Dole a dawo daga rakiyar siyasar ubangida wajen zaɓen shugabanni — Shekarau

Ya yi Allah wadai da cewa ‘yan siyasa na kawo cikas ga ayyukan gwamnati a Najeriya ta hanyar yin watsi da ƙa’idoji.

Dole a dawo daga rakiyar siyasar ubangida wajen zaɓen shugabanni — Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce dole ne a dawo daga rakiyar siyasar ubangida domin zaɓen shugabanni nagari.

Sanata Shekarau ya kuma yi Allah wadai da yadda wasu ‘yan siyasa ke dakile kwararar romon dimokuradiyya ga ayyukan gwamnati a Nijeriya ta hanyar yin watsi da ƙa’idojin gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu.

Shekarau ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da ƙasida mai taken, ƙalubalen gudanar da harkokin siyasa daga jami’an gwamnati’ a wani taro na kwanaki 4 da aka shirya wa mambobin hukumar yi wa ma’aikata hidima ta ƙasa (NASC) da manyan jami’an gudanarwa na majalisar tarayya da aka fara a Abuja ranar Juma’a.

Shekarau ya ce maganganun da shugabannin siyasa ke yi a bainar jama’a don burge magoya bayansu ya saɓa wa ƙa’idojin aikin gwamnati.

Ya ƙara da cewa, naɗe-naɗen siyasa da ba su da muhimmanci kuma waɗanda ba su zama dole ba, na ƙara yawan kashe kuɗaɗe da hakan yana haifar da ruɗani a ayyukan jama’a.

A cewarsa, batun shugabanci shi ne babban jigon nasara na kowace ƙungiya ko al’umma.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka