Dole ne a yi zabe ranar 28 ga Maris – Barista Hawaja

Wani lauya mai zaman kansa da ke Jos a Jihar Filato, Barista Yusuf Gambo Hawaja ya ce dole ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da zabe a ranar 28 ga Maris da 11 ga Afrilu mai zuwa kamar yadda ta fada.  Barista Yusuf Hawaja ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa […]

Dole ne a yi zabe ranar 28 ga Maris – Barista Hawaja
Dole ne a yi zabe ranar 28 ga Maris – Barista Hawaja

Wani lauya mai zaman kansa da ke Jos a Jihar Filato, Barista Yusuf Gambo Hawaja ya ce dole ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da zabe a ranar 28 ga Maris da 11 ga Afrilu mai zuwa kamar yadda ta fada. 

Barista Yusuf Hawaja ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce shi ne a yi zabe kafin kwana 30 da rantsar da sabon Shugaban kasa ko Gwamna, don haka duk wanda ya kawo wani abu sabanin wannan ya kawo son ransa ne kawai. Ya ce ko wancan dage zaben da aka yi, an yi ne saboda lokaci bai kure ba, amma a yanzu lokaci ya kure.
Barista Hawaja ya ce tsarin mulkin Najeriya ya fadi cewa a bayan duk shekara hudu za a yi sabon zabe a Najeriya, idan mutum ya ci zaben ya zarce idan kuma mutum bai ci ba ya sauka.
Ya ce maganar kafa gwamnatin rikon kwarya babu ita a tsarin mulkin Najeriya, don haka kafa ta ya saba wa tsarin mulki.
Barista Hawaja ya ce, “Muna da kotuna da lauyoyi a Najeriya kuma yanzu idon ’yan Najeriya ya bude kamar yadda lauya zai bude kundin tsarin mulki ya karanta haka su ma ’yan Najeriya za su bude su karanta. Don haka dole ne a yi zaben kamar yadda tsarin mulki ya fadi,” inji shi.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta bi tsarin mulki ta hanyar barin hukumar zabe ta gudanar da zaben yadda aka tsara don kauce wa fadawa cikin rikicin a kudnin tsarin mulki.