Dole Shugaba Jonathan ya tsaya zabe a shekarar 2015 – Edwin Clark

Tsohon Ministan Watsa Labarai Cif Edwin Clark ya ce dole Shugaban Goodluck Jonathan ya tsaya takara karo na biyu kamar sauran shugabannin farar hula da suka gabace shi. Cif Clark ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da ya jagoranci dattawan Kudu maso Kudu da yankin Tsakiyar Najeriya a karkashin kungiyar […]

Dole Shugaba Jonathan ya tsaya zabe a shekarar 2015 – Edwin Clark
Dole Shugaba Jonathan ya tsaya zabe a shekarar 2015 – Edwin Clark

Tsohon Ministan Watsa Labarai Cif Edwin Clark ya ce dole Shugaban Goodluck Jonathan ya tsaya takara karo na biyu kamar sauran shugabannin farar hula da suka gabace shi.
Cif Clark ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da ya jagoranci dattawan Kudu maso Kudu da yankin Tsakiyar Najeriya a karkashin kungiyar Tabbatar da Daidaito da Kawo Canji zuwa Fadar Shugaban kasa.
Lokacin da yake jawabi ga manema labarai na Fadar Shugaban kasa bayan ganawar sirri na tsawon awa biyu, Mista Clark ya ce kamar sauran daukacin tsofaffin zababbun sshugabannin kasar nan, Jonathan ya cancanci ya nemi a sake zabensa a matsayin Shugaban kasa a shekarar 2015.
“Ba zan taba jagorantar wata kungiya da za ta nuna adawa a shekarar 2015 (game da zango biyu na Jonathan ba), ba don Clark yana fadin haka ba. Yana rubuce a tsarin mulkin Najeriya. Shagari da Obasanjo sun yi haka. Wani soja ya kwace zango na biyu na Shagari. Idan Shagari ya cancanci yin zango biyu me zai hana Jonathan? Ko saboda shi ya fito ne daga kabila marar rinjaye? Don haka duk wata kungiya da ke zuwa ta gana da Shugaban kasa bisa ra’ayin kada ya tsaya takara a shekarar 2015 ba na cikinta. kungiyar da na kawo mu dattawa a nan mun yi imanin cewa wajibi ne Jonathan ya tsaya takara a shekarar 2015 kamar yadda tsarin mulki ya tanada,” inji shi.
Ya ce, “Muna tattaunawa don ilimantar da mutane. Ka yi naka zamanin. A shekarar 50 zuwa 53 ba mu mulki kasar nan ba. Mu ba ’yan kasar nan ba ne? Mu rika yi wa juna adalci. Bai kamata mu yi magana kan shekarar 2015 ba, amma mun yi ne saboda wasu mutane sun fara cewa bai cancanci ya tsaya takarar ba, kuma irinmu da muka yi imani da hakan muke ilimantar da su abin da muke yi.”
Clark ya kara da cewa, “Wannan ganawa ce ta dattawan Midil Belt da na Kudu maso Kudu, kuma Midil Belt ta kunshi Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu gaba dayansu jihohi 19. Kowa a Najeriya daidai yake da dan uwansa. Ba wanda ya fi wani, kuma ba wanda bai kai wani ba. Don haka ne muka sanya wa kungiyarmu kungiyar Tabbatar da Daidaito da Kawo Sauyi. Tilas a samu canji a kasar nan.”