Dole mu hadu mu yaki talaucin da yake a Najeriya – Tinubu ga Gwamnoni

Ya ce a shirye yake ya yi aiki da su wajen dakile talauci a kasar

Dole mu hadu mu yaki talaucin da yake a Najeriya – Tinubu ga Gwamnoni

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya yi kira ga Gwamnoni da su hada kai da Gwamnatin Tarayya wajen yaki da talauci a Najeriya.

Shugaban, wanda ya yi wannan kiran lokacin da ya karbi Gwamnonin Najeriya a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba, ya ce yawan talaucin ba abin da za a lamunta ba ne.

Tinubu ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su manta da bambance-bambancensu su hada gwiwa wajen kakkabe talauci a Najeriya.

Ya ce, “Muna ganin tasirin talauci a fuskokin mutane da yadda talauci ya zame musu kamar gado. Babban abin da muka sa a gaba shi ne yaki da talauci ta hanyar ajiye bambance-bambancenmu da gina kasa,” kamar yadda sanarwar Daraktan Yada Labarai na Aso Rock, Abiodun Oladunjoye ya fitar.

Ya kuma ce, “Dukkanmu ’yan gida daya ne da muke barci a dakuna daban-daban. Idan muka kalli junanmu a haka muka yi aiki tare, za mu cire mutanenmu daga talauci.”

Shugaba Tinubu ya kuma ce shugabanci na gari ne zai tabbatar da ci gaban Dimokuradiyya a Najeriya.

Kazalika, ya kuma ba Gwamnonin tabbacin cewa kofarsa za ta zama a bude ga dukkan Gwamnonin.

Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine

Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi

Tsohuwar ɗaliba ta kai ƙarar makarantar da ta kammala

Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya