Dole mu kwato ’yancinmu daga masu son mayar da mu bayi – Wamakko
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga shugabannin Arewa su yi watsi da bukatunsu na kashin kai domin ceto kasar nan daga rugujewa. Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarce shi a gidan gwamnati, inda ya ce […]

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga shugabannin Arewa su yi watsi da bukatunsu na kashin kai domin ceto kasar nan daga rugujewa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarce shi a gidan gwamnati, inda ya ce lallai kasar nan tana bukatar canji mai ma’ana da zai kawo gwamnati mai inganci da za ta tallafa wa talaka ta fitar da shi daga cikin halin kunci da matsi da yake fama da shi, “amma hakan ba zai samu ba sai shugabanninmu sun kauce wa kuskuren da aka tafka a shekarar 2011 na kowane dan Arewa ya fito neman kujerar Shugaban kasa, don Allah kowa ya hadiye kwadayinsa a zabi wanda ya fi cancanta,” inji Wamakko.
Gwamnan ya ce abin da ke faruwa a Najeriya bai tafiya daidai domin an mai da Cif Edwin Clark da Asari Dukobo shafaffu da mai, inda ake ware wasu don musguna musu kamar yadda aka yi wa El-Rufa’i don ya fadi gaskiya kuma duk maganar da ya yi in har ba daidai ba ne ba ta kai kamar na wadancan ba, amma ba wanda ya ce musu komai, “Dole mu tashi tsaye mu kwato ’yancinmu daga wadanda ke son su mayar da mu bayi,” inji shi.
Sai ya yaba wa tunani da hangen nesa mai kyau na Atiku Abubakar inda ya nemi ya kara taimaka wa Jam’iyyar APC don kawo sauyin da ake bukata da zai kawar da bambancin addini da na kabila da ya fara kunno kai a kasar nan.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya gode wa al’ummar Jihar Sakkwato da kyakkyawar tarbar suka yi masa, inda ya ce ya je jihar ce domin a duk Najeriya Sakkwato ce aka fara samun canji inda aka kafa Daular Usmaniyya, saboda haka duk wanda zai yi kokarin kawo nasa canjin ya kamata ya faro daga Sakkwato.