Dolaye biyu
Bahadeje ne da Banufe sun je yin itace a daji, kowa ya yo nasa itacen sosai ya dora a kai. Da suka dawo gari, har za su shiga gida ke nan sai Bahadeje ya ce ya manto addarsa a daji. Sai ya koma da itacen nasa a kai, ya je neman addar; shi kuma Banufe […]
Bahadeje ne da Banufe sun je yin itace a daji, kowa ya yo nasa itacen sosai ya dora a kai. Da suka dawo gari, har za su shiga gida ke nan sai Bahadeje ya ce ya manto addarsa a daji. Sai ya koma da itacen nasa a kai, ya je neman addar; shi kuma Banufe ya tsaya jiransa da itacen nasa a kai. Shi ne mutane ke ta gardamar wanda ya fi dolonci a tsakaninsu.
Daga Iliyas Idris Fahad Suleja