Dole a bar Al-Bashir ya halarci taron Majalisar dinkin Duniya – Sudan
kasar Sudan ta tsaya kai da fata cewa Shugaban kasar Omar al-Bashir yana da ’yancin hakartar taron Majalisar dinkin Duniya da za a gudanar a birnin New York na kasar Amurka a makon gobe, duk da gargadin da Amurka ta yi cewa ba za a marabce shi ba, sakamakon tuhumarsa da laifin haddasa yaki.Ma’aikatar Harkokin […]
kasar Sudan ta tsaya kai da fata cewa Shugaban kasar Omar al-Bashir yana da ’yancin hakartar taron Majalisar dinkin Duniya da za a gudanar a birnin New York na kasar Amurka a makon gobe, duk da gargadin da Amurka ta yi cewa ba za a marabce shi ba, sakamakon tuhumarsa da laifin haddasa yaki.
Ma’aikatar Harkokin kasashen Waje ta kasar Sudan ta ce, Amurka a matsayinta na kasar da ke daukar bakuncin taron ba ta da ’yanci a bangaren shari’a na ta hana wani wakilin wata kasa da mamba ce a Majalisar dinkin Duniya halartar taron majalisar.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Sudan ya buga sanarwar ta Ma’aikatar Harkokin Wajen kwana daya bayan da jami’an Amurka suka tabbatar da cewa Shugaba al-Bashir ya rubuta takardar neman biza don zuwa taron.
Kotun Duniya tana tuhumar Shugaba al-Bashir da laifin cin zarafin dan Adam dangane da yakin da ya gudana a yankin Darfur. Kuma an zarge shi da aikata miyagun ayyuka ciki har da kisan kai da fyade da halaka fararen hula a yankin.
A ranar Litinin da ta gabata Jakadan Amurka a Majalisar dinkin Duniya, Samantha Power ta ce shirin tafiyar ta Shugaba al-Bashir na iya zama “abin takaici” kuma “babban abin da bai dace ba.”
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Marie Harf ta ce Amurka tana la’antar “duk wani yunkuri” na al-Bashir domin halartar taron Majalisar dinkin Duniya. Sai dai ta ki cewa komai kan ko za a ba shi biza.
Sudan ta ce ma’aikatar harkokin wajen ta nuna “kin amincewarta da damuwarta” kan kalaman na Harf da kuma Power. Kuma ta ce Amurka ba ta da baki ko goyon bayan doka ko karfin gwiwar siyasa da za ta yi “huduba” kan ’yancin dan Adam ga wani, inda ta kawo misali da mamayar Iraki da Amurkan ta yi a shekarar 2003.
kasashen Afirka da dama ciki har da Najeriya sun bar Shugaba al-Bashir ya shiga kasashensu, duk da cewa kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi ta kiraye-kirayen kada su yi haka.