Don me muke yin rubutu (1)
kwakwalwa ita ce kandamin da ke ajiye da duk wani tunani na dan Adam. Daga cikinta ne ake tsara da shirya da kuma luguden dukkan abin da ake so ya kasance na rayuwar yau da kullum. Idan har an kammala dafuwar ne sai harshe ya shigo domin idar da sako. Kamar yadda aka sani, harshe […]
kwakwalwa ita ce kandamin da ke ajiye da duk wani tunani na dan Adam. Daga cikinta ne ake tsara da shirya da kuma luguden dukkan abin da ake so ya kasance na rayuwar yau da kullum. Idan har an kammala dafuwar ne sai harshe ya shigo domin idar da sako. Kamar yadda aka sani, harshe shi ne injin din da ke sarrafar da kuma aiwatar da duk tunani da kwalya ta shirya ko ta tsara a cikin kowace irin al’umma. Da harshe ne ake fiddo yawancin al’adu da adabi da ma duk wani ilmi na rayuwar dan Adam, ta fuskar bayyanawa ta baki ko kuma a rubuce. Wannan dama ce ta sa ake ba harshe muhammanci, ta yadda wadanda ba su da shi sukan kasance nakasassu, wadanda kuma suke amfani da wani abu makamancin sa, ake musu kallon wadanda suka kasance tara, ba su kai goma ba. A nan ina magana ne kan bebaye ko kuma masu kama da su da kuma masu amfani da hito a matsayin hanyar sadarwa a tsakanin mutane, misali al’ummar Mazatec da ke kasar Medico, haka wannan yanayi yake ko a cikin rubutaccen harshe.
Duk wadanda ke da hanyar rubuta harshensu, ana yi musu kallon wadanda suka ci gaba, suka fi sauran al’ummomi na duniya wayewar kai da sanin abin da duniya take ciki. Wannan shi ne fasali na farko da aka fara amfani da shi wajen gane bambancin da ke tsakanin Turawa da bakaken fatar Afirka, dab da za a yi mana mulkin mallaka. Rubutu, ko kuma in ce harshe a takarda shi ne ya sanya wa Turawa ji da kai da kuma tokabo, har suke ganin cewa ba wata hujja da bakaken fatar Afirka za su kyamace su dangane da zuwan su nahiyar a madadin ‘yan jari hujjar wancan lokaci.
Ba sai an fada ba, harshe a magance da kuma rubuce ya kara sanya wani wagegen gibi tsakanin Turawa da mutanen Afirka, domin kuwa ko da suka yi amfani da alburusai da bindigogi wajen cin wannan nahiya ta Afirka da yaki, daga cikin rubutaccen harshe aka samo wannan tunanin. Saboda haka ko da masana irin su Jahn a 1963 ke bayanin cewa, ai ko da Turawa suka zo Afirka sun iske mu da wayewar kanmu da tunaninmu da kuma ci gaban zamani irin namu, shi kuma Rodney a shekarar 1973 ya kara jaddawa ta hanyar cewa ai zuwan Turawan ma ya dakushe ne a maimakon ya taimaka wajen ciyar da nahiyar Afirka gaba, kuma ko kafin zuwan Turawa akwai wasu al’ummomi da suke da harshensu a rubuce, akwai kuma wadanda ke da hanyar sadarwa ta gargajiya; irin ‘yan ma’abba da kuma kida da ganguna ko makamantan haka wajen sadarwa; wannan bai nuna mana irin yadda tunanin jama’ar nahiyar Afirka ya kasance a zahiri ba. Domin kuwa mulkin mallaka abin da ya mayar da hankali shi ne sanya mutumin Afirka ya dinga tunani da rubutu a cikin harshen da ba nasa ba, a cikin harshen da zai sanya Bature ya dinga ci gaba da mulkin Afirkawa ko da kuwa bayan ya nade tabarmarsa ya bar nahiyar a tsawon shekaru.
Wannan shi ne a halin yanzu ke faruwa a yawancin kasashen da ake yi wa lakabi da masu tasowa ko kuma wadanda ba su ci gaba ba, ba wai a nahiyar Afirka kadai ba, har da sassan duniya da makircin mulkin danniya da mallaka ya shiga cikinsu ya yi kaka-gida. Shi ya sa yau kasar Ingila da masu magana da rubutu da harshen Ingilishi a matsayin harshen uwa ba su wuce ka kwana ka kirge su ba, amma kuma masu magana da Ingilishi a duniya sun fi kowa yawa a doron kasa, shi ya sa ma ake wa harshen lakabi da harshen duniya, ko kuma harshen danniya!
An fadi haka ne saboda sanin irin yadda tunani da Ingilishi da rubutu da Ingilishi yake nakasa kowace al’umma da ta ba wannan abu muhimmanci fiye da harshen uwa ko harshen gida. Ba yadda za a yi al’umma ta ginu ta kuma ci gaba ba tare da kare harshenta da kuma rubuce-rubucenta ba; duk irin yadda mutum zai yi ya ciyar da kasarsa gaba ta hanyar amfani da ilmi da ke cikin littafin da ba a harshensa yake ba, zai kasance cikin matsala da kuma kunci, domin zai zamanto mai yaki da tunani iri biyu, na baki da kuma nasa na gida, wannan na daga cikin abubuwan da suka cunkushe harkar ilminmu da kuma halin da ilmin yake ciki da kuma rubuce-rubucenmu a yau.
Wannan abu da muke fama da shi yau, shi ne kuma Turawa suka yi fama da shi tsakaninsu da Larabci, a lokacin da Larabcin yake cikin ganiyarsa. Kusan duk wani ilmi na kimiyya ko fasaha ko kuma na ci gaban al’umma a Larabce yake kafin Turawa su gaje, su kuma mallake shi daga baya. A lura, ba don Turawa na so ba ne suka debi ilmin Larabcin suka yi amfani da shi, dole, kanwar na ki ce ta sa Turawa suka yi amfani da tunani da nakaltar Larabci don cin moriyar ilmin da ke kimshe a cikin littattafan Larabawa da ke mulkin duniya a wancan lokaci. Daga baya ne Turawa suka fahimci cewa ai yawancin ilmin da Larabawa ke takama da shi su ma sun kwaso wasu ne daga littattafan Girkawa, don haka suka yi watsi da na Larabawa suka koma wa na ainihin, wato Girkanci, ta haka ne mallakar da Larabawa suka yi wa duniya ta fuskar ilmi ta subuce ta koma ga Turawa, musamman na Ingila. Wannan ba wani abu ya nuna mana ba sai cewa gadon gida halal ne ga raggo. Ba ta yadda za a kai ga kololuwar ilmi da ci gaba ta amfani da bakon harshe, domin kuwa komai iya nakaltar harshen wasu da aka yi, ba za a taba zama kamar su ba, kuma za a kasance ne a kullum ana magana da bakin ne, ba mutanen cikin gida ba ko kuma ‘yan uwanka, domin kuwa kashi 7 cikin 10 na mutanenmu ba su san da wannan bakon harshen ba, idan kuwa haka ne, to mu da wa muke magana a rubuce-rubucenmu idan mun kimshe al’amarunn cikin harshen Ingilishi ko kuma mun jona tunanin bakuwar al’ada da adabi da addini a cikin rubuce-rubucenmu?
Za Mu Ci Gaba