‘Don magance cutar shan-inna muka kafa kungiyarmu’

Shugaban kungiyar masu shan-inna Malam Aminu Ahmed Tudun Wada ya ce sun kafa wannan kungiyarsu domin ba da gudummawar su wajen kawar da cutar shan-inna daga Jihar Kano da kuma kasar nan. Ya yi wannan bayani ne a ganawarsu da Aminiya jim kadan bayan kaddamar da zagayen allurar riga-kafin cutar shan-inna ranar Asabar din makon […]

‘Don magance cutar shan-inna muka kafa kungiyarmu’
‘Don magance cutar shan-inna muka kafa kungiyarmu’

Shugaban kungiyar masu shan-inna Malam Aminu Ahmed Tudun Wada ya ce sun kafa wannan kungiyarsu domin ba da gudummawar su wajen kawar da cutar shan-inna daga Jihar Kano da kuma kasar nan.

Ya yi wannan bayani ne a ganawarsu da Aminiya jim kadan bayan kaddamar da zagayen allurar riga-kafin cutar shan-inna ranar Asabar din makon jiya.
Ya bukaci iyayen yara su rika ba da ’ya’yansu a rika yi musu rigakafi don kaucewa kamuwa da wannan muguwar larura ta shan inna.
Ya kara da cewa “Babu shakka ta hanyar rigakafi ana dacewa da kawar da kowace irin larura, domin an ga yadda aka kawar da cutar kuturta da cutar ’yar rani da kuma kurkunu, wanda a halin yanzu babu wadannan cututtuka sakamakon riga-kafin da aka rika yi.”
Ya ce a matsayinsu na masu cutar shan-inna sun fi kowa sanin illolinta da kuma fa’idar yin riga-kafi.
“Don haka za mu kara zage damtse wajen ceto al’umma daga wannan cuta mai nakasa dan Adam cikin yardar Allah.”
Ya ce kafin su kafa wannan kungiya, ana samun bullar cutar a sassa daban-daban na Jihar Kano da wasu bangarori na kasar nan, amma a yanzu an samu raguwar kamuwa da ita, saboda wayar da kan al’umma da kungiyar su keyi dare da rana.
Ya ce “Akwai dangantaka mai kyau tsakanin kungiyarmu da sauran hukumomin gwamnati da na kula da lafiya da kuma wasu cibiyoyi a kasashen waje, kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu kwarai.”
Ya ba da misali da kungiyar kula da lafiya ta duniya WHO da ta UNICEF da ta USAID da kulob din ROTARY, wadanda suke aiki tare bisa kwazo da fahimtar juna a duk lokacin aikin kawar da cutar shan-inna a Najeriya.
Sauran wadanda suka yi tsokaci akwai ma’ajin kungiyar Malam Ayuba Bello da Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Alhaji Muhammadu KT wadanda suka nuna yadda kungiyar ke tafiyar da aikace-aikacenta na yau da kullum, duk da halin da take ciki na bukatar tallafi.
Sun bukaci Gwamnatin Jihar Kano da kungiyoyin kula da lafiya da hukumomin kula da lafiya da sauran mahukumta da su rika taimaka wa kungiyarsu don ta rubanya aikinta.
Daga karshe, kungiyar ta bukaci masu jagorancin al’umma da masu iko da su rika sayen kekunan guragu da suke kerawa domin taimaka wa guragun yankunansu wadanda ba su da ikon sayen kekunan da za su rika hawa.

 

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya