Dole a nemo wadanda suka kashe Janar Alkali

Yadda Rundunar Sojan Kasa ta gano gawar Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya, wanda shi ne tsohon Shugaban Gudanarwa na rundunar a ranar Larabar makon jiya ya kawo karshen rudani da mamakin yadda ya bace ba labari. An gano gawar ce a cikin wani buhu da duwatsu a wata tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet da […]

Dole a nemo wadanda suka kashe Janar Alkali
Dole a nemo wadanda suka kashe Janar Alkali

Yadda Rundunar Sojan Kasa ta gano gawar Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya, wanda shi ne tsohon Shugaban Gudanarwa na rundunar a ranar Larabar makon jiya ya kawo karshen rudani da mamakin yadda ya bace ba labari. An gano gawar ce a cikin wani buhu da duwatsu a wata tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet da ke lardin Sheng na Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato. Kauyen Guchwet yana da nisan kimanin kilomita 10 ne daga Dura-Du, inda a makon jiya aka gano wani kabari da aka fara binne tsohon sojan kafin aka hako shi.

An samu labarin ne a garin Jos, kwana 58 bayan bacewar Janar Alkali, inda Komandan Sashe na 3 na Rundunar Sojan Kasa da ke Babban Barikin Rukuba, Jos Birgediya Janar Umar Muhammad wanda shi ne ya jagoranci binciken ya fitar sanarwar, inda ya ce “Rundunar Soja ta ba mu aiki guda uku. Na daya shi ne mu nemo Janar Alkali ko a raye ko a mace. Na biyu mu nemo motarsa wadda Toyota Corolla ce, sai na uku shi ne idan har wani abu ya faru da shi, to mu nemo wadanda suke da hannu.” Ya kara da cewa daya daga cikin wadanda ake zargi da laifin da ya kawo kansa ne ya taimaka musu wajen gano rijiyar. Sojoji sai suka kwalfe rijiyar suka ciro gawar janar din.

Janar Muhammad ya kara da cewa, “mun kammala yanki biyu na aikin. Wanda ya rage shi ne na kama wadanda suke da hannu a aika-aikar domin su fuskanci hukunci komai girmansu.” Sannan ya ce sun gudanar da binciken ne tare da hadin gwiwar ’yan sanda da Jami’an Hukumar Kashe Gobara. Ya kuma ce mutum 6 na hannun ’yan sanda, sannan ya bukaci sauran wadanda ake nema da su kawo kansu domin sojojin na bibbiyansu. An birne Janar Alkali a Abuja ranar Asabar kamar yadda addinin musulunci ya tanadar bayan an gabatar da Sallar Janaza a Masallacin Abuja.

Janar din ya bace ne a ranar 3 ga watan Satumba a lokacin da yake tafiya daga Abuja zuwa Bauchi ta Jos. Rundunar Soja ta fara bincike ne a ranar 22 ga watan Satumba bayan iyalansa sun ce ba su ganshi ba. Kwatsam sai aka gano motarsa mai lambar Kwara MUN 670 AA a kududdufin Dura-Du a ranar 29 ga watan Satumba. An kuma gano motoci guda biyu daga kududdufin. An gano Toyota Hiace mallakar wani mai suna Abdullahi Abdullahi wanda ya bace a ranar 24 ga watan Yunin bana da kuma mota kirar Rober mai launin ja mai lamba AG 645 TRR mallakar Alhaji Isa Lawal wanda ake zargin an kashe tare da abokinsa Alhaji Dantani a Dura-Du tun a shekarar 2013.

Yadda dattawan kalibar Berom suka yi gum da bakinsu bayan an gano wannan lamari mai cike mamaki abin takaici ne. Muna yin Allah wadai da shirunsu. Shirunsu na tabbatar da maganar shugaban sashe na 3 na Rundunar Sojan Manjo Janar Benson Akinruloyo inda ya ce “wasu ’yan tsiraru ne suka kashe Janar Alkali amma mutanen garin suna taimaka musu.” Akalla mun so a ce mutanen garin su yi Allah wadai da abin da ya faru. Amma yadda suka yi gum da bakinsu ya nuna yadda tsana da rashin son mutane ke sa wa mutanen wani yanki suke danne wani yanki bisa la’akari da kabilanci.

Haka kuma yadda ’yan sanda suka kasa bankado yadda matasan Dura-Du suke hallaka mutane tun shekarar 2013 ya nuna gazawarsu. Ya kamata a ce akwai Jami’an Hukumar DSS a duk garuruwan da ke kasar nan a boye. Haka ma wasu matafiya da yawa an kashe su ba tare da an sani ba.

Muna jinjina wa Rundunar Soja bisa dogewarsu da hadaka da ’yan sanda wajen bankado wannan lamarin. Wannan shi ne yadda ya kamata a rika yin bincike na kwa-kwaf a duk lokacin da aka kashe wani a Najeriya. Muna kira ga sojoji da ’yan sanda da kada su yi kasa a gwiwa har sai an hukunta duk wadanda suke da hannu a kashe Janar Alkali.