Domin zaman lafiya muka kafa kungiyarmu -Shugaban ’Yan Nijar a Kurosriba
Aminiya ta tattauna da Shugaban kungiyar ’Yan Nijar Mazauna Jihar Kurosriba, Alhaji Nasiru Ishaka, kamar haka: Yaushe ne kuka kafa wannan kungiya kuma mene ne makasudinta? Mun kafa wannan kungiya ce a 2011 kuma sanadin kafa ta shi ne, mu dai mutane ne masu son zaman lafiya kuma masu bin doka da oda. Wannan kungiya […]
Aminiya ta tattauna da Shugaban kungiyar ’Yan Nijar Mazauna Jihar Kurosriba, Alhaji Nasiru Ishaka, kamar haka:
Yaushe ne kuka kafa wannan kungiya kuma mene ne makasudinta?
Mun kafa wannan kungiya ce a 2011 kuma sanadin kafa ta shi ne, mu dai mutane ne masu son zaman lafiya kuma masu bin doka da oda. Wannan kungiya ba a nan Kurosriba ma kadai ta tsaya ba, ko’ina a fadin wasu sassa na kasashen duniya kama tun daga kasashen Afirika, zuwa kasashen Larabawa; a takaice ina ga kasashe 99 na duniya akwai ta, an kafa ta ne a lokacin Jamhuriyar Nijar ba ta da gwamnati, tana karkashin gwamnatin rikon kwarya, lokacin da aka yi taron makomar kasa. Sai asalin shugabanninmu na Nijar suka ce akwai mutanenmu ga su nan a duniya sun watsu kuma suna da amfani ga iyayensu da kuma Nijar, su da suke zaune a waje akwai amfanin da ake samu a jikinsu; idan wani ya turo da kudi idan wani abu ya faru a kasa. Sai aka ce to me za a yi masu, wanda zai amfana gare su yadda za su more, su zauna lafiya a kasashen da suke? Shi ne sai aka ce to a kafa wannan kungiya. To, ka ji wannan shi ne makasudun kafa wannan kungiya kuma ko’ina take alamunta duk iri daya ne, babu wani bambanci a tambarinta da alamunta, ko nan Afirika da Asiya da kuma sauran kasashen Turawa; bambancinnsu kawai sunan kasar da kake zaune amma komai daya ne. Ko’ina ka je da katinka ka nuna a kowace kasa.
Wane irin ayyuka wannan kungiya take yi wa ’ya’yanta, musamman Jihar Kurosriba da kake shugabanta?
Alhamdu lillahi, gaskiya wannan kungiya tana yi wa ’ya’yanta ayyuka iya matuka, matukar dai kai dan Nijar ne kuma kana karkashin kungiyar nan, to duk wani abu da ya faru da kai na alheri, ko na akasi, Allah Ya kiyaye, kungiya tana iyakar bakin kokarinta ta ga cewa damuwarka din nan an yi maganinta. Daga cikin abubuwan da muke taimaka wa membobinmu, akwai bangaren haihuwa idan an yi wa mutu ko aure ya samu mutum ko hadari shi ma muna taimakawa.
Kuna da wani aiki da kungiya za ta iya yin tinkaho da shi, wanda ta yi wa ’ya’yanta, tun da aka kafa ta?
kwarai kuwa, akwai ayyuka da daman gaske, to ka san a nan Najeriya akwai matsalar nan ta Boko Haram; farkon tashinsa abin da ake zargi shi ne wai akwai hannun ’yan Nijar ciki kuma mu, mun tabbatar wa hukuma cewa mutanenmu ba su cikin wannan kungiya ta Boko Haram, a kodayaushe mun yi ta kokarin gaya wa gwamnatin Najeriya da ta Kurosriba wannna abu ba abun da ya shafe mu ba ne kuma babu wani dan Nijar da ke cikinta domin idan ban manta ba, shekarar da ta wuce kamar wata goma sha biyar da suka wuce, mun yi wani zama a Abuja; mu da manyanmu na kasarmu, da kuma shugabannin kungiya na sauran sassan Najeriya, karkashin jagorancin Gwamnatin Najeriya, muka nunar masu cewa ’yan Nijar ba su cikin wannan kungiya.
Idan mun fahimce ka, kamar kun wanke kanku daga zargi ke nan?
Yauwa, hakika wannan mun wanke kanmu daga zargin da ake yi mana kuma hukumar Najeriya ta yarda, ta kuma gamsu da hakan, ta kuma tabbatar da cewa haka ne. Gwamnatin Najeriya ta nuna mana tun da ake ba mu taba zama na fahimta ba tsakaninmu kamar irin wannan zaman, sun gamsu cewa lallai-lallai ba mu da hannu cikin lamarin Boko Haram.
Tun da ka yi bayanin yadda kuke ta ganin cewa an fahimce ku, ku masu son zaman lafiya ne, me kuke yi ta fuskar wayar da kan ’yan kungiya, domin su kara sanin fa’idar zaman lafiya, musamman nan Kudu maso kudu da kuke zaune?
Eh! Muna ci gaba da fadakar da su da yi masu gargadi da jan kunne, dayake muna taro kowane mako. Duk ranar Lahadi muna yi masu gargadi kada su shiga duk wata harka da ba tasu ba kuma kada su shiga abun da bai shafi kasarsu ba. Duk abun da bai shafe su ba, kada ma su je kallo ko su tsaya wurin, su ci gaba da nuna su baki ne; abinci suka zo nema ba tashin hankali ba.