Don maigida: Dabarun zama da mata sama da biyu
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. A wannan makon za mu karasa bayani kan dabara ta farko watau (bin umarnin Allah Madaukaki) wajen zama da mata sama da biyu, sannan mu ci gaba da sauran dabarun inshaAllah; […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. A wannan makon za mu karasa bayani kan dabara ta farko watau (bin umarnin Allah Madaukaki) wajen zama da mata sama da biyu, sannan mu ci gaba da sauran dabarun inshaAllah; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Domin natsuwarku
A cikin Aya ta 21 cikin Suratul Rum, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kawunanku, domin ku natsu zuwa gare su; sannan Ya sanya soyayya da rahma a tsakaninku…”
Sai zuciya ta natsu ruhi ya sanyaya, sannan gangar jiki take iya hutawa. Zuciya na natsuwa da duk wani abu mai kyau, mai tsarki kuma mai aminci. Duk maigidan da ke son ya natsu da matansa, dole sai ya natsar da zuciyar matan nasa, domin ran da ba natsuwa a cikinsa, ya za a yi ya iya natsar da wani rai? Kafin magidanci ya iya natsar da zuciyar matansa dole shi ma sai ya natsar da tasa zuciyar, hanyoyin natsar da zuciya suna da yawa: amma dai muhimmin daga cikinsu shi ne, kadaita Allah Madaukakin Sarki da bin umarninsa da kauce wa duk wani abu da ya yi hani da shi, wannan yana tabbatar da natsuwa cikin zuciya. Hanyar da maigida zai natsar da zuciyar matansa kuwa shi ne, ta hanyar tabbatar masu da aminci, so da kauna da ba su yankewa.
Tabbatar da wannan ga mace daya ma ba karamin aiki ba ne ga mazan wannan zamani, ballantana kuma ga mata sama da 1 a bayanin dabara ta uku da ta hudu za mu ji yadda maigida zai iya yin hakan Insha Allah.
Dabara ta 2: Koyi da sunnar Manzo SAW
Annabinmu masoyinmu SAW ya kasance ba mutumin da ya kai shi kwarewa wajen iya zama da mutane ko wadanne iri ne, haka kuma ba wanda ya kai shi iya zama da mata da iya kula da su da nuna musu soyayya; tun da kuwa ya zauna da mata har 9 a lokaci daya, kuma ba abin da ya faru tsakaninsu na tashin hankali sai dai dan kishin da ba a rasa ba, wanda wannan kuma halitta ce da ba mai iya boyewa. Irin wannan kishin ne da ya bayyana tsakanin iyayenmu mata za mu kawo da irin yadda Ma’aiki SAW ya yi a kowane irin yanayi.
1. Annabi SAW bai taba amince wa daya daga cikin matansa ta ambaci daya da ambato marar kyau ba, koda a bisa kowane irin dalili ne, sai ya nuna mata ba ta yi daidai ba. Misalin irin haka shi ne: Lokacin da annabi SAW ya auri Ummuna Safiyya Bint Huyay RA a yakin Khaybar. Bayan sun dawo Madina ya zaunar da ita a wani gida mallakin Haris bin Annu’aman RA; matan Madina sun fito don ganinta saboda sun ji an ce tana da kyau, cikinsu har da Ummuna Aisha RA amma ta rufe fuskarta da mayanin rufe fuska, duk da haka Annabi SAW ya gane ta, don haka sai ya same ta ya ce da ita “Me kika gani ya Shukaira?” Cikin fushin da kishi, sai ta ce da shi: “Me na gani kuwa in ban da Bayahudiya!?” Sai Annabi SAW ya ce da ita kada ki ce haka, domin kuwa ta musulunta!”
Haka kuma wata rana kanwar Ummuna Khadija ta yi sallama ga Annabi SAW, sai ta tuna masa da irin yadda Ummuna Khadija kan yi sallama, sai hankalinsa SAW ya tashi da begen Ummuna Khadija. Wannan ya sa kishi ya turnike Ummuna Aisha Har ta ce da shi SAW: “Me ya sa kake tunawa da wata tsohuwa wacce hakoranta sun zube bayan Allah SWT Ya musanya maka da wata wacce ta fi ta?” Sai Annabi SAW ya ba ta amsa da cewa: “Har yanzu Allah bai ba ni wacce ta fita ba.”
Haka kuma akwai lokacin da Annabi SAW ya yi tafiya tare da Ummuna Safiyya da Zainab Bint Jahsh RA, sai taguwar Ummuna Safiyya ta samu matsala, sai Annabi SAW ya bukaci Ummuna Zainab ta bayar da aron daya daga rakumanta ga Ummuna Safiyya, sai ta fada cikin kishi: “Yanzu sai in bayar ga wannan bayahudiyar?” Sai Annabi SAW Ya juya ya bar ta cikin fushi kuma a kan haka sai dai ya yi wata biyu zuwa uku baya kula ta ba kawai don ya nuna rashin amincewarsa a kan kalamin da ta yi.
Wata rana Annabi SAW ya iske Ummuna Safiyya RA tana kuka, sai ya tambaye ta ko lafiya, sai take gaya masa ai Ummuna Hafsa RA ta ce mata ita Bayahudiya ce, sai Annabi SAW ya lallashe ta da kalamai masu dadi don ya kore mata bacin ran da take ciki; ya ce da ita: “Lallai ke diyar Annabi ce (watau Annabi Harun AS) kuma lallai Kawunki ya kasance Annabi ne (watau Annabi Musa AS), sannan tabbas ke matar Annabi ce, don haka mene ne na bata ranki a kai?” Sannan Ya ce da Ummuna Hafsa: “Ki ji tsoron Allah Yake Hafsah!”
2. Yana hakuri da su ta fannin kishinsu, ba ya masu fada ko ya hantare su saboda bayyanar wani bangare na kishinsu. Akwai Lokacin da daya daga cikin matansa ta aiko masa da abinci alhalin yana dakin daya; sai wacce yake dakin ta tasa hannu ta buge akushin abincin ya fadi ya fashe, abincin ya zube a kasa; Annabi SAW da kansa ya kwashe abincin sannan ya sa aka nemo wani kwano aka mayar wa wacce natan ya fashe, bai hau ta da fada ba, bai kuma ji haushinta ba, don ya san yadda karfin shaukin kishi yake yayin da ya motso ga ‘ya mace, sai dai ya ce da dan aiken “Kishi ne ya kama mahaifiyarka.” (watau Uwar Muminai).
Sai mako na gaba za mu kare wannan bayani Insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.