Don inganta rayuwar matasan Bauchi muka kafa kungiyarmu – Malam Yazid

Malam Yazid Malamin Kasuwa shi ne Shugaban kungiyar Kobi Youths Awareness Forum kungiyar da take wayar da kan matasa game da illolin shan miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma. A wannann tattaunawarsa da wakilinmu ya yi fashin baki game illolin da ke tattare da zaman kashe wando a tsakanin matasan kasar nan da sauransu. Ga yadda […]

Don inganta rayuwar matasan Bauchi muka kafa kungiyarmu – Malam Yazid
Don inganta rayuwar matasan Bauchi muka kafa kungiyarmu – Malam Yazid

Malam Yazid Malamin Kasuwa shi ne Shugaban kungiyar Kobi Youths Awareness Forum kungiyar da take wayar da kan matasa game da illolin shan miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma. A wannann tattaunawarsa da wakilinmu ya yi fashin baki game illolin da ke tattare da zaman kashe wando a tsakanin matasan kasar nan da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Za mu so ka fara gabatar da kanka?
Malam Yazid: Sunana Yazid Malamin Kasuwa, Shugaban kungiyar ta Kobi Youths Awareness Forum, kungiyar da ta ke wayar da kan matasa game da mahimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma sannan kuma muna da dimbin mambobi maza da mata kuma kashi 95 cikin 100 na mambobin kungiyarmu suna da sana’a. Domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba, sai matasanta kowa ya kama sana’a kuma muna yaki da zaman kashe wando da shan miyagun kwayoyi. Yawan mambobinmu ya zarce sama da mutum 300.
Har yanzu muna ci gaba da yin rijista ga sabbin mambobin kadan daga cikin manufofin kafa kungiyar shi ne hada kan matasan Jihar Bauchi waje guda. Matasan sun kunshi ’yan siyasa da wadanda ba ’yan siyasa ba. A duka kananan hukumomin Jihar Bauchi guda 20 muna da mambobi wanda suke wayar da kan matasa game da muhimmancin zaman lafiya.
Aminiya: Wadanne hanyoyi za a bi wajen dakile rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar nan?
Malam Yazid: Hakika idan ka duba sosai matasa suna ba da gagarumar gudunmawa a lokacin kamfe, amma da zaran an kafa gwamnati sai kaga wasu shugabannin sun yi watsi da su. Saboda haka za mu ci gaba da addu’a ga wadanda muka zaba Allah Ya ba su damar cika alkawuran da suka dauka.
Maganar gaskiya shi ne tsoffin shugabannin da suka gabata sun lalata komai a kasar nan kuma da gangan suka jefa al’umma cikin mawuyacin hali na talauci da rashin kwanciyar hankali. Kashi 55 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba sa cin abinci sau uku a rana. Saboda yadda talauci ya yi mana kamun kazar kuku, amma yanzu muna godiya ga Allah bisa wannan nasara da muka samu Muhammadu Buhari yau shi ne shugaban Najeriya, a nan Bauchi kuma Barista Mohammed Abubakar shi ne sabon gwamnanmu.
Da yawa daga cikin matasan da ake amfani dasu wajen tada zauna tsaye matasa ne wanda ba su da aikin yi saboda haka idan aka basu kudi kadan sai su ta da zaune tsaye.
Aminiya: Me kake so gwamnan Jihar Bauchi ya yi wa matasan jihar nan?
Malam Yazid: Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar tabbas yazo da manufofi masu kyau na bunkasa rayuwar matasan Bauchi, sai dai muna fatar za a taya shi da addu’a domin akwai masu zakon kasa a gefe. Kuma ya kamata matasa su fahimci cewa wannan gwamnati ba za ta rika daukan kudi tana raba wa wasu mutane ’yan tsiraru ba aiki za a yi a kasa wanda zai shafi rayuwar kowa da kowa ba. Ina albishir ga matasan Najeriya nan da badi abubuwa za su daidaita domin Shugaba Buhari zai yi aiki a sama da kasa kuma Barista Abubakar zai ci gaba da shimfida ayyukan raya kasa ga talakawan Bauchi.
Aminiya: Me ye sakonka ga wadanda suka yi sama da fadi da kudin al’umma?
Malam Yazid: Sakona ga wadanda suka yi wasoso da kudin talakawan Jihar Bauchi shi ne yakamata duk wanda yasan ya yi cuwa-cuwa da kudin talakawa ya yi sauri ya dawo da abin da ya dauka domin gwamna ya nada Alhaji Tijjani Baba Gamawa a matsayin shugaban kwamitin karbo kayayyakin gwamnati da aka sace a waccen tsohuwar gwamnati.
Saboda haka wannan kungiya muna fatan idan gwamna yazo nada sabbin kwamishinoni zai mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana wanda suka yi wahala a lokacin kamfe.
Muna ba da shawara ga wadanda za a ba su mukamai daban-daban a gwamnati a fahimci cewa duk wanda yazo da niyyar zai yi kudi a sabuwar gwamnatin Bauchi, to tabbas yana yaudaran kansa ne domin talakawa ne suka zabi gwamnatin saboda haka za a fi ba da fifiko wajen aikin raya kasa don amfani kowa da kowa.
Aminiya: Me ye sakonka ga ma’aikatan Jihar Bauchi?
Malam Yazid: Ma’aikatan gwamnati Jihar Bauchi muna fatar za su ba da goyon bayansu ga wannan gwamnati domin gwamnatin da ta gabata ta hana ma’aikata albashinsu na watanni biyu don haka ayi hakuri komai zai daidaita nan da wani lokaci. Har ila yau, sakona ga matasa shi ne don Allah a kama sana’a a daina yawon roko a tsakanin al’umma. Na biyu ayi hakuri da abin da aka samu komai kankantarsa Hausawa sun ce mai raina kadan barawo ne muna fatar sabbin shugabannin da aka zaba za su ba da kulawa ta musamman wajen samarwa matasa hanyoyin samun kudin shiga.