Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Manzon Allah (SAW) ya gaya mana cewar mu nemi arziki da jijjifi wato da sassafe, domin Allah Ya sanya wa wannan lokacin albarka, amma sai ka ga mutum bai tara komai ba, bai ajiye komai ba, amma ya sanya wa kansa wata ka’ida ta banza, cewar ba zai fita kasuwa ko wajen sana’arsa ba sai karfe goma zuwa sha daya na safe

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Almajirai

A halin da ake ciki yanzu a kasar nan, mutane Gabas da Yamma, Kudu da Arewa suna fama da talauci, birni da kauye. Da yawan mutane suna fadin hakan.

Ko da gaske ne ko ba da gaske ba ne, amma a zahiri idan mutum ya kalli halin da ake ciki na tsadar kayan masarufi, ya san lallai masu karamin karfi suna fama da wahala da damuwa, domin wanda yake da abin batarwa, shi ne yake kiran akwai tsada.

Shi kuma wanda ba shi da shi, bai ma san da tsadar ba, saboda ba shi da abin batarwa balle ya ji zafin halin da ake ciki. 

Amma wanda yake da wadata da rufin asiri har yana iya yin cefane, shi ne zai ba da labarin halin da ake ciki, saboda ya san me ke faruwa a rayuwar yau da kullum, wato ana halin uwa kuturwa kaka mayya da talauci a kasar nan, inda kusan yanzu mafiya yawan mutane za ka ji suna maganar abinci, har wadanda ba su cika raki a kan abinci ba, yanzu za ka ji zancensu a kan abinci ne.

Wannan kuma gaskiya ne, domin a zamanin Gwamnatin Mai Malafa, wato Goodluck Jonathan, an sanya mafi karancin albashi na Naira dubu goma sha takwas, amma a lokacin albashin zai iya sayen buhun shinkafa da jarkar man gyada da na manja da buhun gawayi, har da kudin cefane, duk a cikin mafi karancin albashin da bai wuce dubu sha takwas ba. 

Amma kuma a yanzu da mafi karancin albashi ya zama Naira dubu saba’in, duk da haka, ba zai iya saya maka buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ba, saboda kudinsa ya doshi Naira dubu dari.

Haka nan man girki da buhun gawayi duk kudinsu ya zarta hankali, domin kuwa galan din man girki ya kai Naira dubu goma sha takwas, buhun gawayi kuma ya doshi dubu goma. 

Wadannan uku ne kacal daga cikin abubuwan bukata domin yin girki; sauran kayayyakin kuma kudinsu ya wuce hankali. Da ma ba a maganar madara ko naman kaza ko naman rago, domin su kam yanzu sai wanda ya isa.

A yanzu idan mutum zai sayi kwai da madara da nama da ’ya’yan itace da ganyayyaki, to babu shakka aljihunsa zai gaya masa.

Idan ka kalli kasar nan Kudu da Arewa, za ka fahimci cewar gaskiya talaucin da ake fama da shi a Arewa ya ninka na ko’ina, domin a Arewa ne mutane suke shan bakar wahala da azaba. 

Yanzu dai babu wasu masana’antu na ku-zo-ku-gani, babu wutar lantarki kuma babu ruwan famfo, wadanda ginshikai ne wajen samun arziki a ko’ina a duniya.

Mun rasa wadannan biyun yanzu a Arewa, mutane na shan bakar wahala wajen samun lantarkin da za su yi sana’arsu, sakamakon halin da aka shiga — dama yaya lafiyar kura balle ta yi zazzabi? 

Tun asali lantarkin ba samun sa muke yi wadatacce ba, balle kuma yanzu da aka shiga wani hali na lalacewar hanyoyin samun sa, ai sai abin da muka gani kawai.

Kamfanoni da otal-otal da suke amfani da man dizal yanzu da yawansu sun sare, wadanda ya zama dole su yi amfani da shi, za ka tarar sun yin karin kudi mara misali a kan kayayyakinsu, wadanda ba za su iya ba tuni suka kashe injina suka sallami ma’aikata har sai lokacin da lamura suka hau saiti. Wannan shi ne kadan daga misalin irin halin da muke ciki a Arewa.

Amma kuma idan an bi ta barawo a bi ta mabiyin barawo. Mu Musulmi, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya gaya mana cewar mu nemi arziki da jijjifi wato da sassafe, domin Allah Ya sanya wa wannan lokacin albarka.

Amma galibinmu muna ji muna kallo wannan albarkar ta wuce mu.

Mutum bai tara komai ba, bai ajiye komai ba, amma ya sanya wa kansa wata ka’ida ta banza, cewar ba zai fita kasuwa ko wajen sana’arsa ba sai karfe goma zuwa sha daya na safe.

Ai dole wahala da talauci su yi mana katutu. Mutane suna kwance suna barci mara ma’ana, alhali ga lokacin da za su tashi su nemi arziki ya yi, amma sun yi sake.

Duk mazaunin Kudancin kasar nan ya san yadda sauran kabilun kasar nan suke cin ribar sammako da kuma duku-duku, domin wani zubin, kafin a kira Assalatu wani ya fita kasuwa ya bude shago, ko wata mai sana’a ta fita ta saro abin da za ta sana’anta.

Za ka yi mamaki, karfe biyar na asubahi, mace da goyo a bayanta ta tashi ta shiga gona ta yanko ayaba ta dauka ta kai kasuwa.

Tun kafin gari ya waye za ka ga yara ’yan makaranta a Legas da sauran jihohin Kudu a bakin tituna suna jiran ababen hawa, a lokacin da takwarorinsu a Arewa suke can suna sharbar barci da minshari, su kuma wadancan ga su a kan titunan birnin Ikko suna jiran abin hawa zuwa makaranta.

Masu sana’a da masu kasuwanci duk sun fito suna neman arziki, amma takwarorinsu a Arewa suna kwance suna minshari, kuma a haka suke tunanin Kano za ta kamo Legas ko Arewa za ta kamo Kudu, ai mu da kamo su haihata-haihata, domin hanyarmu da tasu ba iri daya bace.

Su mutanen Kudu, suna neman arziki ne da gaske tare da jajircewa da aiki tukuru, yayin da mu kuma muke tunanin samun arziki ta hanyar yin addu’a da dabo da kasala da son jiki da lalaci da mutuwar zuciya. 

A ganina za mu jima muna kukan talauci kuma ba zai rabu da mu ba, matukar ba mu tashi tsaye mun yaki kasala da lalaci da mutuwar zuciya ba.

Dole ne mu ma mu zage dantse kamar yadda takwarorinmu na Kudu suka zage dantse suke neman arziki, wanda Shi Allah babu ruwanSa, wanda ya tashi tsaye ya nema, Shi Yake taimaka wa.

Za ka yi mamaki a Arewa karfe bakwai na safe ko takwas na safe, kana neman wani abu, sama ko kasa, ka kasa samu, saboda masu kantuna ba su bude ba, suna kwance cikin gidajensu.

Idan ka ga ana sammako wajen nema a Arewa, to watakila yara ne rataye da buhu a bayansu suna tsince-tsince a tituna.

Wannan kam ko shakka babu suna kokarin fitowa da jijjifi neman abin da za su tsinta.

Na taba fitowa karfe shida na safe, bukatar zuma ta kama ni, amma wallahi ban iya samu ba, sai da na karade wasu manya da kananan tituna a birnin Kano ina neman zuma, amma na kasa samu. Tsirarun kantunan da na iya samu a bude ba su da ita, wadanda suke da ita kuma ba su bude ba.

Mun gode wa Allah da yanzu aka fara samun manyan kantuna irin su Sufi Mart da ke kan Titin Gidan Zoo, wadanda suke aiki tsawon sa’o’i ashirin da hudu.

Haka nan shi ma kantin Best-Medid da ke Tal’udu, su ma yanzu suna aiki ba dare babu rana, koyaushe kana iya samun abin da kake nema.

Lallai idan muna neman arziki da gaske, mu tashi mu zage dantse mu nemi arziki a wajen Allah mu yi sammako, sannan mu nemi Allah Ya ci gaba da sanya mana albarka a nemanmu. 

Amma idan muka ci gaba da lafkewa a gidajenmu kwance muna barcin da ba zai amfane mu ba, to shakka babu, za mu ci gaba da zama kurar baya a sha’anin arziki a kasar nan, kuma za mu yi ta ganin koma baya a kudaden da muke samu na haraji wanda da shi ne ake yi mana ayyukan raya kasa.

Lallai ya kamata gwamnatoci da hukumomi su tashi tsaye su zaburar da mutane a kan sammako da kuma zage dantse da jajircewa wajen nema, sannan mu yi gaskiya mu yi da’a a sha’anin ciniki da kasuwanci.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja