Don me muke yin rubutu? (2)

Tambayar farko da zan soma da ita, ita ce, shin marubutan baya, wato kafin mu, haka suka yi? Yaya tasirin amfani da baqon harshe da al’ada da adabi wajen gina tunani da rayuwarmu zai kasance ga  masu gudanar da wannan harka, musamman ga ci gaban al’ummarmu da kuma qasarmu? A tuna, su kansu Turawan mulkin […]

Don me muke yin rubutu? (2)

Tambayar farko da zan soma da ita, ita ce, shin marubutan baya, wato kafin mu, haka suka yi? Yaya tasirin amfani da baqon harshe da al’ada da adabi wajen gina tunani da rayuwarmu zai kasance ga  masu gudanar da wannan harka, musamman ga ci gaban al’ummarmu da kuma qasarmu?

A tuna, su kansu Turawan mulkin mallaka sun san irin tazarar da Larabci ya yi wa sauran harsunan duniya ne, shi ya sa suka yi amfani da dabashiri kafin su durqusar da shi, su maye gurbinsa da nasu, shi ya sa duk inda suka samu kansu a matsayin masu mulkin mallaka a wancan lokaci, a Afirka ko Asiya ko Amurka ba su yi wasa da cusa tunaninsu da kuma aqidojinsu ga al’ummomin da suka ci karo da su ba. Sun yi haka ne da sani, domin ta haka ne kurum za su iya yin zaman dirshan a cikin harkokin qasashen da suke yi wa sukuwar salla a wancan lokaci. Shi ya sa tsarin ilimin nasu da littattafan da suka shigo da su domin horarwa, suka kasance cikin harshen ’yan mallakar, a wasu wurare suka matsa sai a yi komai tamkar a Turai, a wasu wuraren kuwa a kaikaice, wasu kuma ba ka iya bambanta su da masu mulkarsu ta kowace irin fuska. Dubi Amurkawa ka kwatanta su da mutanen Indiya ko Pakistan da kuma baqaqen fatar Afirka, musamman a tsakanin inda Faransa ta yi turke da kuma inda Birtaniya ta kafa tata lemar. Ma’ana, wannan rarrabuwar ita ce ta taimaka wajen gane illar mulkin mallaka da kuma yadda aka rarraba kawuna domin a ji dadin mulki. Bisa wannan tafarki ne Leopord Senghor na Senegal ke nuna baqin cikinsa game da irin ilimin da ya samu ta hanyar Turawan Faransa, yana cewa, ‘a lokacin da nake fafutikar karatu a gida da waje, ’yan uwana da na bari a gida ba su yi boko ba, sun kasance ’yan qasa nagari, ni kuwa a kullum da na bar makarantar firamare na shiga sakandare, na wuce zuwa jami’a, sai qara hannun riga na riqa yi da al’ummata da kuma qasata.’ Ya ci gaba cewa ‘a daidai lokacin da nake karatu, sai na qara sanin tarihi da yanayin qasashen Turai, ina kuma qara jahilcewa game da tarihin al’ummata da kuma qasata.’ Daga qarshe ya ce,  ‘a lokacin da na dawo gida daga Faransa, sai na ga na kasance baqo cikin jama’ata. Tsararrakina da na bari ba su yi karatu ba, suka kasance malamaina game da qasata.’

Wannan haka ya kasance dangane da yawancin marubuta da shugabanni a Nahiyar Afirka, musamman wadanda suka kasance qarqashin mulkin qasar Faransa. A bangare daya kuwa, wadanda suka zauna cikin inuwar mulkin Birtaniya ba haka abin ya kasance ba, ga wasu, kamar yadda Mista East ya bayyana game da Abubakar Imam a matsayinsa na marubuci, ya ce, ‘Abubakar (Imam) yana daya daga cikin ’yan qalilan da ya kasance duk da cewa ya samu iliminsa ta hanyar horarwa cikin Ingilshi da littattafan Ingilishi, daga kuma Turawan Ingilishi, bai yi watsi da harshensa ba, domin kuwa yana bayyanar da tunaninsa cikin harshen nasa, ba a cikin Ingilishi ba kamar yadda saura ke yi.’

Tambaya. Me ya bambanta Senghor da Imam? Ba wani abu da ya wuce cewa shi Imam bai yarda Ingilishi ya kasance masa harshen tunani ba, bai yarda baqin al’adu sun yi masa katutu ba, ba ma Ingilishi kadai ba, kusan duk wani baqon abu da ya ci karo da shi a lokacin da yake nadar ilimi da ya gina masa rayuwa bai cika amsarsa kai-tsaye, sai ya yi bita da naqaltar irin tasirin da zai yi masa. Shi kuwa Senghor ya tashi ne cikin wani tsari da ya fifita tunani da al’adun Faranshi bisa na baqar fata, haka al’adu da addini da kuma tsarin ilimin baki daya. Bai samu damar bambance barcin makaho ba ko kuma duma daga kabewa ba, ba don komai ba kuwa saboda irin yadda aka rene su tun daga gida.

Imam ya samu ilimin addini mai zurfi ko kafin ya hadu da Bature da makircin da ya shigo da shi, saboda haka bai yarda wani makiri ya yi masa wayon waniqiqi ba, tun yana qarami. Ko da ya shiga dakin ajiyar littatafai na makarantar elemantare da midil a Katsina domin ya yi nazari domin shiga gasar rubuta littatafai da aka shirya a 1929 da kuma 1933, bai yarda ya yi amfani da duk abin da ya ci karo da shi ba, sai dai ya karanta, ya jinjina kamar mai sayen kaza, amma yana buqatar mai qwai. Haka kuma sai ya auna abin da abin da addininsa da kuma tadojinsa na qwarai suka aminta da su, sa’annan ya kattaba shi a cikin nasa aikin. Saboda haka muna iya cewa bai taba yarda da tasirin baqin al’adu ko addinai da ya yi nutso a cikinsu, sun ja masa akala wajen yin rubutunsa ba.

Haka su Tafawa balewa da Ahmadu Bello da Aminu Kano da Sa’adu Zungur da Mu’azu Hadeja da Mudi Sipikin da Alqali Bello Gidadawa da Gambo Hawaja da Shekara Sa’ad da wadansu da dama daga cikin marubutanmu na da suka yi, kuma wannan shi ya haifar da aqidar nan ta goya wa talaka baya da nema masa mafita daga al’amurran da suka kasance suna sa masa qunci da dabaibaye shi ta fuskar siyasa da mulki da tattalin arziki da sauran al’amurran zamantakewa na yau da kullum.

Bari mu yi bitar wasu daga cikin ayyukan daya daga cikin mashahuran marubutan qasar Hausa wato Abubakar Imam, domin mu gani ko za mu iya samun haske dangane da irin abubuwan da aka yi a da, da yadda suka yi tasiri har zuwa yau, kafin mu koma ga ainihin batun namu na yau, shin mu wa muke yi wa rubutu, don me muke yin rubutu, me kuma muke so rubutunmu ya yi a rayuwar da muke ciki?!

Za mu ci gaba