‘Dole gwamnati ta kara himma don kwato fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja’

Dangiwa Umar ya bukaci kungiyar agaji ta Read Cross ta shiga tsakani a sako mutanen

‘Dole gwamnati ta kara himma don kwato fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja’

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna na mulkin soji, Kanar Abubakar Dangiwa Umar (mai murabus), ya roki kungiyoyin kasa da kasa musamman Kungiyar ba da Agaji ta Red Cross (ICRC), da su shigo su taimaka a yi sulhu don sako fasinjoji 60 da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kanal Umar wanda shi ne shugaban kungiyar nan ta ‘Movement for Unity and Progress’, ya kuma yi addu’ar Allah Ya tabi zukatan masu garkuwar wajen tausaya wa duka mutanen da suke tsare da su.

Dangiwa Umar ya ce, “Ina rokon Gwamnatin Tarayya da ta kara himma wajen gaggauta kubutar da wadannan bayin Allah.

“Kazalika, ina rokon kungiyoyin kasa da kasa, musamman Kungiyar Red Cross (ICRC), da su taimaka wajen sako wadannan mutane.”

Wata guda ke nan tun bayan da aka yi garkuwa da fasinjojin a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Da yake jawabi a kan hotunan da ’yan bindigar suka fitar na mutanen da ke hannunsu, Dnagiwa Umar ya ce hotunan suna daga hankali da ban tsoro musamman idan aka yi la’akari da yadda mutanen suka jigata saboda zama cikin wahala.