Dole bara ta yi zarra saboda ta’azzara wa ‘yan Najeriya

Sana’ar bara ta zama kusan ruwan dare da Malam Bahaushe ke ce wa gama duniya. Duk da yake bara kara girma take da nisa kamar wutar daji amma a wasu lokuta idan na tsaya tsam na tambayi kaina kan me ya sa bara ke kara ruruwa kamar wutar daji, tambayoyi biyu ne a koyaushe sukan […]

Dole bara ta yi zarra saboda ta’azzara wa ‘yan Najeriya
Dole bara ta yi zarra saboda ta’azzara wa ‘yan Najeriya

Sana’ar bara ta zama kusan ruwan dare da Malam Bahaushe ke ce wa gama duniya. Duk da yake bara kara girma take da nisa kamar wutar daji amma a wasu lokuta idan na tsaya tsam na tambayi kaina kan me ya sa bara ke kara ruruwa kamar wutar daji, tambayoyi biyu ne a koyaushe sukan fara kewayawa a zuciyata.

Na san abin da ya fara haifar da bara a Najeriya musamman a yankin Arewa amma kuma me ya sa bara ta zama sana’a kuma me ya sa take kara fadada a kowane lungu da sako na kasar nan domin a yanzu ba  Malam Bahaushe kadai ke bara ba saboda  salon da tattalin arzikin Najeriya ya dauka na hajijiya da mafi yawan ’yan kasa.

A zamanin da a kusan karni 11 zuwa na 12 bayan shigowar addinin Musulunci kasar Hausa ta hanyar  fatake Larabawa. Manema ilimin sun yi ta kokarin neman ilimi inda da yawa daga cikin ‘almajirai’ kan yi tattaki zuwa wata uwa duniya domin neman ilimin addini. Wannan shi ne dalili na farko da ya fara haifar da mabarata wadanda ke tafiya wata uwa duniya don neman ilimi bisa dogaro da Hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ke cewa a je a nemi ilimi ko da zuwa birnin Sin (China) ne, kuma wani Hadisi na cewa neman ilimi wajibi ne ga dukkan Musulmi namiji da Musulma mace. Wannan dalili ya sa malamai karbar masu ilimi da aka kawo musu daga ko’ina ko kuma suka kai kansu.

Ladar da malaman zaure kan samu na ilimantar da almajiransu ba ta wuce ta taya malaman yin aikin gona ba da kuma lura da gidan malaman wajen yi musu hidima ta aikace-aikace don yarda da cewa ladar malami na wurin Allah. Inda su kuma yaran kan shiga gari domin barato abincin da za su ci duk da yake malamin kan samar wa almajiran wani kaso daga abincin gidansa a matsayin ladar noma.

Ta haka bara ta soma duk  da cewa addinin Musulunci ya yi hani a kan roko kamar yadda wani Hadisi na Manzon Allah, Annabi Muhammad, (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ke cewa mai yawan roko zai tashi a Ranar Alkiyama ba ya  da nama a fuskarsa. Wani abu da zai nuna wa jama’a rashin alfanun roko shi ne Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba ya cin sadaka.

Kan me ya sa mabarata ke kara yawa duk da yunkuri da gwamnatoci ke yi a kasar nan musamman ma a jihohin Arewa da kuma Gwamnatin Tarayya, don tabbatar da cewa Najeriya ba uwar guzuma ce ba a Afirka. Abin da bincikena ya ba ni shi ne bara ta wuce kan almajirai domin kuwa kusan babu irin jinsin mutanen da babu a cikin mabarata daga yara har tsofaffi don yanzu kusan sana’a ce ga marasa galihun ’yan Najeriya. Wahalhalun kasar nan kara ta’azzara suke yi. Kullum mutanen kasa na kara fuskantar kunci da ukubar rayuwa inda ukubar ta zame wa mafi yawan jama’ar Najeriya gaba kura baya siyaki.

Duk gwamnatin da ta zo kan karagar mulki kan lasa wa talaka zuma a baki amma sai ka ga al’amarin ya zama kamar an aiki bawa garinsu don sai dai a yi ta gafara sa amma babu ko kahon nunawa.

Ba ta canja zane ba domin abin da ya yi jiya shi ya yi yau da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin kuwa a irin alkawura na jin dadi da more rayuwa da Shugaba Buhari ya wa mutanen Najeriya alkawura ne irin na boka domin ko shakka babu kowa ya tuna bara to bai ji dadin bana ba.

Amma shakka babu kokarin da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi a kan ’yan Boko Haram abin a yaba ne amma shahararren Musulmin malamin nan masanin halayyar dan Adam wato Ibn Kaldum yana cewa gwamnati kamar gangar jikin dan Adam take in har wani bari ya kamu da ciwo to kusan ko’ina kan kasance cikin rauni da gazawa. A gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kunci da rashin samu sun jefa dimbin jama’a cikin halin kaka-ni-ka-yi inda alkaluman mabarata suka kara yawa har suka ninninka.

Bisa irin wannan yanayi da mutanen kasa ke fuskanta ya sa nake ganin sana’ar bara ba za ta taba yankewa ba domin kuwa hanyar magance bara ita ce yalwa, budi da yaduwar arziki amma a inda masu kasuwanci, kasuwancinsu ya rushe, wadanda suke son yin karatu suka zama ba su da kudin karatu, asibitin gwamnati ya zama na kudi sannan haraji ya zama tilas a kan kowane talaka, to dole hanyar bara ta zama dodar a kasar nan har illa masha Allah. Don a yanzu irin tsarin da Turawa suka rushe na jangali da haraji wanda ba sani ba sabo kuma ba ruwanmu da ko yaya kake ci kake sha shi ne ya dawo cikin wata fuska a kasar nan, a takaice, wannan shi ne an ki cin biri an ci dila.

A yanzu a wannan kasa ko ma’aikatan gwamnati na bara domin kudin da suke amsa cikin cokali ne don kudin sun yi karanci wajen kula da lafiyar iyalansu, ga kuma kayan masarufi sun daga kamar tashin gwauron zabo dalilin tashin Dalar Amurka, inda rashin wutar lantarki da ta yi wa kasar katutu ke ta kara durkusar da ’yan sauran kamfanonin da ake tinkaho da su a kasar nan wajen rage radadin talaucin da ke ci kamar ciwon ajali.

Wani al’amari da zai kara wa talakawan kasar nan radadin rayuwa shi ne karin kudin haraji ga masana’antu wanda babu wani hijabin da zai hana zafafa wa mazauna kasar nan a fannin saye da sayarwa. Karin digo biyu cikin biyar din da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi karin karaya ne a kan targade. Wani abin mamaki shi ne karin kudin harajin bai rasa nasaba da karin albashi na Naira dubu 30 da Gwamnatin Tarayya take son yi wa ma’aikatanta. Inda al’amarin ke so ya zama abin da Malam Bahaushe ke cewa a kwaci kayan dan kauye a ba dan birni ko kuma a bar jaki a rika dukan taiki. Ni ina ganin yunkurin gwamnati na kara kudin harajin kamfanoni ya fi kyau jama’a su kalle shi a matsayin ba ka ci nanin ba, dole nanin ta ci ka.

Koda yake Shugaba Muhammadu Buhari ya ce manufarsa ta kara kudin harajin ba wai don sa talakan Najeriya tagumi ba ne daga zugum din da yake, amma dai Hausawa na cewa hanyar Aljanna a bayyane take kamar yadda ta wuta take. Karin kudin albashin da ake son yi wa ma’aikata ko shakka babu wannan shi Hausawa ke kira da kyautar maye, a ba ka da hannun hagu a karbe da na dama.

Gwamnatocin baya sun ta yin kokari su yi wa sana’ar bara tufka don ganin an yi mata korar kare a kasar  nan, amma da wuya haka ta cimma ruwa in dai gwamnatoci ba za su samar da sauki ga jama’a ba, domin duk kokarinsu don dakile barar ba zai haifar da da mai ido ba don kudi ne za a yi ta narkarwa kamar ana shuka dusa babu ranar girba.

Gwamnatin da ta shude ta Goodluck  Jonathan ta yi hobbasa wajen ganin ta samar da makarantun almajirai a yankin Arewa a wani yunkuri na kawar da bara a matakin yara amma abin a yanzu ya canja zane domin irin tsarin da aka gina makarantun a kai ba shi ne suke a kai ba don an canja akalarsu.

Gwamnatin Buhari da hadin gwiwar kungiyoyin sa-kai sun yi ta wayar da kai kan illolin bara da kuma shirya tarurruka don lalubo bakin zaren da za a magance bara a tituna, amma yunkurin bai yi wani tasiri ba domin kamar yadda Hausawa ke cewa ba ka hana wa makaho sanda kuma ka kwace masa dan jagora. Domin idon rana ta zama zafi inuwa ta zama kuna ciki bai san ya yi hakuri ba. Kama mabarata da ake a kai su wani killataccen wuri don a rika kula da su kusan kidan ganga ne da lauje ake ta faman yi kuma shi mai kidan bai ma san cewa gangar ta rakwarkwabe ba don kuwa mabarata da yawa kan fada da bakunansu cewa juyin duniya kawai suke fuskanta irin na kwado daga ruwan sanyi zuwa ruwan zafi a gidajen da ake shirge su. Ko jihohin da suke kokarin killace mabarata kanwar duk ja ce domin ba a haifi Habu ba ne ake haifan Bukar, kamar yadda mabaratan suke fadi halin ko in kula da watsi da ake da su, shi yake sa su dawo ruwa tsumdun kada yunwa ta kashe su domin bakin da Allah Ya tsaga ba Ya hana masa hatsi ba.

A kullum a kasuwanni da masallatai sai ka ga sababbin fuskoki suna rokon abin da za su ci ko kudin sayen magani domin magance cutar da ke damunsu. Ba wai cewa babu irin wadannan matsalolin ba ne a Najeriya tun kafin amsar mulkin kai, amma abin nuni a nan shi ne karuwar tsananin rayuwa da take hauhawa a kasar nan kamar gyambo domin irin lalacewar da harkar tattalin arzikin kasar ta yi a lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake jagorantar akalar kasar ya fi zama abin al’ajabi domin kuwa ba haka jama’a suka zata ba wai wuta a masaka.

Fatar ’yan Najeriya shi ne samun sauki na tattalin arzikin kasa, tsaro da sauki a al’amuran gwamnati domin wadannan su ne dalilai da suke sa kowane dan kasa ya yi zabe ba don al’ada ba, addini ko kuma don mutum a matsayinsa na shugaba ba. Allah Ya kara wa shugabanninmu tausayinmu, su zama masu sonmu ba wai mu zama masu kaunarsu kadai ba.

 

Auwal Ahmed Ibrahim ya aiko ne Jihar Kaduna, za a iya samunsa ta email: [email protected]