Dole a faɗa wa Shugaban Ƙasa gaskiya — Ndume
Zan iya cewa na ma riga Shugaban APC [Ganduje] shiga APC, in ji Ndume.
Ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, wanda aka sauke daga muƙamin Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar ya ce, bai yi nadama kan kalamansa da suka kai ga tsige shi daga muƙamin ba.
Sanatan ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi da ’yan jarida a karon farko bayan matakin da majalisar ta ɗauka a kansa.
- Za mu rage mace-macen mata wajen haihuwa — Gwamnan Kano
- Zanga-zanga: Gwamnati ta tsaurara tsaro a iyakokin Najeriya
Ya ce, bayan abin da ya faru, ya zauna ya sake yin nazari kan kalamansa, inda ya ce, “Kuma ban ga wani aibi ba kan abin da na faɗa.
“Na nemi taimakon shugabannin ƙasar nan da aminai su sake nazari kan kalaman, su faɗa min ko abin da na faɗa ba haka ba ne, ko na yi kuskure, amma dukkansu sun ce ba su ga wani aibi ba kan abin da na fada,” in ji Sanata Ndume.
A cewar Ndume “Ina ganin babu abin da na faɗa wanda ba daidai ba, don haka ina nan a kan kalamaina.”
Sanatan ya yi watsi da tayin da aka yi masa na Shugaban Kwamitin Harkokin Yawon Shaƙatawa, yana mai cewa ba ya da wata ƙwarewa kan sha’anin yawon buɗe -ido.
Game da Jam’iyyarsa ta APC wadda ta buƙaci a tsige shi, Sanata Ndume ya ce, “Na ɗauki wannan a matsayin ƙaddara, domin Allah ne Ya ba ni wannan muƙami.
“Ba takara na yi ba, aka naɗa ni matsayin Mai Tsawatarwa, ba takara na yi aka ba ni Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi ba, illa takarar Sanata na yi, kuma Allah Ya ba ni, don haka alhamdulillah.”
Sanata Ndume ya ce, “Zan yi amfani da kalaman tsohon Shugaban Amurka Franklin D Roosevelt da ke cewa: “Ba kishin ƙasa ba ne, ka goyi bayan Shugaban Ƙasa kan duk abin da ya yi.
“Kishin ƙasa shi ne faɗin gaskiya ba wai ga Shugaban Ƙasa kawai ba, har ma ga kowa.
“Ba kishin ƙasa ba ne ka ɓoye gaskiya ga masu mulki, kai har ma ga kowa. Dole a faɗa wa Shugaban Ƙasa gaskiya kuma na yi imani da waɗannan kalaman, kuma Allah yana tare da mai gaskiya.
“Don haka na sani ban yi kuskure ba, mutane ba su yi kuskure ba saboda faɗin gaskiya da kuma tsayawa kan gaskiya.
“Don haka ina ƙara nanata wa Shugaban Ƙasa cewa ya koma ya sake nazarin kan kalaman da na yi domin ɗaukar matakan da suka dace wajen samar wa ’yan ƙasa sauƙi kan halin da suke ciki.”
Sanatan ya yi magana kan makomarsa a jam’iyyarsa ta APC da ta ce ya saɓa mata.
Ya ce, yana cikin waɗanda suka kafa Jam’iyyar APC.
“Zan iya cewa na ma riga Shugaban APC [Ganduje] shiga APC,” in ji Ndume.
Ya ƙara da cewa, yana cikin sanatoci 22 daga PDP da suka kafa APC, lokacin da shugaban jam’iyyar na yanzu Abdullahi Umar Ganduje ke Mataimakin Gwamna.
Ali Ndume, sanata ne wanda ya yi suna wajen sukar manufofin gwamnati, yayin da magoya bayansa ke masa kallon mai faɗin albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ba.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da Majalisar Dattawan ta dakatar da wani wakili nata.
Ko a watan Maris ɗin 2024 majalisar ta dakatar da Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya daga majalisar bayan zarginsa da furta “kalaman da ke iya zubar da ƙimar majalisar.”
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan wata tattaunawa da sanatan ya yi da kafar yaɗa labarai ta BBC, inda ya yi zargin cushe a cikin kasafin kuɗin bana.