Don me muke yin rubutu? (4)
Abin nuni shi ne zamani ai riga ne, in Imam ya hana bako wucewa cikin gida sai dai zaure, za mu ga cewa ya yi hakan ne don ya yi daidai da zamaninsa, kila mu yanzu, bakon har cikin dakunan masu gida yake shiga. Ke nan za mu iya ganin haka a namu rubutun, amma […]
Abin nuni shi ne zamani ai riga ne, in Imam ya hana bako wucewa cikin gida sai dai zaure, za mu ga cewa ya yi hakan ne don ya yi daidai da zamaninsa, kila mu yanzu, bakon har cikin dakunan masu gida yake shiga. Ke nan za mu iya ganin haka a namu rubutun, amma shi ma sai a bayyana dalilin yin haka da yadda zamani ya zo da shi, ba wai a turbude shi tamkar shi ne mafita ga al’umma ba.
Shi ya sa a yawancin rubuce-rubucen marubutan kwarai za a ga ba su yarda mugu ya sha daga muguntarsa ba, ba su barin azzalumai su wuce da zaluncinsu, ba su barin kunci ya tabbata a cikin rayuwa. Duk yadda za su yi za su nuna wa masu karatu, kyau da rashin kyawun abu, irin wannan shi ya bi ya gina tunanin marubutan kwarai da adabi mai walwala. Wannan kuma shi ya sa, har yau har kwanan gobe ayyuka irin wadannan da marubutan suka rubuta da kewar mutanensu da tunanin mutanensu da neman inganta rayuwar mutanensu suke kasancewa kamar yau ne aka yi su duk da cewa sun yi shekara dari da dabbakawa. Darussan da ke cikin irin wadannan ayyukan adabi har yau suna da tasiri a rayuwar jama’ar yau din, ba wa sai na jiyan ba, za su kuma ci gaba da wanzuwa a haka har gobe da yardar Allah.
Tambayar da kila wadansu ke faman yi zuwa yanzu ina jin ba ta wuce to mu wa muke wa rubutu ba, don me mu muke yin rubutu? Muna yin rubutun ne don mu samu na cefane, wato mu samu abin da za mu ciyar da kanmu da iyalanmu? Ko kuwa muna yin rubutun ne don gwamnati ta san da mu ta ba mu kwangila ko lambar yabo? Ko kuwa muna yin rubutun ne don talakawa masu karantawa su samu abin nishadi ko kuwa don dai kawai rubutu maganin wani ciwo ne, idan ba mu yi shi ba, ba za mu samu saukin radadin ciwon ba? Kafin in bayar da wannan amsa, zan so in dan mazaya tukun, domin ta haka ne nake jin za mu samu haske game da irin rubutunmu da wadanda muke wa rubutun da dalilan yin rubutun.
Rubutu baiwa ce, Allah ke sa iliminSa inda Ya so ga wanda Ya so, yadda Ya so a lokacin da Ya so. Wadansu kuma haye suke yi wa rubutu, su kuma kasance ’yan gida a cikinsa, ta yadda duk abin da dan gado zai iya yi, su ma za su iya, kila ma har su fi ’yan gida. Saboda haka kowace irin dama mutum ya samu ya zama marubuci, abin da ke da muhimmanci shi ne ya san tasirin irin rubutun da yake yi da kuma inganci ko akasin haka.
Masana rubutu na yin kirari da cewa alkalami ko biro ko ma dai wane irin abin rubutu ne da ya fi takobi kaifi a fagen juyin-juya-hali ko canjin lamurran rayuwa. Ke nan alkalami ko wani abin rubutu babban makami ne na sauya lamurran rayuwa, idan an yi amfani da shi yadda ya dace. Ke nan abin da ya dace mutum ya fara da shi a fagen rubutu shi ne sanin wadanda yake wa rubutu.
Kai da ke karanta wannan bayani a yau, tambayi kanka wa kake yi wa rubutu? Hausawa ko Turawa ko Larabawa ko wasu baki? Idan Hausawa kuke magana da su a rubutunku, to ya dace rubutun nan naku a cikin jarida ne ko mujalla kuke yin sa ko kuma labari ne ko waka ko kuma wasan kwaikwayo kuka gwanance kai, to ya kasance a cikin harshen da mutanenku za su gane, za su fahimta, za su kuma iya yin aiki da shi yake.
Saboda haka ku da ke nan tare da mu wa kuke wa rubutu? Mutumin Garun-Ali ko kuma Yorkshire ko Manchester ko Makka ko Madina ko Lahore ko ina? Ku da ke ta fafutikar rubuta waka ko rera ta. Ku da ke tsarawa da kuma rubuta da aiwatar da wasan kwaikwayo. Ku da ke ta faman zayyana labarai cikin fasaha iri-iri. Ku da ke ta faman rubutu cikin jarida ko mujalla ko Intanet da sauran kafafe. Ku da ke faman sai kun wallafa littafi a kowace rana ta Allah, don me kuke wannan hankoro? Domin kadafari ko kuwa don a san ku a matsayin marubuta? Me ya sa kuke rubutu? Wa kuke wa rubutun? Wace ribar kuke nema daga rubutu?
Mun kammala