Don Uwargida: Ladubba Lokacin Saki
Ladabi na 1: Faxar Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Duk lokacin da wani abin ki, wani abin tsoro ko abin cutarwa, komin kankantarsa ya samu mutum, koda tuntube ne ko tauna harshe, ko wani rashi ko jin mummunar magana ko mummunan labari, in mutum ya faxi waxannan kalmomi masu tsananin tsada, to Allah zai saka […]
Ladabi na 1: Faxar Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Duk lokacin da wani abin ki, wani abin tsoro ko abin cutarwa, komin kankantarsa ya samu mutum, koda tuntube ne ko tauna harshe, ko wani rashi ko jin mummunar magana ko mummunan labari, in mutum ya faxi waxannan kalmomi masu tsananin tsada, to Allah zai saka masa wannan abin da albarka mai yawa, Ya jiyar da shi daxin rahama kuma Ya shiryar da shi yadda zai tunkari abin nan ko ya warware matsalarsa, shiriya mai kyau wacce babu kuskure a cikinta; domin wannan alkawari ne na Allah, Maxaukakin Sarki kuma alkawarin Allah tabbas ba ya tashi: “Kuma Lallai ne muna jarrabarku da wani abu na daga tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da ‘ya‘yan itace; Kuma ka yi bushara ga masu hakuri. Waxanda suke idan wata musiba ta same su sai su ce ‘Lallai ne mu ga Allah muke kuma lallai ne mu zuwa gareShi muke komawa.’ Waxannan akwai albarku akansu daga Ubangijinsu da wata rahma kuma waxannan su ne shiryayyu.” (Suratul Bakarah: 155-157).
Ladabi na 2: Yin Sallar neman taimakon Allah: Ya zo a Hadisin Manzon Allah Sallallahu alayi wa sallam cewa duk lokacin da al’amura suka tsananta Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya kan kara kaimi ga yin Sallah. Don haka maimakon fashewa da kuka, zage-zage da yin Allah Ya isa, bayan faxar waxancan kalmomi kyawawa na sama, sai uwargida kuma ta yi alwalla, ta gabatar da Sallar Nafila raka’a biyu, sannan ta xaga hannu ta nemi taimakon Allah daidai da bukatunta da kuma yanayin da take ciki a wannan lokacin.
Ladabi na 3: Danne Fushi: Faxar Inna Lillahi wa inna ilauhi raji’un, yin alwalla da gabatar da Sallah duk za su taimaka wajen tafiyar da fushi da fargaba da tashin hankalin da ka iya samun mace a wannan lokaci.
Ladabi na 4: Ki yi Hakuri, Ki yi Godiya: In sakin da mijinki ya yi maki ya zo miki a matsayin abin bakinciki abin tashin hankali, ki yi hakuri; kyakykyawan hakuri; ki maida dukkan al’amuranki ga Allah, domin Shi ne Ya ce: “Kuma idan sun rabu, Allah zai wadatar da kowannensu daga yalwarSa…”
In kuma sakin ya zo maki a matsayin abin farin ciki abinda kike nema, sai ki yi godiya ga Allah kuma ki yi addu’ar Allah Ya sa hakan ya zama alheri a gareku gaba xaya.
Ladabi na 5: Banda Fariya: Kar Uwargida ta rangaxa guxa ta yi tafi tare da murna da faxar maganganun masu nuna jin daxinta da sakin da akai mata, ko don ta ba mijin haushi ko kuma don da gaske sakin take so; yin haka na iya sawa Allah Ya jarrabce ta da wani aure da ya fi wannan muni shi kuma mijin Allah Ya ba shi wacce ta fi ta. Komi dai a yi bisa kyawawan ladubban musuluncu shi ne daidai kuma shi ne zai haifar da riba mai yawa.
Ladabi na 6: Sanya Shaidu: In har maigida bai sanya shaida ba lokacin da ya yi saki, yana da kyau ita uwargida ta sanya shaida don kar daga baya maigida ya canza baki ya ce shi bai yi saki ba alhali kuma tabbas ya yi a hakika.
Ladabi na 7: Tambayar Kyautar Daxaxawa: Uwargida ta sani cewa kyautar daxaxawa wajibi ne akan maza su bayar, kuma hakkinta ne ta tambaya a ba ta in maigida bai ba ta ba lokacin da ya yi saki.
Ladabi na 8: Kame Baki: Babu alheri cikin yaxa maganar saki da tallata kowa ya ji, ‘yan gulma su sami abin yi makiya kuma su ji daxi; ya fi kyau a daure a yi shiru musamman in sakin ba uku ba ne wanda akwai yiwuwar a mayar da aure kafin gama idda.
Ladabi na 6: Yin Idda a gidan miji: Kwashe kaya kaf da zarar faruwar aure ya fita daga koyarwar addinin Islam. Mace za ta zauna ta yi idda a gidan mijinta matukar ba sakki uku ba ne. Don haka kuskure ne abinda matan Hausawa ke yi na barin gidan miji da zarar an sake su.
Sai sati na gaba insha Allah bayani na zuwa kan ladubban idda da kome; da fatan Allah Ya sa mu kasance a cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.