Dokta Zagbayi ya yi alkawarin samar da Hukumar HYPPADEC

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Dokta Shem Zagbayi Nuhu kuma dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben cike gurbi na dan Majalisar Dattawa a karshen wannan wata, ya yi alkawarin tabbatar da samar da Hukumar Kula da Al’ummun Kogunan Madatsun Samar da Wutar Lantarki (HYPPADEC), kamar yadda takwararta ta raya yankin Neja-Delta ke yi.Dokta Shem Zagbayi […]

Dokta Zagbayi ya yi alkawarin samar da Hukumar HYPPADEC
Dokta Zagbayi ya yi alkawarin samar da Hukumar HYPPADEC

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Dokta Shem Zagbayi Nuhu kuma dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben cike gurbi na dan Majalisar Dattawa a karshen wannan wata, ya yi alkawarin tabbatar da samar da Hukumar Kula da Al’ummun Kogunan Madatsun Samar da Wutar Lantarki (HYPPADEC), kamar yadda takwararta ta raya yankin Neja-Delta ke yi.
Dokta Shem Zagbayi ya bayyana haka ne a tattaunawarsu da wakilinmu a Minna, inda ya ce duk da rashin isasshen lokaci zai nemi goyon bayan takwarorinsa da suka fito daga jihohin Kogi da Kwara da Kebbi da Neja domin kwalliya ta biya kudin sabulu, idan ya samu nasarar zuwa majalisar.
dan takarar ya ce muddin hukumar ta fara aiki, matasa da dama za su samu aikin yi a jihohin sannan tattalin arzikin al’ummarsu zai bunkasa, kuma a rage yawan asarar rayuka da dukiyoyin da ake yi duk shekara.
Ya lashi takobin dorawa daga inda marigayi Sanata dahiru Awaisu Kuta ya tsaya ta bin sawun batun a majalisar.
Ya yi kira ga matasa su daina rayuwar da ba ta dace ba, musamman bangar siyasa.Ya ce bangar siyasa ta saba wa manyan addinan kasar nan, kuma halaye ne na rashin tarbiyya, ta kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.