Don Uwargida: Hikimomin Zama da miji

Hikima ta 1: Fahimtar Tasirin dabi’a: Kyawun jiki da fuska, iya girki, kwalliya, tsabta da kwarewa wajen ibadar aure na daga cikin manyan abubuwan da ake yawaita nanatawa da mace in ta rikesu za ta mallake mijinta, ta juya shi yadda ta so. Amma wadannan tubali ne da babu ginshiki, don haka ko bajima ko […]

Don Uwargida: Hikimomin Zama da miji

Hikima ta 1: Fahimtar Tasirin dabi’a:

Kyawun jiki da fuska, iya girki, kwalliya, tsabta da kwarewa wajen ibadar aure na daga cikin manyan abubuwan da ake yawaita nanatawa da mace in ta rikesu za ta mallake mijinta, ta juya shi yadda ta so. Amma wadannan tubali ne da babu ginshiki, don haka ko bajima ko ba dade za su fadar da ginin da suke rike da shi. Ginshikin ginin aminci mai dorewa da zaman lafiya cikin rayuwar aure shi ne kyakykyawar dabi’a; kyaun fuska da jiki, iya kwalliya da iya gyara gida, da sauransu ana cin moriyarsu ne kadai in an garwayasu da kyakykyawar dabi’a. Ma’anar dabi’a shi ne yadda mutum zai gabatar da kanshi wajen hulda da mutane ta fuskoki daban daban na rayuwa. Ga Misalai 2 kan tasirin dabi’a cikin rayuwar aure. 

Misali na 1:

Malam Musa matarsa kyakykyawa ce ga iya kwalliya, ga iya girkin abinci kala-kala na gargajiya da na zamani, gida koda yaushe tsab an gyara, yara kullum cikin tsabta. Amma kuma ba ladabi da biyayya ba girmamawa, da yawan lokutta ta kan ki kawo masa abinci sai dai ya dauko da kansa, a kan abin da bai taka kara ya karya ba ta watza masa harara ko ta yi masa tsaki, kallon banza da gatsine ko sai dai in ranta bai baci ba, in ta bukaci wani abin bai yi mata ba, babu zaman lafiya. Yana iya kokarinsa wajen kulawa ta ko wane bangare, amma ba godiya ko bayyana jinjina kokarinsa, kullum cikin kukan babu take. Da sauran makamantan halaye. Irin wannan auren da wuya ya kai labari.

Malam Isa kuma matarsa ragguwa ce wajen gyaran gida da gyara yara, tsakar gidan kusan koda yaushe a hargitse yake da kayan yara an jefar nan da can, amma da ya shigo gida za ta bar komi take ta tarbe shi, ta gaishe shi tana kasa kasa da murya, ga murmushin alkunya da girmamawa ya kayata fuskarta, ta kawo mashi ruwa mai sanyi da abinci, ta zugunne gefensa yana cin abinci yana mata hira tana amsawa; in ya umarce ta ta yi, in ya hanata komin dacin hanin ta daure ta hanu. Tana girmama shi matuka, komi nasa na musamman ne a gidan, kwanonin abincinsa ba mai ci a ciki sai shi kadai, yara kowa na girmama Baba saboda yadda suka ga mahaifiyarsa na yi. In ta bata masa rai ta ba shi hakuri cikin sassanyar murya. Wannan aure ya samu babban ginshiki mai karfi, guguwar kaddarar da ba ta da magani ne kadai za ta iya tumbuke shi. 

Ba abin mamaki ba ne ya kasance matar Malam Musa ta fi matar Malam Isa son mijinta, ko ta fi ta son adana aurenta, ba burinta ba ne aurenta ya mutu, amma yanayin dabi’a ya sa tana huldatar mijinta da abubuwan da za su kai ta ga faruwar abin da ba ta so. 

Uwargida za ta iya murza sirrin da ke cikin kyakykyawar dabi’a don more rayuwar aurenta ta wadannan hanyoyin:

1. Ta fahimci cewa kyakykyawar dabi’a na da matukar muhimmanci ga nasarar wanzar da zaman lafiya cikin rayuwar aurenta, ta sa wannan a gaba gaba a  farfajiyar tunaninta, kullum ta rika tunowa da hakan, kar ta yi sake rashin ba shi muhimmanci ko mantawa da karfin tasirinsa, wannan zai taimaka mata ta kasance kullum cikin kokarin dabbaka kyakykyawar dabi’un da za su wanzar da aminci da zaman lafiya da rashin gushewar soyayyar maigida.

2. Uwargida ta fahimci cewa kyakykyawar dabi’a kala-kala ce kuma hawa-hawa ce, kowane namiji akwai kalar da yake so da kuma iyakar hawan da yake so game da kowace dabi’a. Don haka kyawawan dabi’un da suka fi muhimmanci ga maigida, wadanda suka fi burge su za ki ba karfi ki dage wajen dabbakar da su kodayaushe cikin rayuwar aurenki. Misali wani namiji bai damu da caba kwalliyarki ba, ko ki yi ko ki bari duk daya a wajensa, shi abin da ya fi so daga matarsa sama da komi shi ne ladabi da saukin hali, wani yawan mita ke bai so sama da iya girki, wani abinci mai dadi yake so sama da girmamawa, wani ki kula da yaransa ki basu tarbiyya mai kyau shi ne abin burgewarsa gareki.

Don haka kar uwargida ta bata lokaci da kuzarinta wajen aiwatar da kyawawan dabi’un da basu da tasiri ga maigidanta, sai ta zabi dabi’un da ta fahimci sun fi muhimmanci ga maigida ta bada lokaci da karfinta garesu. In ma tana shakkarsu, tana iya tambayar maigida kai tsaye, da yawan mazan aure na jin dadin su ga matansu na kokarin faranta masu rai, don haka in maigida ya sanar da ke abubuwan da yake so da wadanda ba ya so, indai basu saba ma Addini, komai wuyarsu ko dacinsu gareki ki daure ki rika yi, ba wanda zai kai cin ribar hakan in kin yi. 

Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.