Dole a dauki mataki a kan Rasha – Hillary Clinton
A ranar Talatar da ta gabata ne ‘yan takarar neman shugabancin kasar Amurka su biyar a karkashin jam’iyyar Democrat, suka gudanar da mahawararsu ta farko gabanin zaben da za a yi a badi, inda daya daga cikin ’yan takarar, Hillary Clinton, ta ce dole a dauki mataki a kan Rasha.Har ila yau, an tafka muhawara […]
A ranar Talatar da ta gabata ne ‘yan takarar neman shugabancin kasar Amurka su biyar a karkashin jam’iyyar Democrat, suka gudanar da mahawararsu ta farko gabanin zaben da za a yi a badi, inda daya daga cikin ’yan takarar, Hillary Clinton, ta ce dole a dauki mataki a kan Rasha.
Har ila yau, an tafka muhawara mai zafi tsakanin tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen kasar wadda Kuma uwargidan tsohon Shugaba Bill Clinton ce da wani sanata mai cin gashin kansa, Bernie Sanders, game da manufar Amurka a Siriya da dokokin mallakar bindiga da kuma tattalin arzikin kasa da kuma farmakin da Rasha take kai wa a Siriya.
Misis Clinton ta ce lokaci ya yi da za a tashi tsaye, ga abin da ta kira cin zalin da shugaban Rasha ke yi.
Ta ce: “Ina tunanin yana da muhimmanci Amurka ta fito fili ta bayyanawa Putin cewa ba za a amince ya kasance cikin Siriya ba inda yake haifar da karin rudani, da yi wa jama’a ruwan bama- bamai a madadin Shugaba Assad.”