Domin yi wa al’umma hidima nake takara – Ali Pate
Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PRP, Dokta Muhammad Ali Pate ya ce ba wani abu ne ya sanya shi shiga takarar Gwamnan Jihar Bauchi ba, sai burinsa na yi wa jama’a hidima da kuma ganin ya kawo wa jiharsa da kasa ci gaba. Dokta Muhammad Ali Pate ya bayyana haka ne ga […]
Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PRP, Dokta Muhammad Ali Pate ya ce ba wani abu ne ya sanya shi shiga takarar Gwamnan Jihar Bauchi ba, sai burinsa na yi wa jama’a hidima da kuma ganin ya kawo wa jiharsa da kasa ci gaba.
Dokta Muhammad Ali Pate ya bayyana haka ne ga Aminiya, yayin da yake bayyana kudirori da dalilin da suka sanya ya shiga siyasa da kuma burinsa na ganin ya zama Gwamnan Jihar Bauchi a badi.
Ya ce, “Za mu mai da hankali wurin samar da managartan ayyukan yi ga matasa, sannan mu ba da tallafi ga kanana da matsakaita da manyan manoma da kuma samar musu da managarciyar kasuwa da za su sayar da amfanin gonarsu. Mun yi kudirin gina masana’antu da cibiyoyin da za su tallafi aikin gona da madatsan ruwa don noman rani.”
Da aka tambaye shi ta yaya zai aiwatar da wadannan kudirori nasa ga al’umma idan ya samu nasara, sai ya ce: “Za mu samar da wadannan ne ta sabuwar hanyar hada-ka tsakanin gwamnati da masu zuba jari na kasashen waje in sha Allah. Da haka za mu mai da jiharmu ta zama kofar arziki ga Arewa maso Gabas.
“Mun kudiri cewa za mu dawo da martabar cibiyoyin gwamnati, ta yadda ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho da malaman makaranta da ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro da iyayenmu masu sarautar gargajiya da shugabannin addini za su samu hakkokinsu da kwarewa, yadda za su yi wa al’ummarmu aiki cikin kwaciyar hankali,” inji shi.
Dokta Muhammad Ali Pate ya zabi Barista Ahmed Farouk Gwadabe ne domin mara masa baya a matsayin Mataimakin Gwamna, inda zai fafata da akalla manyan ’yan takara na Jam’iyyar APC da ke da Gwamna da ke son zarcewa zango na biyu, Muhammad Abubakar da na Jam’iyyar PDP, tsohon Ministan Birnin Tarayya Abuja, Sanata Bala Mohammed.