Don taimakon kanmu muka kafa kungiya – Alhaji Auwalu
Shugaban kungiyar Kainuwa Dashen Allah ta ’Yan Gwangwan da ke hada-hada a kasuwar duniya a yankin Biktoriya Ailan da ke Jihar Legas, Alhaji Auwalu Sulaiman ya ce, sun kafa kungiyar ne don su taimakon kansu. Alhaji Auwalu Sulaiman wanda shi ne shugaban kasuwar duniya da ke unguwar Biktoriya Ailan ya yi furucin ne yayin da […]
Shugaban kungiyar Kainuwa Dashen Allah ta ’Yan Gwangwan da ke hada-hada a kasuwar duniya a yankin Biktoriya Ailan da ke Jihar Legas, Alhaji Auwalu Sulaiman ya ce, sun kafa kungiyar ne don su taimakon kansu.
Alhaji Auwalu Sulaiman wanda shi ne shugaban kasuwar duniya da ke unguwar Biktoriya Ailan ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
“Mun kafa kungiyarmu ne don mu taimaki kanmu da kanmu da iyalanmu da ma wanda yake kusa da mu. Saboda haka ina mai tabbatar maka da cewa mun kafa kungiyarmu bisa tsarin doka da oda. Kuma membobinmu ’yan kasa ne na gari masu bin doka da oda. A lokacin da muka zo Legas sai muka yi tunanin cewa bai kamata mu zauna haka kara-zube ba, sai muka kafa kungiya muka sanya mata suna Kainuwa Dashen Allah. Dalilin sanya mata wannan suna shi ne mun yi imanin cewa idan ka dogara ga Allah to babu shakka zai taimake ka,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Tun daga lokacin da muka kafa wannan kungiyar mun samu nasarori da yawa saboda dogara da muka yi da Allah. Mun gudanar da ayyuka masu yawa wadanda suka hada da taimakon junanmu da bada gudunmawa na taimakon masallacin.”
Ya bayyana cewa kungiyar ta dauki matakan da suka dace kan membobinta da suke shan miyagun kwayoyi.
“Akwai horo na musamman da muke yi wa duk wani membinmu da muka same shi da laifin da shaye-shaye. Wani lokaci mukan yi duk wanda muka samu bulala 10 zuwa 15 idan kuma ya gagare mu sai mu mika shi wurin jami’an tsaro don daukar matakin da suka dace,” inji shi.
Don haka sai ya ce kungiyar ta samu membobinsu da suka kamu da tabin hankali sakamakon shaye-shaye.
“Babu shakka akwai ’yan kungiyarmu takwas zuwa goma da muka samu sun kamu da tabin hankali sakamakon shaye-shaye. Wasu mun kai su asibiti wasu kuwa tuni sun warke sun daina a halin yanzu sun ci gaba da gudanar da harkokinsu,” inji shi.
Sai dai ya dage a kan cewa sun dauki matakan da suka dace don kare kansu daga kamuwa da cututtuka sakamakon mu’amala da karafuna.