Dole jama’a su taimaka wajen yakar matsalar tsaro —Ndume

Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce dole ne jama’a su bada hadin kai domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya. Ndume ya yi kiran ne a zantawarsa da Aminya, inda ya ce mutane suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ganin an kawo karashen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan. Ndume ya […]

Dole jama’a su taimaka wajen yakar matsalar tsaro —Ndume

Sanata Ali Muhammad Ndume

Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce dole ne jama’a su bada hadin kai domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Ndume ya yi kiran ne a zantawarsa da Aminya, inda ya ce mutane suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ganin an kawo karashen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

“Dole mutane su hada kai da jami’an tsaro wajen ganin an kawar da matsalar tsaro, ’yan ta’addar nan ba su da filin tashin jirgi, ba su da kasuwa, ba su da gidan mai dole a cikin gari suke samu wurin jama’a.” cewarsa.

Ya kara da cewa ’yan ta’adda ba su da kayan masarufi, a hannunsu saboda suna cikin daji a boye, mutane ne ke kai musu duk wani abin da suke bukata na amfanin yau da kulllum.

Daga karshe ya yi kira da jama’a a kowane mataki da su hada kai da jami’an tsaro wajen ba su bayanan sirri domin tabbatar da tsaro.