Don Uwargida: Lakanin zama da miji (3)
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama da maigidanta. Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, amin. 3. Tsare Alkawari: Wannan babban al’amari mai muhimmanci ne, wanda Allah Ya yi umarni ga mu’uminai su tsare […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama da maigidanta. Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
3. Tsare Alkawari: Wannan babban al’amari mai muhimmanci ne, wanda Allah Ya yi umarni ga mu’uminai su tsare cikin Littafinsa Mai Tsarki. Tsare alkawari na nufin cika alkawari a kan lokaci da yanayin da aka kulla shi ba tare da an rage ko kara wani abu a kai ba. Kiyaye daukar alkawarin da mutum ya san ba zai iya cikawa ko kiyaye ka’dojin da aka kulla shi a kai ba, shi ma wani bangare ne na tsare alkawari. Tsare alkawari dabi’a ce da ta dace da dukkan wata macen kirki mai son more rayuwar gidan mijinta da kuma son dacewa da more rayuwa a aljanna ranar kiyama in sha Allah. A matsayinki na uwargida, ga irin alkawurran da ya kamata kodayaushe ki kasance mai cika su da kiyaye su a tsawon rayuwarki:
1. Babban Alkawari: Alkawari mafi girma da ya kamata uwargida ki tsare sama da komai shi ne, alkawarin da ke tsakaninki da Mahaliccinki Allah Madaukakin Sarki! A matsayinki na Musulma, kin amince ki bauta wa Allah Shi Kadai ba tare da kin hada Shi da abokin tarayya ba; kin amince Annabi SAW bawanSa ne kuma manzonSa ne; wannan alkawari ne kika dauka na cewa za ki zama Musulma kuma za ki yi aiki da musulunci; don haka yin wani abu akasin wannan saba alkawari ne mai tsananin girma da muhimmanci na tsakanin bawa da Ubangijinsa. Don haka alkawari za ki fi dagewa da ba da kaimin ganin kin cika shi sama da sauran, idan kika cika wannan babban alkawari, Zai sawwaka rikon sauran alkawurran da ka iya bijirowa a tsawon rayuwarki. Da fatan Allah Ya ba mu ikon rikewa da cika wannan alkawari ba tare da kuskure ba, amin.
2. Tsare Alkawurran Aure: Aure wata yarjejeniya ce tsakanin ma’aurata da ta kunshi yi wa juna wasu hidimomi gwargwadon hali da yanayi; kuma ya wajaba ga kowane bangare na ma’aurata su dage ganin sun cika nauyin da ya rataya a kan su na alkawarin aure. Ga yadda za ki tsare alkawurran auren maigidanki:
• Tabbatar Masa Da Dukkanin Hakkokin Aurensa: Wadannan sun kunshi ba shi hakkinsa na ibadar aure a kowane lokaci da yanayin da ya bukata, bin maigida sau da kafa a cikin abubuwan da ba su saba wa Allah ba; tabbata cikin gidansa da rashin fita sai da izininsa, yi masa hidimomi da biya masa bukatunsa daidai gwargwadon hali, kokarin faranta masa rai a kodayaushe da kuma guje wa duk abin da aka san zai haifar masa da bacin rai ko damuwa.
Rashin aikata wadannan, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba karya alkawarin yarjejeniyar aure ne, don haka ya kamata dukkan wata Musulmar kwarai ta kiyaye wannan lokacin da take mu’amalantar maigidanta; ta sani alkawari babban al’amari da za a yi mata tambayoyi game da shi a ranar lahira ne, Kamar yadda Allah SWT Ya umarta cikin littafinSa mai tsarki:
“Kuma Ku cika alkawari, lallai alkawari ya kasance abin da za a tambaya ne” -17:34.
• Ki kiyaye Yardarsa: In har maigidanki ya yarda da ke a kan cewa ke mai kaza ce ko ba ki da kaza, to wannan yarda da ya yi miki aba ce mai tsananin tsada a gare ki, kada ki bari ta kufce miki, ki kiyaye ta sosai, kada ki sake ki aikata wani abu da zai goge wannan yarda da amincewa da ya yi miki cikin zuciyarsa. Idan ya amince miki da wata dabi’a ko ya shaide ki da wani kyakkyawan hali, kada ki yarda ki aikata wani abu da zai nuna akasin haka.
• Rikon Amana: Yana daga cikin cika alkawarin aure ga uwargida rikon amanar maigidanta komia runtsi komia tsanani: duk amanar da Maigida ya ba ki da dukkan wani amincewa da ya yi miki, ki daure ki rike amanarsa, kada ki rugutsa wannan amincewa da ya yi miki. Misali, idan ya hana ki yin wani abu, kamar ya hana ki da yawan shiga makwabta, ko leke, ko fita ba da izini ba, kuma kika amsa masa da ba za ki kara ba, kin karya alkawari ne sake aikata haka ko da sau daya ne kadai, kuma ba shi yiwuwa ki ce ba za ki daina ba, domin wannan ya zama rashin kunya da rashin ladabi.
• Tsare Sirrin Maigida: Lallai babban cin amana ne bayyanar da sirrin maigida ga wasu mutane komia kusancin su da ke ko da maigidanki; don haka idan maigida ya gaya miki magana, kuma kika tabbatar maganar nan ta sirri ce, to ko bai ce da ke ‘maganar nan amana ce ba’ kada ki yadda ki sanar da kowa ita, balle kuma har ya kawo sharadi ya sa miki cewa kada ki gaya wa kowa wannan magana, lallai yin haka ya zama babban karya alkawari.
Tsare Alkawari Wajen Mu’amula: Yana da kyawu uwargida ki kiyaye alkawari lokacin da kike mu’amula da mutane, tun daga ’yan uwa da abokai da makwabta da zuwa sauran jama’a. Ki dabi’antu da cika alkawari, ki dabi’antu da yin magana daya da rashin sauya magana, in kin yi alkawari da mutane na ciniki; na bashi; na sada zumunci; na kyauta, ki tabbatar kin cika wannan alkawari a yadda kika yi shi kuma cikin lokacinsa. Wannan zai kara miki aminci da daraja cikin mutane, kuma wannan shi zai kara dawwamar miki da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aurenki. Da Fatan Allah Ya ba mu ikon kiyaye alkawurran da suka rataya a kan mu a kodayaushe, amin.