Dokubo ya yi alkawarin zubar da jini in Jonathan ya fadi a 2015

Tsohon shugaban ’yan ta’addan Neja-Delta, Mujahid Asari Dokubo ya yi barazanar zubar da jini idan Shugaban Jonathan bai yi tazarce a zaben shekarar 2015 ba.Dokubo wanda ke magana a gidan talabijin na Channels, ya ce “An riga an kammala da batun shekarar 2015; Goodluck Jonathan ne zai zama Shugaban kasa a 2015. Ya alla sun […]

Dokubo ya yi alkawarin zubar da jini in Jonathan ya fadi a 2015

Mista Asari DokuboTsohon shugaban ’yan ta’addan Neja-Delta, Mujahid Asari Dokubo ya yi barazanar zubar da jini idan Shugaban Jonathan bai yi tazarce a zaben shekarar 2015 ba.
Dokubo wanda ke magana a gidan talabijin na Channels, ya ce “An riga an kammala da batun shekarar 2015; Goodluck Jonathan ne zai zama Shugaban kasa a 2015. Ya alla sun yi takara ko ba su yi takara ba, Goodluck Jonathan ne zai zama Shugaban kasa,” inda ya ce zai zauna a shirye domin tada hankali idan bukatar haka ta taso.
Ya ce, “Idan sun ce jinin kare da biri za su cakuda a cikin ruwa a kan titi, a cikin jini a kan titi, a cikin gishiri a kan titi, za mu taimaka musu su dulmuya a cikin jinin.”
Dokubo yana nuni ne da kalaman da aka jingina ga Janar Muhammadu Buhari a watan Mayun bara, wadda bahaguwar fassara ce kan maganar da ya yi da Hausa. An ruwaito Buhari yana gargadin cewa rikici na iya barkewa a shekarar 2015 idan aka maimaita magudin da ake zargin an tafka a zaben 2011.
Dokubo ya ce “Ba za mu kyale Goodluck (Jonathan) shi kadai ba, zan shiga PDP” kuma ku sani “Za mu yi yaki, saboda wannan yaki babu gudu babu ja da baya.”
Ya ce da’awar cewa yana kare mutane ko gwamnatocin da ya ci gajiyarsu ne “cin mutuncinsa ne.”
“Wannan cin mutunci ne, suna karya ne, kuma za su ci gaba da karya su mutu suna karyarsu,” inji shi.
Dokubo ya ce “Shekaruna 50, na yaki dukkan gwamnatoci. A lokacin fafatawar 12 ga Yuni, ina sahun gaba, ba ribar da na samu.”
Ya ce, ya yi mubayi’a ga Shugaba Jonathan ne saboda shi dan kabilar Ijaw ne, kuma yana ta’assubanci ne “saboda so, so ne, amma son kai ya fi.”
Dokubo ya musanta cewa yana cin gajiyar dimbin albarkatun mai da ke yankin Neja-Delta, inda ya zargi biloniyoyin ’yan kasuwa Aliko Dangote da Femi Otedola kan amfana daga abin da nasa ne da ’ya’yansa da zuriyarsa.