Don me muke yin rubutu? (3)

A cikin ayyukan da Abubakar ya yi na adabi ba daya da ya zauna ya shirya a cikin ransa da nufin ya nishadantar kurum ko kuma ya burge kawai ko kuma dai don a san da shi a cikin harkar rubutu ko kuma rayar da ilimi. Bai yi haka a lokacin rubuta littafin Ruwan Bagaja […]

Don me muke yin rubutu? (3)

A cikin ayyukan da Abubakar ya yi na adabi ba daya da ya zauna ya shirya a cikin ransa da nufin ya nishadantar kurum ko kuma ya burge kawai ko kuma dai don a san da shi a cikin harkar rubutu ko kuma rayar da ilimi. Bai yi haka a lokacin rubuta littafin Ruwan Bagaja ba, duk da cewa a lokacin da ya yi rubutun yana da shekara 22 a doron kasa. Ko da ya shiga dakin ajiyar littattafai na makarantarsu domin ya samu samfur na irin yadda zai tsara labarin nasa, ya kuma ci karo da littafin The Water Of Cure na ’yan uwan Grimms daga Jamus, ba haka nan ya bi shi ya kwashe komai da komai ba da ya ci karo da shi a cikin littafin, kamar yadda labaran suke a kasar Jamus, tun asalinsa ba, sai da ya bi ya nakalci labaran, ya yi musu kwaskwarima ya debe al’adun Jamusawu da suka yi hannun riga da na kasar Hausa, sa’annan ya maye gurbin wadanda ya karanto da na Hausawa. Saboda haka za a ga ya cire addinin Kiristanci, ya shigo da Musulunci, al’adun Jamusawa suka ba da wuri domin na Hausawa su samu wurin zama.

Da kuma ya shiga cikin littafin Alfu Lailah ya yi nutso da ninkaya ya debo hikayar Abdussamad da ’yan uwansa, ita kuma ya kwashi wani gefe ne da ya dace da tunanin malam Bahaushe ya jefa a cikin littafin Ruwan Bagaja, ya yi watsi da tadar Larabawa da ya san cewa ba ta da wani alfanu ga mai karanta Hausa. Ba nan kadai ya tsaya ba, ya kuma shiga cikin gonar adabin baka na Hausa inda ya tsamo tatsuniyoyi da labaran Hausawa da suka yi tashe a wancan lokaci ya gina zubin littafin. Da kuma ya natsu sai ya nemo rayuwar Malam Zurke da Alhaji Imam daga rayuwa ta yau da kullum. Shi dai Zurke wani mahaukaci ne da aka yi a cikin birnin Katsina a lokacin da Imam ke karatu a can, Alhaji Imam kuwa ba kowa ba ne marubucin ne da kansa. Sunansa Imam, mahaifinsa sunansa Shehu, shi ya sa ‘Himma dan Shehu’ ya zama lakabinsa. Sai dai ya dace a lura ko da ya je ga rayuwar yau da kullum domin neman gina Malam Zurke da Alhaji Imam, amma kuma siffofin wadannan mutane a zahiri ya same su ne daga littafin Makamatul Hariri, inda Harisu da Abu Zaid suka taka rawa irin ta Zurke da Alhaji Imam, sai dai su Harisu dabaru da wayon wanikiki da suka yi a cikin Makama cike suke da al’adun Larabawa, dole ta sa Imam ya mayar da su na Hausawa, cikin ban dariya da sosa rai.

Idan kuma muka dubi Magana Jan Ce (1-3) sai mu ga cewa nan Imam ya nuna gwanancewa fiye da a Ruwan Bagaja. Ko ba komai a nan ya san da wa yake magana, ya kuma san dalilin yin rubutun da abin da yake son rubutun nasa ya yi ga wadanda aka yi wa rubutun. Tun da farko, nan ba gasa ba ce, an nemi a yi rubutu ne don yara ’yan firamare, domin a samar musu abin karatu da kuma tarbiyya. Nan ma Imam sai da ya nemi samfur da zai gina nasa tunanin, amma kamar kullum sai da ya canja wa duk wani tubali da ya tsinto daga wasu wurare siffa ko kuma kama, don su dace da tada ko al’adun yara ’yan kasar Hausa. Ya dai dubi tsarin Alfu Lailah, ya gina budewar Magana Jari Ce, ya kuma yi amfani da littafin The Parrot ya gina batun Aku mai magana, ya nemo labaran Andersen Fairy Tales na kasar Denmark da labaran Aesop Fables na Girkawa da labaran Grimms Fairy Tales na Jamusawa da labaran Shakespeare na Ingila da tatsuniyoyin Hausa masu tarin yawa domin su kasance masa ’ya’yan da ke tafiya da uwar labarin Magana Jari Ce. Ya yi haka ne cikin tunanin masu karatunsa da neman shirya musu mafita da samar da tasiri nagari. Saboda haka duk inda ya hadu da maganar barayi sai ya yi huduba kan sata da rashin kyan sata, yana kuma bayyana cewa bai son bayar da labarin barayi ba don komai ba sai don gudun kada yara su samu abin kwaikwaya. Shi ya sa kuma duk inda ya kawo labarin barayi to bai barin barayi su yi nasara kan mutanen kwarai. Kai ba wannan kadai ba, duk inda aka yi mugun abu sai ya nuna horon da aka yi wa wanda ko wadanda suka yi mugun abin domin ya kasance darasi.

Imam ya san darajar rubutu, ya kuma san illar rubutu, shi ya sa tun farkon shiga cikin wannan harka kamar yadda ya fada a cikin tarihinsa, ya shiga da zuciya daya. Ga abin da yake cewa a cikin littafin tarihinsa na rayuwa game da matsayin rubutu. Ya ce, East ya koya masa cewa ‘kada ka yarda ka bar mugu ya yi nasara a cikin gina labarinka, domin tasirin barin haka zai iya rusa al’umma.’ Wannan shi ne ke cikin zuciyar yawancin ayyukan adabin da Imam ya gina a cikin Magana Jari Ce.

Misali, duk inda ya ji ana maganar itaciyar Yeuw (mai kwankwamai) sai ya mayar da ita itaciyar tsamiya. Gidan Turawa na ginin bene, ba zaure don baki da sa kwat da duk wasu abubuwan jin dadi na rayuwa, irin na Turawa, canja su ya yi da na Hausawa, bai yarda bakon malam Bahaushe ya shigo har cikin gida ba, domin masaukin bako ai zaure ne in ji Hausawa. Haka abinci da abin sha da abin hawa da sauran makamantan su, ba don komai ba sai don wadanda yake wa rubutun su karu da ilimin da ke ciki da kuma inganta kyawawan al’adu.

kila wani ya ce a wancan zamani da su Imam suke raye ne ai ake yin hakan, yanzu fa, yaya al’adun Hausawa suke, yaya za a iya bambanta na ainihi da wanda yake bako?