Domin karfafa matasa ne zan yi takarar majalisar Kaduna – Shu’aibu Bala
Ka gabatar da kanka ga masu karatu? Sunan Shu’aibu Bala, an haife ni a garin dandaura a shekarar 1988, kuma na yi karatun Firamare da Sakandare a nan garin na dandaura. Sannan na ke Kwalejin Kimiya ta tarayya ta Kaduna (Kadpoly), inda na yi difolama, sannan kuma a yanzu haka ina ci gaba da yin […]
Ka gabatar da kanka ga masu karatu?
Sunan Shu’aibu Bala, an haife ni a garin dandaura a shekarar 1988, kuma na yi karatun Firamare da Sakandare a nan garin na dandaura. Sannan na ke Kwalejin Kimiya ta tarayya ta Kaduna (Kadpoly), inda na yi difolama, sannan kuma a yanzu haka ina ci gaba da yin babban difloma. Wannan ne takaitaccen tarihi na.
Me ya sa kake so ka yi takarar majalisar jiha?
Kasancewa na dan Najeriya kuma dan Jihar Kaduna wanda kundin tsarin mulkin kasar ya ba dama ya yi takara, sannan kuma na lura da yadda ake karancin matasa a wannan harka ta siyasa musamman a majalisar jiha, gashi kuma ana ta maganar mu matasa mune kashin bayan al’umman. Sai na ga ya dace na fito domin bada nawa gudunmuwa wajen kawo sauyi wajen wakiltar mazabata ta Kauru/Chawai don a samu sauyi mai ma’ana. Kuma musamman kasancewa kwanan Majalisar Tarayya ta amince da kudurin nan da zai tabbatar da sanya matasa cikin tsarin mulki, kuma dama mun dade muna babatun a sanya mu a cikin harkar, shi ne na ga ya dace mu shiga a dama da mu a aikace.
Ba ka tunanin cewa za ka fuskanci kalubale ganin cewa kai matashi ne?
kwarai da gaske akwai kalubale. Amma ai duk abin da mutum ya sa gaba ko ya yi kudurin yi, ya san cewa dole zai fuskanci kalubale masu yawa. Amma mun bar wa Allah komai. Kuma a matsayina na matsahi, idan har ina jin tsoron kalubale, to ya zama ke nan ban shirya shiga siyasa ba. Dole duk wanda ke son ya zama wakili na gari ya zama jajirtacce. Kuma kasancewa mun saba gwagwarmaya a siyasar makaranta da na kungiyoyi matasa, wanda irin wadannan gwagwarmar ce ta sa abokanan gwagwarmaya suka ga dace in fito, domin in zame musu madubi. Don haka ko kadan bana shakka.
Wane sauyi za ka iya kawowa?
Gaskiya na ji dadin wannan tambaya domin kuwa ban shigo siyasa da ka ba kamar yadda wasu ke shigowa. Ina da tsare-tsare da na shirya zan yi wa mutanen mazabata idan Allah Ya sa mun kai ga gaci. Ina da tsare-tsare da dama da na rubuta suna nan a rubuce. Kamar a bangaren matasa ‘yan uwana, zan karfafa musu gwiwa sosai, ta hanyar zama musu madubin dubawa kamar yadda muka shirya da su. Hakan zai sa in zama abin koyi a gare su ta hanyar zama dan majalisa na gari mai wakilta tare da kare muradun matasan Jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya. Ka ga idan aka samu haka, to lalai za a samu cigaba mai dorewa. A bangaren ilimi kuwa na shirya gabatar da kuduri a gaban majalisa wanda zai sa karatun tun daga Firamare zuwa Sakandare ya zama kyauta kuma dole. Sannan kuma zan taimaka wa mutanen mazabata da takardun karatu da ma makarantun su kansu da tallafi daidai gwargwado. Sannan a bangaren noma wanda mutanen mazabata suka fi yawa kuwa, na shirya yin duk mai yiwuwa wajen bayar da tallafi ta hanyar samar da takin zamani da feshi da koyar da su dabarun noman zamani da kuma gabatar da kuduri a majalisa da zai kare manoman. Sannan na fahimci muhimmancin tafiyar da mulki tare da sarakuna, don haka zan sanya duk masu rike da sarautun mazabata cikin harkokin siyasa, tun daga masu unguwanni har zuwa sarakunan irin sarakunan Kauru da Chawai da Kumana. Da bangaren kiwon lafiya da kula da harkokin tsaro da dai sauransu. A matsayi na matashi mai ilimi, dole in kawo sauyi, shi ya sa na zauna da masana, muka shirya duk abin da nake so in yi a matsayina na dan majalisa, sannan kuma muka tsara yadda za mu gudanar da wadannan ayyyuka. Don haka a shirye nake. Wasu abubuwan b azan iya fadinsu bane, amma ina tabbatar maka da cewa ina da tsare-tsare masu yawa. Amfanin ilimin ke nan ai, kuma ya kamata duk wanda ya zo neman kuri’a, mutanen gari su tambayeshi kuduroinsa.
Meye kiranka ga matsa a kan su shiga harkar siyasa?
To dama ana cewa haihuwa maganin mutuwa. Idan muka bari tsofaffin ‘yan siyasar suka wuce, mu kuma ba mu shigo mun koya ba, ya siyasar da shugabanci za ta kasance ke nan?. Don haka ya kamata su shigo a rika damawa da su a wannan harka. Kawai dai abin da ake so ga matasan shi ne mu zama masu ladabi da biyayya. Matashi mara kunya ba a bin da zai kawo sai shirme da wargi. Kuma yawancin matasa suna so su shigo amma kuma suna tsoro, ban ga abin tsoro ba a wannan harka. Don haka mu daina tsoro, mu fito a dama da mu. Mu dabbataka babbatun da muke yi, ba wai mu je mana maganganu ba a kan cewa ana danne mu.
Meye kiranka ga jama’ar mazabarka?
Mutanen mazabata, wadanda nake so in wakilta, ina kira gareku tun daga iyaye maza da mata da matasa da dattawa da kuma musamman sarakunan masu daraja de cewa ina neman goyon bayanku a kan wannan manufa tawa. Sannan kuma ina kira gare ku da bude idanunku da kyau ku zabi wanda ya cancanta ya wakilce ku.