Don in tsiyace aka sa Shata ya yi mini waka –Bawa Gilban
“Haji Bawa Gilban Jibiya, Masu kudi na Katsina, Mai arziki na Jibiya, Wannan da Allah Ya tsare,Haji Bawa Gilban Jibiya.” Maman Shata a wakarsa ta Bawa Gilban Alhaji Bawa Gilban Jibiya tsohon direba kuma shararren dan kasuwa, gogaggen dan siyasa ne wanda a lokacin da yake cikin ganiyarsa ya ja hankalin wasu abokan harkarsa suka […]

“Haji Bawa Gilban Jibiya,
Masu kudi na Katsina,
Mai arziki na Jibiya,
Wannan da Allah Ya tsare,
Haji Bawa Gilban Jibiya.”
Maman Shata a wakarsa ta Bawa Gilban
Alhaji Bawa Gilban Jibiya tsohon direba kuma shararren dan kasuwa, gogaggen dan siyasa ne wanda a lokacin da yake cikin ganiyarsa ya ja hankalin wasu abokan harkarsa suka hada shi da Likitan Mawaka Alhaji Mamman Shata ya yi masa wakoki.
Aminiya ta gana da Alhaji Bawa Gilban a garin Jibiya don jin yadda aka yi har Dokta Mamman Shata ya wake shi:
Aminiya: Za mu son jin takaitaccen tarihinka?
Alhaji Bawa Gilban: To! Sunana Bawa Gilban, an kuma haife ni ne a nan garin Jibiya a wata unguwa da ake kira Unguwar dandashe kimanin shekara 72 da suka wuce.
Aminiya: To ina maganar ilmi?
Alhaji Bawa: An kai ni makaranta a garin Malumfashi. To ka san karatun allo wuya ke gare shi. Da na ji wuya ta ishe ni, sai na gudo na dawo gida. Da na dawo gida sai na ci gaba da yin dako a nan kasuwa. A wancan lokacin nan ba kowa, fili ne, sai kasuwar kawai ita ma an zagaye ta da wata ’yar waya. To, wajen wannan sana’a ta dako muka hadu da Gilban. Shi Gilba Ibo ne. To duk lokacin da Gilban ya dawo daga Maradi ni nake yi masa dakon kayansa zuwa gida. Ganin irin halayena ya sa Gilban ya dauke ni ya mayar da ni yaron motarsa.
Aminiya: Ba ka ci gaba da karatu ba?
Alhaji Bawa Gilban: Karatu ai barin shi na yi. Yo ga mota a wancan lokaci kuma ga yaro matashi irina? Ai mota ta yi rinjaye. Wata rana sai Allah Ya jarabci Gilban da ciwon ido, to sai ya aike ni wajen wani direban da ake ce wa Alhaji Abdu Bagobiri in gaya masa ya je ya dauki mota ya dauko mutane daga wani garin da ake ce wa Jiratawa da ke Maradi. Abdu Bagobiri sai ya ce, ba ya tuka motar Inyamuri (Ibo). To wannan abu ya bata wa Gilba rai, sai ya sa harshe ya lashi yatsarsa ya daga sama ya ce, sai ya koya min mota a cikin wata biyu. Haka kuma aka yi. Zanga-zanga ta raba ni da Gilba, amma ya tafi ya bar mana mota ni da dan kamashonsa ana ce masa Maidamma. Maimakon mu ci gaba da aiki tare sai suka hada baki da matarsa wata Bayarbiya suka kore ni. To dama mota ta inshora ce, su kuma suka amshe abinsu tunda ba a biya su ba. Ran nan sai Alhaji Mamman Zigau ya sayo mini mota Tanis. To da wannan mota ce har Allah Ya sa na mallaki tawa, har ma aka wayi gari na ci gaba da sayo motoci ina sayarwa.
Aminiya: To me ya hada ka da Shata har ya yi maka waka?
Alhaji Bawa Gilban: Abin da ya hada ni da Shata, akwai wani tsohon direba ana kiransa Atti Dan-kanan-kaza, a wancan lokaci ana sayar da motoci domin ina dauko mota sama da 30 daga Ibadan. To shi Atti sai ya kira Shata lokacin zan yi bikin ’yata, ya ce wa Shata ka zo ka je Jibiya ka yiwo wa wannan yaro barna, amma duk motocin da ka kwashe daga wajensa ka kawo min ni zan saya. Shata ya zo aka kai shi can inda ake sayar da motocin ya gansu birjik, can sai ya ga wata ’yar Baswaja wadda nake dan yawo da ita cikin gari. Sai Shata ya ce mini, “Alhaji Bawa na lura masu arziki ba su kaunarka, kamar yadda ni Shata nake da sauran mawaka da maroka. To da ni da kai za mu yi abota. Kuma Alhaji Atti Dankanan Kaza shi ya turo ni in yi maka barna. To ka ga wannan ’yar motar karama? To ni ita nake so.” Na ce masa ga ta nan. Na ba shi makulli. Nan fa ya kwana yana kidansa. Kuma a nan ne ya yi mini waka. Yana cewa: “Wani wanda Allah Ya tsare kamar shi ne Shata a maroka, Shatan da Allah Ya tsare. Shata ya ce, mun kulla amana da shi domin ni duk mutumin da ka ga an tura ni wajensa, to ana iya turo barawo ya kashe shi, don ni kamar wutar daji nake mai daukowa daga bangon Gabas sai ta kai bangon Yamma.”
Aminiya: Shi ya sa a cikin wakar yake cewa, “Masu kudi na Katsina, Mai arziki na Jibiya?
Alhaji Bawa Gilban: Ai na san koda su wa yake nufi masu kudin, har da ’yan tara garwar mota a kofar gida.
Aminiya: Wato an turo Shatan ne da nufin a tsiyataka?
Alhaji Bawa Gilban: kwarai da gaske! Wanda za a dauke masa dukiya a kwashe, yo ba an tsiyata shi ba? Ai motocin ake so a kwashe.
Aminiya: To kai lokacin da yake yi maka wakar akwai wani abin da ka ji?
Alhaji Bawa Gilban: Lokacin da yake yi mini waka ai duk duniyar nan ba na jin kidan kowa in ba nasa ba ne.
Aminiya: Ke nan akwai wasu baituttukan da ya yi da suka tsuma ka?
Alhaji Bawa Gilban: kwarai kuwa, inda yake cewa: “Na kan gada dan Mamman. In kana so ka ga Bawa tilas ne ka bi uku. Kodai ka hau gada ka je, koko ka hau bisa rairai ko kuma ruwa kirjinka.”
Aminiya: Ashe da ya ce maka ka ba shi motocin a lokacin da ka ba shi?
Alhaji Bawa Gilban: Tuni ma na ba shi. Yo Shata ya ce maka yana son abu, ai sai in bayan ka ba shi ya tafi kai kuma kyarma ta kwace maka. Kai ni fa har ya mutu ban taba kirga kudi ba in zan ba shi, a duk inda muka hadu sai dai yadda suke a daure, in mika masa. Mun kuma sha haduwa da shi a irinsu Maiduguri da makamantansu, kuma ko wakar wa yake yi da ya gan ni zai kama tawa.
Aminiya: Ko kana ganin za a iya samun wanda zai canje shi?
Alhaji Bawa Gilban: Ba dai a wannan iskar mai kadawa ba. Ni fa jin sauran mawakan kawai nake yi suna kwaramniya, amma waka ai sai Shata.