Dole Shugaban Kasa ya zama Musulmi Bayarabe a 2023 —MURIC
MURIC na zargin nuna wariya da musguna wa Musulmi Yarabawa a Najeriya.
Kungiyar Rajin Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta ce jazaman ne dan takarar Shugaban Kasan da za a tsayar a zaben 2023 a Najeriya ya kasance Musulmi daga yankin Rabawa.
Daraktan MURIC, Farfesa Akintola, shi ne ya jaddada hakan, bisa hujjar cewa tun da Najeriya ta samu ’yancin kai, ba a taba samun Musulmi Bayarabe da ya zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban Kasa ba, amma kuma Kiristoci sun yi har sau uku.
- Najeriya A Yau: Mene ne Amfanin Ayyana ’Yan Bindiga A Matsayin ’Yan Ta’adda?
- Kwanan nan Najeriya za ta fara kera jiragen yaki marasa matuka —Minista
“Daga 1960 zuwa yanzu babu wani Musulmi Bayarabe da ya taba zama Shugaban Kasa. Amma sau biyu Olusegun Obasanjo ya yi: mulkin soji (1976 –79) da mulkin farar hula (1999 -2007). Earnest Shonekan ya yi shugaban riko (Agusta 1993–Nuwamba 1993). Yanzu kuma Kirista ne Mataimakin Shugaban Kasa (Farfesa Yemi Osinbajo),” inji Farfesa Akintola.
Ya ci gaba da cewa, “Duk da haka, sai wariya da musguna wa Musulmi Yarabawa ake ta yi, tun bayan samun mulkin kai. An hana su kusan dukkannin ’yancinsu a matsayin ’yan kasa.
“Wahalar a dauki Musulmi Bayarabe aiki bayan ya kammala jami’a tamkar a sanya giwa ne ta kafar allura. Ana kuma nuna wa Musulmi Yarabawa wariya a wurin rabon mukaman siyasa,” inji shugaban na MURIC.
Farfesa Akintola ya ce kadan daga cikin Musulmi Yarabawa da suka dace da kujerar shugaban kasa su ne Bola Tinubu, Dokta Muiz Banire, Dokta Kadiri Obafemi Hamzat, Babatunde Fashola, Rauf Aregbesola, Farfesa Is-haq Oloyede, Sanata Fatai Buhari, da Dokta Abdul Lateef Abdul Hakeem, da sauransu.