Dole Najeriya ta ci gaba da zama a dunkule – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci tsagerun Neja-Delta da suke fasa bututun maid a iskar gas a yankin su rungumi zaman lafiya don ba kasar nan damar ci gaba, inda ya shaida musu cewa ya kamata su sani dole ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa a dunkule.Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a Fadar […]

Dole Najeriya ta ci gaba da zama a dunkule – Buhari
Dole Najeriya ta ci gaba da zama a dunkule – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci tsagerun Neja-Delta da suke fasa bututun maid a iskar gas a yankin su rungumi zaman lafiya don ba kasar nan damar ci gaba, inda ya shaida musu cewa ya kamata su sani dole ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa a dunkule.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja a shekaranjiyan Laraba lokacin da mazauna Abuja suka kai masa gaisuwar Sallah, inda ya ce, taken nan da aka rika yadawa a shekarun 1960 cikin Ingilishi mai cewa: “Go On With One Nigeria -GOWON),” wato mu tafi a matsayin Najeriya daya har yau yana da tasiri domin tabbatar da dunklewar Najeriya aiki ne day a wajaba a kan kowa.
Ya ce a yayin da aka samu gagarumar nasara wajen yaki da Boko Haram, yanzu gwamnati tana fuskantar wani hadari daga ayyukan tsagerun yankin Neja-Delta.
Buhari ya shaida mutanen yankin Neja-Delta cewa za su samu hakkokinsu kamar yadda doka ta tanada, kuma ya ce gwamnatinsa ta fara kokarin gano kungiyoyi da shugabanninsu domin lallabarsu su ajiye makamansu.
Shugaban kasar ya ce, “A baya ba mu maganar man fetur, damuwarmu ita ce kasancewar Najeriya daya. Don haka a shaida wa tsagerun cewa dole Najeriya ta ci gaba da zama a dunkule.”
Da ya juya kan barayin gwamnati Shugaba Buhari ya bukaci wadanda suka sace kudin jama’a su shiga tattaunawa domin dawo da kudin cikin lumana, inda ya yi gargadin cewa duk barawon gwamnati da ya ki yin haka, ba zai zauna lafiya ba, domin gwamnati za ta ci gaba da takura masa.
“Don Allah kun gaya wa wadanda suke shake da kudin da ba nasu ba ne su yi kokarin tattaunawa su dawo da su cikin lumana ta yadda za mu zauna lafiya. Idan ba haka ba, za mu ci gaba da nemo kudin nan,” inji Buhari.
Shugaba Buhari ya yi nadama kan yadda duk da canjin suna da sake fasali da aka yi wa Hukumar Wutar Lantarki ta kasa (NEPA) har yanzu wauta lantarki ta kasa samuwa a Najeriya.  Ya ce yanzu sai wasu mutane sun je shagon aski suke iya sauraren rediyo don samun labarai, yayin da masu kallon talabijin NEPA ke hana su samun labarai saboda rashin wutar lantarki.
Ya ce yana sane akwai matsaloli masu yawa a kasar nan, sai dai ya bayar da tabbacin cewa Minsitan Noma Audu Ogbe yana aiki tare da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele domin tabbatar da akalla jihohi 13 sun fara samar da isasshiyar shinkafa ga kasar nan. Ya ce shirin yana karfafa gwiwar gwamnati domin tuni manoma da dama sun koma gona.
Tunda farko jagoran ayarin Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce shekara guda da ta gabata ta kasance mai tsauri ga kasar nan sakamakon tabargazar da gwamnatin da ta gabata ta tafka. Ya ce gwamnatin Buhari ta gaji dimbin badakalar kudi kuma har yanzu tana kokarin magance hakan ne. Sai ya yi alakwarin gwamnatinsu za ta dora kasar nan a kan kakkarfan ginshiki, inda ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Shugaba Buhari lafiya da karfin jiki.
Cikin manyan bakin da suka kai gaisuwar Sallar akwai Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello wanda ya mika wa Shugaban kasa babban katin Barka da Sallah , sai Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Babachir Dabid Lawal da Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Manjo Janar Babagana Monguno da  wadansu ministoci da hafsoshin tsaro da sarakunan gargajiya, yayin da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da na Majalisar Tarayya Yakubu Dogara suka tura wakilansu.