Dokta Nasir Sani Gwarzo 2

Mutane na tsoron yin musafaha da juna Tun lokacin da gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ta samu wani dan kasar Laberiya da ya rasa ransa sakamokon kamuwa da cutar Ebola a karshen makon da ya gabata, mutanen jihar suka shiga tashin hankali da fargabar kamuwa da cutar.Kodayake gwamnatin ta bayyana cewa tana gudanar da […]

Dokta Nasir Sani Gwarzo 2

Mutane na tsoron yin musafaha da juna

Tun lokacin da gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ta samu wani dan kasar Laberiya da ya rasa ransa sakamokon kamuwa da cutar Ebola a karshen makon da ya gabata, mutanen jihar suka shiga tashin hankali da fargabar kamuwa da cutar.
Kodayake gwamnatin ta bayyana cewa tana gudanar da bincike don tabbatar da sahihancin lamarin amma tuni labarin mutumin da ya rasa ransa ya rika yaduwa kamar wutar daji a tsakanin mutanen jihar.
Labarin shigowar cutar Ebola jihar Legas ya sanya mutanen jihar sun daina yin musafaha da duk wanda ya yi kokarin mika musu hannu don gaisawa, yayin da wadansu suke gudun hada jiki da mutum a cikin ababan hawa don kada su kamu da cutar.
Jama’a da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyan cewa bayanin da likitoci suka rika yi na cewa ana iya kamuwa da cutar ta hanyar taba jikin mai ita ko kuma yin hulda da shi ta kud-da-kud shi ya sa suka dauki matakin kare kansu ta hanyar nisanta hada jiki da mutane ’yan’uwansu, walau a wurin aiki ko motar haya ko kasuwa ko kuma duk inda akwai cunkoson jama’a.
Malam Garba Abubakar wanda lamarin ya auku da shi a cikin motar haya ya ce, ‘Abin mamaki na shiga mota daga Ikeja zuwa Ogba, sai na lura wanda yake zaune kusa da ni ba ya son mu hada jiki da shi, na ga yana ta matsa wa kansa ba ya so jikina ya taba shi, da na taba jikinsa sai na ga ya yi tsaki, da na tambaye shi, sai ya ce yana jin tsoron kamuwa da cutar Ebola ne saboda likitoci sun ce ana kamuwa da ita ta hanyar hada jiki da wanda ya kamu da cutar.’
Shi kuwa Mista Sunday Papoola cewa ya yi, ‘Na je kofar wani kamfani, sai na mika wa masu gadin wurin hannu don mu gaisa, sai kawai na ga kowa ya ki miko mini hannu, sai na tambaye su me ye dalilin da ba su son gaisawa da ni sai suka ce sun daina gaisawa da jama’a saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.’
Shi ma Jim Ikayike da ke sayar da wayar salula a kasuwar Ikeja cewa ya yi, ‘Jiya da na je kasuwa, ina mika wa makwabtana da muke kasuwanci hannu don mu gaisa sai na ga kowa ba ya son yin musafaha da ni, da na tambayi dalili sai wani abokina ya ce mini ban san cewa yanzu mutane sun daina yin musafaha ba saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola?. Da na yi bincike a kasuwarmu sai na gano cewa ko da abokin huldar kasuwa ne ya zo ba a bashi hannu a yi musafaha da shi don ba a san daga inda ya zo ba.’
Hakazalika Aminiya ta gano cewa ma’aikata na tsoron a tura su filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.
Wani jami’i da ke aiki a sashen kasuwanci na wata jarida wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ‘Yanzu ma’aikatanmu suna tsoron zuwa filin saukar jiragen sama su yi aiki, da ka ce wane tafi filin jiragen sama ka dauko jarida sai ka ga yana bata rai ba ya son zuwa saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.’ In ji shi.
Mutane da dama da Aminiya tattauna da sun sun nuna farbarsu tare da tsoron yaduwar cutar a jihar.
Malam Isa Faskari cewa ya yi, ‘Gaskiya tun lokacin da muka ji labarin cewa wani dan kasar Laberiya ya mutu sakamokon cutar hankalinmu da na iyalanmu ya tashi domin ba mu san abin da zai faru ba a gaba. Saboda haka nake kira ga gwamnati da ta dauki matakan da suka dace wajen ganin cutar ba ta yadu a nan ba’.
Ita ma Alaja Fatimoh Ajimobi ta yi kira ga gwamnati da kada ta boye komai don yin hakan zai iya cutar da jama’a. ‘Ni abinda nake so shi ne gwamnati ta yi gaskiya. Kada a mayar da abin siyasa ko kuma bangaranci. Ya kamata gwamnati ta yi gaskiya kuma ta dauki matakan da suka kamata wajen maganin cutar tun kafin ta yadu a tsakanin al’umma.’ Inji ta.
Malam Isyaka Halliru  ya bayyana cewa, ‘Ni tunda na ji labari sai na dimauce na shiga fargaba hankalina ya tashi don ba mu san ta inda cutar za ta fara ba. Ta yiwu ma cutar ta bulla a Najeriya amma hukumomi suke yi mana rufa-rufa. Saboda haka muna kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen tunkarar lamarin ba tare da bata lokaci ba.’

Ba laifi kin yin musafaha saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola   –Ustaz Suraj
Abubakar Haruna, Daga Legas

Wani fitaccen mai wa’azin musulunci mai suna Ustaz Muhammad Suraj Abdullahi ya ce wadanda suke kin yin musafaha saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola ba su yi laifi ba a addinin musulunci.
Ustaz Suraj wanda mai wa’azi ne a kungiyar Izala reshen jihar Legas, ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya.
Ya ce, ‘addinin musulunci, kamar yadda ya zo a Hadisai na Buhari da Musulim, Manzon Allah ya umarce mu da mu rika yi wa juna sallama tare da yin musafaha. Namiji zai gaisa da dan’uwansa namiji, mace ma za ta gaisa da ’yar’uwarta mace, amma dangane da binciken da malamai suka yi na cewa duk wata cuta tana da musabbabin da yake kawo ta. Kamar cutar Ebola da likitoci suka bayyana cewa ana iya kamuwa da ita ta hanyar taba jikin wanda ya kamu da ita, haka zalika ma kungiyar Izala ta yi bayanin a kafar sadarwarta ta facebook cewa likitoci sun ce za a iya kamuwa da cutar ta hanyar yin musafaha da wanda yake dauke da ita, saboda haka aka yanke hukuncin cewa kin yi musafaha ya zama lalura ke nan. Saboda haka idan mutum ya ki yin musafaha da wanda yake ganin yana dauke da cutar bai yi laifi ba.’
Ya ci gaba da cewa, ‘amma mutum ya sani cewa yin musafahar ya fi rashin kin yi. Kuma ba a son mutum ya rika nuna kyama ga wanda yake dauke da wata cuta saboda ba shi ya dora wa kansa ba, Allah ne ya dora masa. Kuma bai kamata mutane su rika yin isgilanci da haka ba. Saboda haka idan ka san mutum ba ya dauke da cutar amma kuma ka ki mika masa hannu ba ka yi daidai ba, musulunci bai ce haka ba.’
Ya bayyana cewa, kone gawarwakin wadanda suke dauke da cutar Ebola ya saba wa addinin musulunci. ‘Bai hallata  a kone gawa addinin musulunci ba don kawai tana dauke da wata cuta, dole sai dai a binne ta kuma ma ai akwai kayayyakin da likitoci suka tanada da idan aka yi amfani da su wajen binne gawar wanda yake dauke da cutar ba za a kamu da ita ba, to me zai hana a yi amfani da irin wadannan kayayyakin a rika binne gawarwakin da su?’ In ji shi.

Masu cin naman daji sun firgita a Jihar Binuwai

Daga Hope Abah, Makurdi da Bashir Musa Liman

Tsoron kamuwa da cutar Ebola, wanda aka samu rahoton ta kama wani likita a Jihar Legas ta sanya masu cin naman daji sun firgita a Jihar Binuwai.
Al’ummar jihar wadanda yawancinsu manoma ne, sun saba da cin namun daji iri daban-daban, inda suke kawo su gida daga gonakinsu, ko kuma su saya a wuraren sayar da abinci.
Wadansu daga cikin al’ummar jihar da ke zaune a Makurdi babban birnin jihar sun bayyana wa wakiliyar Aminiya cewa ba za su kara cin naman daji ba sai an samu tabbacin bacewar cutar a Najeriya, inda wadansu kuma suka ce babu abin da zai hana su cin naman daji.
Tiblumun Micheal cewa ya yi, ya dakatar da saye ko cin naman daji a gidansa har sai yadda hali ya yi. “Mun samu labarin cutar ba ta da magani, kuma za a iya kamuwa da ita ta hanyar cin naman daji, hakan ya sanya na bayar da umarnin dakatar da saya da kuma cin naman daji a gidana.” Inji Micheal.
Kate Akande kuwa ta ce za ta daina cin naman daji ne kawai don tsoron kamuwa da cutar Ebola, inda za ta koma cin kifi. Ta ce: “Ya zama wajibi in daina cin kowane irin nau’in nama, musamman ma naman daji.”
Ita kuwa Terhemen Ugondo ba ta yarda za a iya daukar cutar Ebola ta hanyar cin beran Masar ko zomo ba, sai dai ta hanyar cin jemagen da ke dauke da cutar. “Ni kam zan ci gaba da cin naman daji kamar su beran Masar da zomo. Sai dai ba zan ci jemage ba, kasancewar shi ne yake dauke da cutar, zan kuma ba masu cinsa shawara su daina a halin yanzu.” Inji ta.
Etim Akpabio kuwa cewa ta yi  ba za ta daina cin naman daji ba duk da cewa batun cutar ya firgita jama’ar jihar, musamman ma mazauna Makurdi babban birnin jihar.  “Ba zan daina cin naman daji ba, ko yau ma na ci beran Masar.” Inji Akpabio.
Wakiliyar Aminiya ta rawaito masu sayar da naman daji a kasuwanni da kantunan sayar da abinci na fama da karancin ciniki makonni biyu da suka wuce, wato tun lokacin da aka samu rahoton bayyanar cutar Ebola a kasar nan.
Hankalin jama’ar jihar ya kara tashi a makon jiya bayan da aka yada jita-jitar bayyanar cutar Ebola karamar Hukumar Logo. Hakan ya sanya limaman coci suka bukaci jama’a su ci gaba da bin matakan hana kamuwa da cutar.
Darakta a Sashin Lafiyar Jama’a na Ma’aikatar Lafiya a Jihar Benuwai Dokta Peter Kumba ya karyata jita-jitar kwantar da wani mai cutar Ebola a Asibitin Mkar da ke karamar Hukumar Gboko, ya ce batun “ba shi da tushe ballantana makama”.
Kumba ya ce mutumin da aka rika yada jita-jitar ya kamu da cutar Ebola an kawo shi daga Jihar Taraba ne, kuma yana fama da ciwon hanta ne.
“Batun an samu yaduwar cutar Ebola a Jihar Benuwai ba gaskiya ba ne. Akwai wani marar lafiya da ke fama da ciwon hanta da aka kwantar asibitin Mkar da ke karamar Hukumar Gboko, wanda aka kawo daga Jihar Taraba, wannan marar lafiya ya rika aman jini, amma ba hakan na nufi yana da dauke da cutar Ebola ba.” Inji shi.