‘Dole gwamnoni su bunkasa hanyoyin samun kudin shiga- Gwamna Tambuwal

Gwamnan Sakkwato,  Aminu Waziri Tambuwal ya shawarci gwamnoni da su bunkasa hanyoyin samun kudin shiga, don ita ce kawai mafita nan gaba.Da yake jawabi a taron horar da masu rike da mukaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da ke jiharsa, wanda aka gudanar a Jihar Kaduna, Tambuwal ya ce, yanzu jihohi na fama da kalubalen […]

‘Dole gwamnoni su bunkasa hanyoyin samun kudin shiga- Gwamna Tambuwal
‘Dole gwamnoni su bunkasa hanyoyin samun kudin shiga- Gwamna Tambuwal

Gwamnan Sakkwato,  Aminu Waziri Tambuwal ya shawarci gwamnoni da su bunkasa hanyoyin samun kudin shiga, don ita ce kawai mafita nan gaba.
Da yake jawabi a taron horar da masu rike da mukaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da ke jiharsa, wanda aka gudanar a Jihar Kaduna, Tambuwal ya ce, yanzu jihohi na fama da kalubalen rashin kudi, sai su duba hanyoyin samun kudin shiga a jiha, fiye da jiran kason gwamnatin tarayya don samun makoma mai kyau da za ta dore.
“Tafiyar da ayyukan al’umma na fama da matsalolin da ba a koyar da hanyoyin warware su a makaranta, amma samuwar kafafen sadarwa da ake mu’amala da su, suna wayar da kan al’umma, don haka akwai matukar bukatar bayyana gaskiya, wajen tabbatar da shugabanci nagari,” inji shi.
Gwamnan ya ce al’umma na bunkasa, don haka dole gwamnati ma ta bunkasa sababbin hanyouyin aiwatar da nagartattun ayyuka, don haka ya shawarci mahalarta taron horarwar su rage jin zafin junan su, su inganta hadin kai don tabbatar ayyukan gweamnati cikin nagarta.
“Mun yi hasashen cewa, yin nazari da bibiyar al’amura, a irin wannan taron horarwar zai yi matukar tasiri wajen samar da sababbin tsare-tsare da shirye-shirye, da za su yi mana nuni yadda za mu biya bukatun wadanda suka zabe mu, tare da fatan za mu tabbatar da jagoranci nagari, “ inji shi.
Ya ce takaddamar da ake samu a tsakanin jami’an gwamnati, ba tare da la’akari da matakin da suke ba, suna aukuwa ne idan aka sanya son rai, maimakon kyakkyawar manufa da jajircewa wajen kare bukatun al’umma.
“Mukamai da ayyuka duk an bayyana su da kyau, ta yadda babu wanda zai shiga aikin wani. Don haka ina da tabbacin cewa ana shiga rudani ne kawai, in an ki sadaukar da akai don al’umma, an koma kokarin cimma manufar son rai,” a cewarsa.