Dole ne a hukunta ‘yan Ombatse da suka kashe jami’’an tsaro -Janar Buhari
Tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya yi watsi da bayanin da Babban darektan hukumar jami’an tsaro na farin kaya (SSS) Mista Ita Ekpenyong ya yi cewa sun yafe wa matsafan Ombatse da suka kashe jami’ansu, inda janar din dole ne a gano wadanda suka kashe jami’an kuma a hukunta su.Janar Buhari, wanda ya bayyana […]

Tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya yi watsi da bayanin da Babban darektan hukumar jami’an tsaro na farin kaya (SSS) Mista Ita Ekpenyong ya yi cewa sun yafe wa matsafan Ombatse da suka kashe jami’ansu, inda janar din dole ne a gano wadanda suka kashe jami’an kuma a hukunta su.
Janar Buhari, wanda ya bayyana haka yayin da yake ganawa da editocin kamfanin buga jaridun Media Trust a ofishinsa da ke Kaduna, ya yi nuni da cewa kuskure ne Babban darektan ya ce an yafe wa wadanda suka kashe jami’an tsaron.
‘’Shugaban na SSS ko kuma ko wane ne ya ce an bar wadanda suka yi kisan da Allah, ba shi da ikon yin haka a tsarin mulki, ‘yan Najeriya suna da daman bin duk addinin da suke so, idan sun ga dama suna iya zama wadanda ba su da addini ko kuma su bi duk abin da suka ga dama, tsarin mulki ya ba su damar yin haka. Amma babu wanda zai raunata wani dan Najeriya a kyale shi, balle kuma a ce an yi wa jami’an tsaro har 56 yankan rago, sannan wani da ya fito daga cikin wannan tsarin ya ce wai an yafe musu, mai wannan maganar ko dai bai san abin da ya fada ba, ko kuma bai kamata ya kasance a inda yake ba.’’
‘’Haka kuma ban goyi bayan masu cewa a rushe wuraren masu bautar tsafi ba, domin tsarin mulki ya ba su dama su yi ibadarsu matukar ba su saba wa tsarin mulki ba. Amma wadanda suka kashe jami’an tsaro 56 dole ne a gano su kuma a hukunta su komi dadewa.
Dangane da cikar Najeriya shekara 14 a mulkin demokaradiyya kuwa, Janar Buhari wanda dan takarar shugaban kasa ne a karkashin inuwar jam’iyyar CPC, ya ce babu wani abu da aka samu da za a yi murna saboda shi.