Don Uwargida: Lakanin Zama Da Miji (2)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama da maigidanta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.Abubuwan Da Allah Ya yi Umarnin A Tsare: Shi ne lakanin zama da miji na biyu […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama da maigidanta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Abubuwan Da Allah Ya yi Umarnin A Tsare: Shi ne lakanin zama da miji na biyu da ya kamata uwargida ta lakanta, don more jin dadin zama da maigidanta. Tsare gaibi shi ne, uwargida ta kasance mai tsare kanta da amanar mijinta a bayan idonsa, kamar yadda za ta tsare a gabansa; duk wani abin da ta sa na gabansa ba za ta iya aikata shi ba, to a bayan idonsa ma sai ta tsare amanarsa kamar dai yana nan ne. Haka tsare gaibi na nufin ta tsare amanarsa har cikin zuciyarta ba a fili kawai ba. Abubuwan da Allah Ya yi Umarni ga macen aure Musulma ta tsare suna da yawa, amma ga bayani kan muhimmai daga cikinsu:
Tsare Hakkokin Allah: Abu na farko kuma mafi muhimmacin da ya wajaba dukkan mace Musulma ta kwarai ta tsare shi ne, hakkokin Allah SWT: Wannan ya kunshi kadaita Shi wajen bauta, da yin aiki da sharuddan addinin a kowane bangare na rayuwa, da kiyaye ketare dokoki da iyakokin Allah SWT.
Yin aiki da dukkan abin da ya yi umarni da shi da kauce wa dukkan abin da ya yi hani da shi. Tsare hakkokin Allah a kan ki ya uwargida ba ya yiwuwa dole sai da ilimi, don fahimtar abubuwan da aka hane ki da abubuwan da aka umarce ki da aikatawa, kuma shi ilmi mun san kogi ne da ba shi da iyaka, don haka ya zama wajibi a gare ki ki kasance kullum cikin neman ilimin fahimtar addininki wanda zai taimaka miki wajen tsare hakkokin Allah SWT. Da fatan Allah Ya ba mu ikon dagewa da jajircewa wajen neman ilimin da zai amfane mu duniya da lahira, amin. Daga cikin abubuwan da Allah Ya yi umarni ga mumunai su tsare a cikin LittafinSa mai Tsarki sun hada da:
1. Tsare Sallah: Domin Sallah ibada ce maigirma wacce take sa da dan Adam da mahaliccinsa akalla sau biyar a kowace rana. Wannan ganawa tana saukar da damshi a ruhin dan Adam, kuma ta tsare zuciya daga aikata munanan ayyuka, kamar yadda Allah SWT Ya bayyanar cikin Alkur’aninsa.
Uwargida, a matsayinki ta macen kwarai, mai fatan samun cin nasara a rayuwar duniya da lahira, wannan shi ne, mafi girman abin da za ki tsare, don haka yana da kyawu ki dage wajen tsare sallah da gabatar da ita a farkon lokacinta. Kada ki bari harkokin kula da gida ko yara, ko al’amuran rayuwa na yau da kullum, komai tsanantuwar muhimmancinsu, su hana ki gabatar da sallah a farkon shigar lokacinta, ballantana har ki bari kananan abubuwa, kamar shagaltuwa da dadin hira ko wasu abubuwa marasa alfanu su hana ki tsayar da sallah. In kuma har kin yi sakaci yin ta ba a cikin lokacinta ba ya zama jiki a gare ki, to ya zama dole ki dage ki yaki shaidan, don ganin cewa kin tsare sallah kamar yadda Allah SWT Ya umarta.
2. Tsare Amana: Amana ita ce dukkan abin da aka yi yarjejeniya da shi tsakanin mutum biyu ko sama da haka. Rikon amana siffa ce ta macen kwarai, kuma tana daukaka darajar duk mutumin da ya siffance ta. Amanar farko da ya kamata uwargida ta dage wajen rikon ta ita ce, amanar da ke tsakaninki da Allah, wannan ya kunshi tsare dukkan dokokinSa da tsare dukkan abubuwan da Ya yi umarnin a tsare. Daga nan sai rikon amanar maigida, za ki rike amanar maigidanki, ta yadda duk abin da kika san za ki tsare a gaban idonsa, to a bayan idonsa ma haka za ki tsare; duk wasu dokoki da sharuddan da ya gindaya miki, dole ki yi aiki da su, lokacin da yake tare da ke da lokacin da ba ya tare da ke; kada maigida ya umarci ki yi wani abu, amma ya kasance idan yana gida ne kawai kike yin abin nan, ko ya hane ki yin wani abu, amma idan kin ga ba ya nan sai ki aikata abin nan.
Haka kuma yana daga cikin tsare amanar maigida kada ki bar kowa ya rika shige da fice cikin gidansa, sai wanda ya yi wa izini, kuma kada ki yi kyauta da wani abu na daga dukiyarsa sai da izininsa, kuma kada ki rika daukar wani abu daga cikin dukiyarsa don amfanin kanki ba tare da saninsa ba, matukar yana wadata ki da dukkan kayan bukatun rayuwa da addini ya aza masa nauyin ya wadata ki da su.
Haka kuma yana daga cikin rikon amana tsare sirrin maigida da boye laifukansa da rauninsa da rashin bayyanar da su ga ’yan uwa ko abokai. Da sauran duk wani abu da ya danganci rikon amana wanda yanayin zama ke kawowa. Uwargida ki sani, rikon amana da tsare amana, abubuwa ne da za su daga darajarki a gidan auren ki, kuma su kara miki kwarjini a wajen mijinki da wajen mutane gaba daya.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.