NAJERIYA A YAU: Dole gwamnatin Tinubu ta nemi amincewar duk ’yan Najeriya —CNG

Tinubu zai taho da sabon shirin habaka tattalin arziki, da bunkasa hanyoyin samar da abincin da Najeriya za ta iya dogaro da kanta, da kuma buda wa matasa tare da ba su damar yin rawar gaban hantsi. 

NAJERIYA A YAU: Dole gwamnatin Tinubu ta nemi amincewar duk ’yan Najeriya —CNG

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

Daga yau, saura kwanaki biyu kacal Bola Ahmed Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.

Shugaban mai jiran gado zai taho da sabon shirin habaka tattalin arziki, da bunkasa hanyoyin samar da abincin da Najeriya za ta iya dogaro da kanta, da kuma buda wa matasa tare da ba su damar yin rawar gaban hantsi.

Ko me Gamayyar Kungiyoyin Mutanen Arewa za ta ce game da wannan? A ganinta ta yaya sabon shugaban zai iya cimma wannan sabon buri duba da irin matsalolin da ke gaban gwamnatinsa?

Shin akwai wasu abubuwa na takamaimai da ya kamata gwamnati mai zuwa ta sani game da Arewa?

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan