Don Ma’aurata: Sunnonin Shagalin Sallah

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ina taya masu karatu murnar zagayowar ranar babbar Sallah tare da addu’ar Allah SWT Ya sa mu dace da alheran da cikinta. Ga tunatarwa ga ma’aurata kan kyawawan ayyukan da ya kamata su fi ba muhimmanci yayin gabatar da shagulgulan murnar babbar […]

Don Ma’aurata: Sunnonin Shagalin Sallah
Don Ma’aurata: Sunnonin Shagalin Sallah

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ina taya masu karatu murnar zagayowar ranar babbar Sallah tare da addu’ar Allah SWT Ya sa mu dace da alheran da cikinta. Ga tunatarwa ga ma’aurata kan kyawawan ayyukan da ya kamata su fi ba muhimmanci yayin gabatar da shagulgulan murnar babbar Sallah. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Sunnonin Shagalin Sallah:
1.    Ibada: Mu sani ya ’yan uwa, duk da kasancewar ranar Sallah rana ce ta murna da shagali da jin dadi, amma abu mafi muhimmanci a cikin wannan rana shi ne, kasancewarta ranar ibada. Kamar yadda aka ruwaito Manzon Allah SAW Yana cewa: “Abu na farko da za mu gabatar a wannan rana shi ne Sallah (sallar Idi); sannan layya…” don haka Sallar idi ya kamata ma’aurata maza da mata su fi ba muhimmanci sama da dafe-dafen abinci da shiryen-shiryen shagalin Sallah. Don haka kuskure ne abin da mafi yawa daga cikin matan Hausawa ke yi na kin zuwa sallar idi kawai don yin dafe-dafe da soye-soyen kayan abincin sallah. Ai zuwa idin nan shi ya fi alfanu sama da komai; don haka ne ma a lokacin rayuwar Manzon Allah SAW duka mata ne ke zuwa filin idi har masu jinin haila Annabi SAW ya umarce su da zuwa wajen da ake Sallar Idi, amma su tsaya daga baya suna kallon masu Sallah. Haka har macen da ba ta da hijabin da za ta rufe jikinta, an umarci ta nemi aron na ’yar uwarta ta tafi wajen Sallar idin. Wannan duk yana kara nuna mana matukar muhimmancin zuwa Sallar idi ga kowane Musulmi ba wai maza da kananan yara kadai ba. Don haka duk wata uwargida Musulma ta kwarai dole ta tabbatar ta karasa duk wani aikin abincinta kafin lokacin zuwa idi; in kuma ba halin haka to sai ta yi hakuri ta dawo, ta karasa domin zuwa idin ya fi komai muhimmanci a wannan rana.
2.    Sadaka: Haka kuma yana daga cikin ibadodin murnar Sallah yin sadaka ga talakawa da mabukata, domin Annabi SAW ya yi umarni yin hakan ga taron mata bayan idar da sallar idi, sai ya yi musu wa’azi, sannan ya umarce su bayar da sadaka, kuma take suka bi wannan kyakkyawan umarnin na Manzon Allah SAW, inda suka ruka ciro gwala-gwalensu suna bayarwa sadaka saboda Allah. Don haka ya ’yan uwa ma’aurata, musamman mata, mu yi kokarin yin koyi da wannan Sunna ta Manzon Allah SAW ta hanyar bayar da sadaka a wannan rana ta shagalin babbar Sallah. Ba dole sai mutum ya wadata sosai ba sannan  zai yi sadaka, in dai mutum ya yi ta da  kyakkyawar niyya, to Allah SWT Zai cika masa ladarsa. Misali kamar mutum ya bayar da sadakar kudi ga masallacin unguwarsu; ko ya sayi batir don a sa a lasifikar masallacin, ko katuwar fitila mai haske ko tabarma da butoci da sauransu. Ko taimakon wani mabukaci, ko taimaka wa gidajen marayu da kudi da sutura ko kayan abinci. Ko sayen magani ga marasa galihu a asibiti da sauran kyawawan ayyuka da mutum ya ga sun dace, sai ya yi don dacewa da wannan kyakkyawar sunna ta Manzon Allah SAW.
3.    Ranar Murna: Abu na uku mafi muhimmanci a wannan rana shi ne, kasancewarta ranar murna da shagali. Don haka yana da kyau kowane Musulmi yin murna a wannan rana, ta hanyar jin ta cikin zuciya, da bayyanar da ita a fuska da kokarin sa ’yan uwa da makwabta cikin nishadi ta hanyar kyakkyawar gaisuwa mai cike da raha, kalmomin kyautatawa da kuma yin abubuwan kyautatawa da jinkai ga kowa a wannan rana. Haka nan ya halatta yin wakokin nishadi masu dauke da kyawawan kalmomi, musamman mata da yara sunna ce mai kyau su aikata wannnan a ranakun murnar Sallah. Misali, yana da kyau a tara yaran unguwa a gabatar da wani abun wasa da jin dadi wanda zai sanya su cikin murna da farin cikin zuciya; ko macen aure ta tara ’yan matan unguwa su yi gada ko wakoki cikin wasa da dariya da raha, wannan duk ayyukan alheri ne wadanda idan mutum ya aikata su zai samu lada ga kuma nishadi da jin dadin da zai ji a zuciyarsa.
4.    Ranar Soyayya: Idan muka bibiyi sunnonin Manzon Allah SAW za mu ga cewa, ranar idin Sallah rana ce ta soyayya da romansiyya da kyautatawa tsakanin ma’aurata. Kamar yadda aka ruwaito uwar Mumunai A’isha Radhiyalla Anha ta ce, a ranar wata idin, ya kasance mutanen Habasha suna wasa da sulke da mashi a harabar masallaci, sai Annabi SAW Ya katange ta da jikinsa, ta yadda kuncinta yana bisa kuncinSa, kuma ya yi ta jiran ta har sai da ta kalla ya ishe ta. Wannan darasi ne mai kyau kuma abin koyi ga ma’aurata, ta yadda za su sadaukar da lokacinsu wajen nuna kauna da kulawa ga junansu a wannan rana ta idi. Don haka yana da kyau duka maza da mata su yi wani abu na sadaukarwa da nuna kulawa ga junansu ranar Sallah, don su dace da wannan Sunna, kuma su ji dadi da nishadin da ke cikin kyautatawa ga juna.  
5.    Ranar Zumunci: Yana da kyau ma’aurata su yi amfani da ranar murnar sallah wajen sada zumunci ga ’yan uwa, makwabta da abokan arziki; da yin musayar kyawawan kalmomi masu dadada rai tsakaninsu. Lokaci ne mai tsada na samun lada kuma zumunci mun san babban al’amari ne mai matukar muhimmanci. Sannan iyaye su guji dabi’antar da yaransu zuwa yawon Sallah don kawai su samo kudin barka da Sallah, ya fi dacewa a nuna musu muhimmancin sada zumunci a kuma kwadaitar da su lada da albarkar da za su samu idan suka yi zumunci don Allah kadai ba da niyyar samo kudin barka da sallah ba!
6.    Ranar Kwalliya: Yana daga cikin kyawawan Sunnonin murnar Sallah kure adaka da yin kwalliya mai kyau, musamman lokacin zuwa Sallar idi da kuma zama cikin kwalliya da shiga mai kyau daukacin wannan rana, don haka kada aikace-aikacen abincin Sallah ya sa a zauna da tsofaffin kaya, kuma ba ado ba kwalliya; yana da kyau a yi aikin wannan rana da shiga mai kyau kuma da kwalliya ta yadda kowa zai rika kyalli da haskakawa.
Allah Ya sa mu yi shagalin Sallah lafiya, amin.