ta samu kyaututtuka da lambobin yabo da dama daga kungiyoyi, hukumomi da ma daidaikun mutane.

A shekarar 2018, Babbar Kwalejin Lafiya ta Najeriya ta ba ta lambar girmamawa ta “fellow” a Matsayin Kwararriyar Likita (FMCFM).

A matsayinta na Kwamishina a Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Jihar Kano, Dokta Mariya ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kafa Kwalejin Lafiya a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano (YUMSUK) da kuma giggina sabbin azuzuwan karatu da ofisoshi a kusan dukkan manyan makarantun Jihar.

Kazalika, Kwamishinar ta kuma tabbatar da kirkiro sabbin kwasa-kwasai tare da fara karatun digiri na biyu da kuma sake tantance wadanda ake yi a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da Jami’ar Kimiyya da Fasaha (KUST) da ke Wudil da YUMSUK da kuma Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos