Don samar wa matasa sauyi muka kafa kungiyarmu -Kwamred Babanyara
Aminiya ta zanta shugaban kungiyar YLAN, reshen Jihar Kaduna, Kwamrade Injiniya A Y. Babanyara bayan ya samu lambar yabo na matashin da ya fi gwagwarmaya a Kaduna, inda ya bayyana dalilin bude kungiyar YLAN, da nasarorin da suke samu da kuma matsaloli. Ga yadda hirar ta kasance: Ka gabatar mana da kanka? Sunana Abubakar […]
Aminiya ta zanta shugaban kungiyar YLAN, reshen Jihar Kaduna, Kwamrade Injiniya A Y. Babanyara bayan ya samu lambar yabo na matashin da ya fi gwagwarmaya a Kaduna, inda ya bayyana dalilin bude kungiyar YLAN, da nasarorin da suke samu da kuma matsaloli. Ga yadda hirar ta kasance:
Ka gabatar mana da kanka?
Sunana Abubakar Yakubu Babanyara, an haifeni a Birnin Zazzau. Na yi Firamare da Sakandire duka a Zaria. Bayan nan sai na tafi Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Bauchi wato Abubakar Tafawa Balewa Unibersity, Bauchi inda na karata tsare gibe-gine wato Cibil Engineering. A yanzu haka ni Iinjiniya ne mai zaman kansa, kuma memba a kungiyar injiniyoyi ta kasa wato Nigeria Society of Engineers(NSE), kuma memba a kungiyar masu tsara gine-gine na Amurka wato American Society of Cibil Engineers(ASCE). Kuma ni memba ne gungiyoyin da yawa. A yanzu haka ni ne shugaban kungiyar Young Leadership Association of Nigeria (YLAN) reshen Jihar Kaduna.
Mene ne tarihin kungiyar YLAN?
kungiya YLAN ta samu rajista da Hukumar kula da kungiyoyi (CAC) a ranar 3 ga watan Augusta, 2017. Kuma ita wannan kungiya tana da rassa a duk fadin jihohin Najeriya da Abuja. Kuma tana da mahukunta guda shida, masu wakiltan shiyoyon da muke da su guda shida a Najeriya. Kuma muna da shuwagabanni kungiyar na kasa baki daya.
Mene ne manufofin kafa kungiyar?
Wato ita wannan kungiya an kafata ne domin samo wa matasan Najeriy sauyi. Domin lokaci ya yi da za a saka a cikin tsarin shuwagabancin al’umma, domin mu ne muke da fiye da kashi 65% na mutanen Najeriya, amma ba a bamu dama mu yi fafutikar neman zabe, sai dai ayi amfani da mu. YLAN an kafata ne domin ta haska wa matasa cewa to lokaci ya yi da za su fito ayi gwargwarmayar neman zabe da su a kowane mataki a Najeriya. Kuma ta horar da matasa a kan yadda ya kamata ayi shugabanci, ta hanyar jawo kwarrarru su horar da su. Da kuma horar da matasa da su yi dogaro da kansu, ta hanyar samo musu sana’o’i da za su dogara da kansu.
Ina kuke samun kudaden da kuke gudanar da kungiyar?
Yadda muke samun kudaden da muke tafiyar da ayyukan kungiya, shi ne mun sa wa kanmu haraji duk mako, wanda kowane memba yake bayarwa. Sai kuma sauran kungiyoyin masu zaman kansu wato NGO’s na gida da na wajen Najeriya, wadanda suke taimakawa irin kungiyoyin masu manufa irin tamu. Amma har yanzu ba mu samu wata ba, sai dai muna kokarin kulla alaka da su. Kuma da yardaa Allah muna tunani za su gowa ya mana baya domin ci gaba da aikin da muke yi.
Wane nasarori kuka samu?
Alhamdulillah. Bisa yardar ubangiji mun sami nasarori. Mun ki ziyara gidajen marayu, asibitoci da kuma gidan fursuna. Membobinmu sun samu ziyartar gidajen marayu da ke cikin garin Kaduna da na Zaria, gidan marayu na Jam’iyyar Matan Arewa da kuma Faith Work a garin Kaduna da kuma gidan marayu da ke Zariya. Kuma mun kara musu kwarin gwiwa cewa babu maraya sai rago. Kuma mun samu daman kai musu kaya, sabulai na wanka da wanki, manshafawa, da dai sauran su. Hakanan kuma mun samu ziyarta asibitin dabke garin Kafanchan, domin mu kara musu karfin gwiwar cewa ciwo ba mutuwa ba ne. Kuma mun kai musu kayan agaji irin su magun guna, da makantansu. Ziyara ta karshe shi ne gidan fursuna da ke Zaria. Suma mun kara musu kwarin gwiwa cewa zamanka a gidan yari ba shi ne karshen rayuwa ba, kuma koda yaushe ya kamata mu zamo mutane nagari domin al’umma su yi Alfahari da ku, kamar irin Shugaban kasa na yanzu Mohammadu Buhari, Olusegun Obasanjo sun shiga gidan kafin suka zama shugabannin kasa. Nigeria, da irin su Manjo Hamza Almustapha. A yanzu haka muna shirye-shiryen kwarya-kwaryar taro domin kara wa juna sani akan zaman lafiya wanda zai gudana nan ba da dadewa in Allah Ya yarda.
Mece ce matsalar da kuke fuskanta?
Matsalolin da muke fuskanta, wanda ya fi damun kungiya wajan tafiyar kungiyar yadda ya kamata akwai yadda ‘yan uwa matasa suke tunanin a kan kowace irin kungiya, da ance ga kungiya, tunanin farko shi ne ta yaya zan samu kudi da kungiyar ba yadda za a tafiyar da ita yadda ya kamata ba. In aka ga gungiyar ba ta siyasa bace, ba a samun kudi sai ka ga membobinta basa mayar da hankali a kan tafiyar da ita yadda ya kamata.
Mene ne kiranka ga gwamnatin?
Kirana ga gwamnati shi ne ta rika ba matasa dama domin a tattauna da su, ta san matsalolinsu domin ayi maganin abun. Don matsalar matashi gaskiya sai matashi. Toh za ka gwamnati ba ta bai wa matasa gurbin da ya kamata a basu, sai kaga mai wakiltar matasan ba matashin ba ne, ka ga ba za a gane mece ce matsalar ba har sai gwamnati ta gyara.
Mene ne kiranka ga matasa?
Kirana ga ‘yan uwa matasa shi ne a koda yaushe su kasance cikin mutane nagari domin lallacewar matasa bai da alfanu ga al’umma. Kuma mu ne gimshikin bayan kowace al’umma, idan muka lallace, al’umma ce ta lallace.