Dole Isra’ila ta dakatar da kisan kiyashi a Gaza — Kotun Duniya

Isra’ila ta kai munanan hare-hare wadanda sun yi sanadiyar kashe Falasdinawa sama da 26,000

Dole Isra’ila ta dakatar da kisan kiyashi a Gaza — Kotun Duniya

Kotun Duniya (ICJ) ta kada kuri’ar amincewa da umartar Isra’ila ta dauki dukkan matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan kiyashi a Gaza.

Alƙalan kotun sun kaɗa ƙuria’a 16 kan cewa akwai bukatar Isra’ila ta dauki dukkan matakan da suka dace na hanawa tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen haddasa yi wa Falasɗinawa kisan kare dange a Zirin Gaza.

Har ila yau, ta hanyar kuri’a 16, kotun ta ce dole ne Isra’ila ta ɗauki matakan gaggawa don tabbatar da samar da agajin jin kai da na yau da kullum da ake bukata cikin gaggawa.

A wannan Juma’ar ce dai Kotun Duniyar ta yi zaman karshe na zartas da hukunci kan karar da Afrika ta Kudu ta shigar gabanta.

Ana iya tuna cewa dai, a ranar 29 ga watan Disamban bara ce Afirka ta Kudu ta garzaya gaban Kotun, inda take tuhumar Isra’ila da kisan kare dangi a Gaza.

Wannan dai na zuwa bayan kashe tarin fararen hula da yawansu ya haura dubu 25 galibinsu mata da kananan yara daga ranar 8 ga watan Oktoba kawo yanzu.

Isra’ila dai ta sha musanta zargin bisa kafa hujja da cewa Hamas ta kashe mutanen da yawansu ya kai dubu 1 da 200 a hare-haren da ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba.

Kafin hukuncin, Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce ba duk inda aka je aka dawo, ba za ta sauya zani ba domin kuwa ɗamara ma yanzu suka tumke ta ci gaba da luguden wuta a Gaza.