Dole PDP ta lashe zaben shugaban kasa na 2019- Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce dole PDP ta kwace mulkin kasar nan a zaben 2019 mai zuwa daga hannun APC. Tsohon shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake karvan bakuntan Raymond Dokpesi, wanda ke fafutukar neman zama shugaban Jam’iyyar PDP a taron ta na kasa da za ayi a […]
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce dole PDP ta kwace mulkin kasar nan a zaben 2019 mai zuwa daga hannun APC.
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake karvan bakuntan Raymond Dokpesi, wanda ke fafutukar neman zama shugaban Jam’iyyar PDP a taron ta na kasa da za ayi a watan Disamba mai zuwa.
Ya kara da cewa bai kamata jam’iyyar ta sake yin kuskuren da ta yi a baya ba wajen zaben shugaban jam’iyya da jami’in hulda da jama’a, domin “Suna da muhimmanci sosai”
“A yanzu muna bukatar mutum mai juriya da baki ya zama mana shugaban jam’iyya. Idan muka yi kuskuren zaben shugaban jam’iyya da jami’in hulda da jama’a, lallai za mu ji-jiki.
“Wannan zaben na da matukar muhimmanci ta yadda lokacin da babban zaben zai zo, PDP za ta samu mafi rinjaye a majalisun jihohi da na tarayya, sannan kuma dole PDP ta lashe zaben shugaban kasa,” inji shi.