‘Don bunkasa kasuwanci muka kafa kungiyarmu’
Shugabannin kungiyar masu sayar da busasshen barkono da ke kasuwar Whiteson a unguwar Oyingbo a Jihar Legas sun ce sun kafa kungiyarsu ne don bunkasa kasuwancinsu. Shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar Shu’aibu ya shaida wa Aminiya a karshen makon da ya gabata cewa kungiyar ta samu nasarori da yawa tun lakacin da aka kafata.Ya ce ‘Mun […]
Shugabannin kungiyar masu sayar da busasshen barkono da ke kasuwar Whiteson a unguwar Oyingbo a Jihar Legas sun ce sun kafa kungiyarsu ne don bunkasa kasuwancinsu.
Shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar Shu’aibu ya shaida wa Aminiya a karshen makon da ya gabata cewa kungiyar ta samu nasarori da yawa tun lakacin da aka kafata.
Ya ce ‘Mun kafa kungiyarmu tun shekara 13 da suka wuce kuma mun ci nasarori da dama. Dalilin da ya sa muka kafa ta shi ne don ci gaban sana’armu da kuma hadin kanmu da kyakkyawar zamantakewa da abokanan huldarmu. Da farko mun fara kungiyar da mutane 20 daga bisani muka gayyaci jama’a su shigo. Mun gode wa Allah mutane sun amsa kiran da muka yi musu sun shigo cikin kungiyar ba tare da wata matsala ba.’
Ya ci gaba da cewa “Kuma zancen da nake yi da kai mun cimma burin da muka sanya a gaba kamar taimakon juna da biyan kudin magani ga marasa lafiya. Kuma ba zan ce ba mu da matsala ba, muna da matsaloli da ba a rasa ba amma mun gode wa Allah da irin taimakon da yake yi mana. Kuma muna da ’yan kungiya masu biyayya ga shugabannin ba tare da tayar da kayar baya ba.”
Shi ma sakataren kungiyar, Malam Aliyu Gula Sumaila ya ce daya daga cikin nasarorin da suka samu shi ne samun membobi fiye da 500.
Ya kara da cewa kungiyar tana da alaka da sauran takwarorinta da ke kasuwar Alaba da Mil 12 da sauran kasuwanni daban-daban.
Mataimakin Shugaban kungiyar, Alhaji Halilu Sumaila ya bayyana cewa zaman lafiya na daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu.