Dole mu hada kai domin mu kayar da APC- Kwankwaso
Dan takarar Shugaban Kasa a inuwar Jam’iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce dole sai dukkansu masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar PDP sun hada karfi da karfe domin kayar da APC a zabe mai zuwa. Sanata Kwankwaso ya fadi haka ne a sakatariyar PDP ta Jihar Neja da ke Minna, inda ya kai […]

Dan takarar Shugaban Kasa a inuwar Jam’iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce dole sai dukkansu masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar PDP sun hada karfi da karfe domin kayar da APC a zabe mai zuwa.
Sanata Kwankwaso ya fadi haka ne a sakatariyar PDP ta Jihar Neja da ke Minna, inda ya kai ziyarar tuntuba a ci gaba da ziyarar tuntuba da yake domin neman goyon baya a shirinsa na tsayawa takara.
Kwankwaso ya tabbatar da cewa duka wanda jam’iyyar ta tsayar a zaben fidda dan takara, zai goya masa baya dari bisa dari.
“Mun nemi canji a zaben 2015, amma a tsakiyar tafiyar sai na gane cewa babu abin da canjin ya kawo face karin kashe-kashe da yunwa da talauci da rashin ci gaba.”