Don namen mulki ’yan siyasa ke sukan Tinubu —Gwamnan Kaduna
Uba Sani ya ce, ’yan siyasar da ke kwarzanta Tinubu ne suka koma bakin ganga bayan sun sauka daga mulki
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya soki ’yan siyasar da ke sukar gwamnatin Shugaban Bola Tinubu da cewa suna yi ne kawai domin neman mulki.
Uba Sani ya bayyana cewa ’yan siyasar da ke yawan sukan Tinubu a baya-bayan nan ba su da wani abin da za magance matsalolin Najeriyar da suke suka shugaban kasan a kai.
Ya kara da cewa masu sukan Tinubun su ne suke ta yabon shugaban kasar, amma yanzu da mulki ya bar hannunsu suka dawo suna zagin sa.
A cewarsa, babu mutum daya a cikin taron masu kushe Tinubun da ke da nagartar da ta fi shugaban kasar, yana mai jaddada cewa Tinubu ya yi yaki kai da fata kuma har yanzu yana kare muradun tsarin dimokuradiyya.
- Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani
- Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba
Idan ba a manta ba a makon jiya ne a yayin wani taro da suka gudanar a Abuja, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, da tsohon Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi da sauransu suka salon mulkin Tinubu da jam’iyyar APC.
Amma a yayi wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin na TVC a ranar Litinin, Gwamna Uba Sani ya bayyana zargin nasu matsayin mara tushe.
Ya ce, “yawancin wadannan ’yan siyasan kamar a kan kansu suke magana. Ai da a jam’iyya daya muke da su, don haka ina makamin abin da suke yi.”
Ya bayyana maganganun nasu da soki-burutsu da “neman wautar da hankalin ’yan Najeriya,” amma ai yawancinsu masu rike mukaman gwamnati ne kimanin shekaru biyu da suka gabata, mai suka yi a lokacin?”
Don haka ya zarge su da sukan Tinubu domin samun karbuwa a wurin ’yan Najeriya a yunkurinsu na samun madafun iko.
Amma ya ce, “’Yan Najeriya na da hankuale, sun san cewa ’yan siyasar na yakar Tinubu ne kawai saboda babu abin da suka fi shi da shi. Sun samu dama a bayan, amma me suka yi da ita?”