Don Maigida: Ladubban Saki (2)
Ladabi na 10: Sa Shaidu: Kamar yadda aure bai inganta sai da shaida shi kuma saki ana ingantashi da kyautatashi ta hanyar sanya shaidu guda biyu lokacin yinsa, ba sharadi ne na dole sai shaidan ba, amma yin haka abu ne mai kyau kuma yana kawar da gardandami tsakanin ma’aurata daga baya. Don haka ko […]
Ladabi na 10: Sa Shaidu: Kamar yadda aure bai inganta sai da shaida shi kuma saki ana ingantashi da kyautatashi ta hanyar sanya shaidu guda biyu lokacin yinsa, ba sharadi ne na dole sai shaidan ba, amma yin haka abu ne mai kyau kuma yana kawar da gardandami tsakanin ma’aurata daga baya. Don haka ko a baki mutum ya furta, ko a takarda ya rubuta duka sai ya sanya shaidu guda biyu, in a takarda ce shaidun nan biyu sai sun sa mata hannu. Shaidun dole su kasance mazaje biyu masu cikakken hankali, mutanen kirki masu gaskiya, rikon addini da rikon amana. In ba a samu maza biyu ba to namiji daya da mace biyu ko mata hudu.
Ladabi na 11: Saki daya; ba a yin Saki biyu ko uku lokaci daya, irin wannan saki ya fita daga tsarin Musulunci, sai dai saki daya kadai a lokaci daya, sai bayan an maida ita ne za a iya yin wani saki dayan sai ya zama biyu da sauransu. Amma ko mutum ya ce na sake ki saki biyu a lokaci daya yana nan a matsayin saki daya.
Ladabi na 12: Haramcin tsawaita idda da gangan. Tsawaita idda shi ne magidanci ya bari sai matar da ya saka ta kusa gama idda sai ya mayar da ita ba a dalilin ya zauna da ita ba sai dalilin ya kara sakinta ta kara yin wata iddar. Yin haka zalunci ne kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fada cikin Suratul Bakarah Aya ta 234: “Kuma idan kuka saki mata sa’annan suka isa ga ajalinsu, sai ku rikesu da alheri ko ku sake su da alheri. Kuma kada ku rike su akan cutarwa domin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan to hakika ya zalunci kansa. Kuma kada ku riki Ayoyin Allah da izgili…”
Don haka komai ya halatta ne kadain akwai kyakykawar niyyar cigaba da zaman aure, duk wanda ya yi komai da niyyar cutarwa to kansa zai cutarwa kuma ya riki zunubi mai girma na yin izgili da Ayoyin Allah.
Ladabi na 13: Kyautar Bankwana: Allah Madaukakin Sarki Ya yi umarni ga mazaje su bayar da kyautar dadadawa ga matan da suka saka kamar yadda ya zo a Aya ta 241 cikin Suratul Bakarah. “Kuma wadanda aka saki suna da dadadawa gwargwadon hali wajabce akan masu takwa.”
Haka kuma a Aya ta 26 cikin Suratul Ahzab an kara bayyanar fa muhimmanci da wajabcin yin kyautar bankwana lokacin saki: “Ya Kai Annabi ka cewa Matanka, idan kun kasance kuna nufin rayuwar duniya da kawarta. To ku zo in yi maku kyautar ban-kwana kuma in sake ku saki mai kyau.”
Don haka wannan kyauta dole ce kuma wajibi ce kamar yadda Ayar ta bayyana. Kuma duk magidanci da ya saki matarsa ba tare da bayar da wannan kyauta ba alhali yana da ikon yin haka kuma yana da masaniya, to ya sani hakkin hakan na nan akansa sai dai in ita ce ta ce ta yafe masa.
Ga matar da aka saki kafin kadaitar ibadar aure da ita ya faru, kuma ya kasance ba a kai ga ba ta sadakinta ba, to ita ma ana mata wannan kyautar dadadawa daidai gwargwadon hali. Da mai kudi da talaka kowa zai bayar gwargwadon iyawarsa, kamar yadda ba daidai ba ne ga talaka ya kure kansa ko ya ci bashi don yin wannan kyautar. Haka kuma ba daidai ba ne mai kudi ya kame hannu ya ki bayar da kyautar ko ya bayar da ‘yar kadan.
Wadannan ayyukan kyautatawa da dadadawa da Allah Madaukakin Sarki Ya umarci maza su aikatar lokacin saki su kan rage kuncin zuciya, rudani fa halin ka-ka-ni-ka-yi ga matar da aka saki, saboda saki yana da zafi da kuna a zuciyar ‘ya mace matukar ba ita ce ta neme shi ba koda kuwa ita take yin abubuwan da suka sa ta cancanci a sake ta. Don haka irin sakin da mazajen wannan zamani suke hade da wulakanci da cin fuska da muzgunawa kwata-kwata ya fita dags tsarin da Allah Madaukakin Sarki Ya aza.
Ladabi na 14: Yafe Sadaki: Ga matar da aka saka kafin kadaituwar ibadar aure da ita wacce an riga an ba ta sadakinta a hannunta, to sai a amshi rabi a bar mata rabi ko kuma a yafe mata duka, kuma Allah. Madaukakin Sarki Ya nuna yafewar ta fi kusa ga takawa; wannan bayani ya zo a cikin a Aya ta 236-237, cikin Suratul Bakarah. Sannnan bayan nan kuma sai a kara mata da kyautar dadadawa wacce take wajibi akan dukkan wani Musulmin da Ya saki matarsa.
Ladabi na 15: Kar a kwace mata kaya: Ba daidai ba ne magidanci ya kwace dukkanin kayan da ya riga ya kyautar da su ga matarsa lokacin sakin aure, yin haka zalunci ne. Kyautatawa shi ne ya bar mata dukkan abinda ya mallaka mata komin karanci ko girman darajarsu; kama daga sutura zuwa kayan gida, da sauransu. Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawasa a kodayaushe, amin.