Don zabi-sonka na fara aikin gidan rediyo- Halilu Ahmed Getso

Halilu Getso tsohon shugaban gidan rediyon tarayya na Kaduna ne, Wakilin Aminiya ya tattauna da shi, inda ya bayyana yadda ya yi gwagwarmayar a lokacin da yake aikin gidan rediyo, inda ya fadi nasarori da kuma kalubalen da ya fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka. Halilu: Assalamu […]

Don zabi-sonka na fara aikin gidan rediyo- Halilu Ahmed Getso

Halilu Getso tsohon shugaban gidan rediyon tarayya na Kaduna ne, Wakilin Aminiya ya tattauna da shi, inda ya bayyana yadda ya yi gwagwarmayar a lokacin da yake aikin gidan rediyo, inda ya fadi nasarori da kuma kalubalen da ya fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka.

Halilu: Assalamu Alaikum. Bismiillahir Rahamanir Rahim. Ni ina daga cikin mutanen da mukan ce ba mu san lokacin da aka haife mu ba. Ni sanda aka haife ni a lokacin nan babu wannan al’ada ta a rubuta sunan mutum, an haifi wane dan wane ran kaza ga watan kaza a unguwa kaza. Allah bai kawo wannan ilimin ba ko hikimar ko umarnin ba.
To ni dai daga baya na ji daga bakin iyayena, a kiyasin da na yi ina dauka an haife ni kamar a 1948. Ka ga yanzu ina da kamar shekara 66 ke nan. To amma yawanci a takardu abin da na fi rubutawa shi ne 1949 aka haife ni, dalili ni ba na son 1948, na fi son 1949 saboda mara ce. Ni kuma duk yawanci abubuwa mara na fi son su, domin Allah ma an ce Ya fi son su.
An haife ni a Getso kasar Gwarzo a daidai wannan shekara, na yi makarantar allo a hannun malamai kamar goma. Sannan da na isa shiga makarantar boko aka saka ni a makaranta, amma a lokacin nan ba a sa mutane da wuri. Ina jin a lokacin da aka sani ina da shekara wajen goma, a 1958 na fara karamar makarantar Firamare a Getso. Shekara 4 ake yi a lokacin, sannan a tafi babbar makarantar firamare. To ni ban yi hudu ba, uku na yi, sai na tafi babbar makarantar firamare ta Gwarzo, nan kuma na shekara uku.
Daga nan muka yi jarrabawa, Allah Ya ba ni sa’a na ci, kuma ina cikin waddanda aka dauka aka tura su Sakandire, a lokacin muna da makarantun gaba da firamare guda biyu ne kacal a duk fadin lardin Kano, da wacce ake kira Kwalejin Rumfa a yanzu da kuma Sakandire ta Birnin Kudu. To ni ta Birnin Kudun aka kai ni, shekara biyar ake yi, nan ma ban shekara biyar ba, na yi kamar shekara hudu da rabi. Daga nan kuma na fita, idan da da sarari jami’a na so in je, to amma gaskiya babu hali. Rashin halin shi ne babu wanda zai tsaya mini, mahaifina ya rasu, a hannun wansa nake tare da kannena da aka rasu aka bar mu.
Saboda haka sai ya rika gani kamar wancan karatu na Sakandire ya isa, a fito a nemi aiki saboda a taimaka masa. To na dai rarrashe shi, na ce masa a’a da ka ga jami’a nake son zuwa, amma tun da ka tsananta, bari in tafi wani wuri, ba jami’ar ba, ba kuma aikin ba. Sai aka zo za a dauki sababbin ma’aikatan da suka gama sakandire daga ma’aikatar gona, a lokacin marigayi Amadu Rufa’i ne babban jami’in gona na ma’aikatar ayyukan gona ta Jihar Kano.
To shi ya zo makarantarmu wajen daukar yara, kuma ni ma na nemi in shiga cikinsu. Sai aka tura mu kwalejin koyon ayyukan gona ta Samarun Zariya, muka je a 1969 dama karatun shekara biyu ne, to nan ma ban gama ba, sai na bar makarantar na fada aikin Rediyo. Na ga sanarwa a jarida ana neman wadanda suka yi karatun sakandire ko wadanda suka yi karatun horon malamai na matakin daraja ta biyu. A lokacin ana kiran gidan Rediyon da Rediyo Talabijin Kaduna, ko BCNN.
To ni kuma dama ina da sha’awar aikin Rediyo, amma sha’awata ita ce in je in gabatar da zabi-sonka. Yana ba ni sha’awa kuma ni na dauka masu gabatar da zabi-sonka manyan mutane ne, saboda muna jin su yau da kullum kuma suna burge mu. To da aka dauke ni sai kuma na ga ma mukamin da aka ba ni ya fi na ’yan zabe. Daga nan wasa-wasa abu ya ci gaba har sai da na kure na zama shugaban tashar Rediyon Najeriya na Kaduna, har ma na rike ofishin Legas, daga nan kuma na yi ritaya da kaina.
To a lokacin an dauke mu ne mu shida, da ni da aka turo ni Kano, ni ne wakilin gidan rediyon na farko a nan Jihar Kano, ina aika labarai da rahotanni da sauransu. An turo ni ne a lokacin marigayi Gwamna Abdu Bako a 1970. An dan yi mana ’yar horarwa aka feffeke mu, yadda za mu yi kaifi can, mu yi tsini nan, sai a farkon 1971 aka ce in je Kano in zauna a matsayin wakilin gidan rediyon.
Akwai Umar Faruk da ka tura shi Jihar Arewa maso Gabas, a Maiduguri; sai Muhammad Bashir Gulma, wanda aka tura Sakkwato, wakilin Arewa Maso Yamma. Tunde Oladipo kuma aka tura shi wakili a Jihar Kwara, sai kuma Shado Pkara, shi kuma aka kai shi Kaduna, a lokacin ba a raba ta da Katsina ba, a matsayin wakilin Arewa ta Tsakiya.
Ina nan Kano har na kai kamar shekara biyu, yau da gobe dai ana yi, wani abin a yi daidai, wani ba a yi daidai ba. Can Kaduna wani lokacin su ji labari mai dadi, wani lokacin su ji marar dadi. Ka san kowane ma’aikaci musamman idan kana karami, ba ka sanin abin da wasu za su je su fada game da kai. Wani zai ce “ai yaron nan naku yana kokari,” ka ga an kyautata ka, an yaba maka, wani kuma sai ya ce “kai ai dan iska ne, ba ma a ganinsa ma.”
Aminiya: Saboda kana fadar gaskiya?
Halilu: Ai a lokacin ba ka isa ma a dora a kan mizanin ko kana fadar gaskiyar ko ba ka fada ba. Wani kawai don ba ka zuwa ka gai da shi a ofis ne, sai ya je ya sare ka, shi ke nan sai a je a bada labari cewa “ai yaron nan naku…” ko “mai girman kai ne,” ko “ba a ganinsa a wurin aiki.”
Wata rana wata Asabar akwai wani abokina Allah Ya ji kansa, ana ce masa Gali Ahmad Daura, tare muka yi kwalejin aikin gona da shi. Ya gayyace ni daurin auren wani abokinsa a Kazaure, to ni ina da Babur, shi ba shi da abin hawa, na dauke shi muka tafi. Ashe ban sani ba a wannan ranar akwai wani biki da za a yi a Kano, wallahi ba ni da labari kuma Asabar ce ba ranar aiki ba, saboda haka na dauke shi muka tafi Daura daurin aure.
Wallahi sai ga labari ya je Kaduna cewa duk Asabar din duniya ina Kazaure. Ni kuma tun da nake a duniya idan ban da wannan zuwan da na yi, wallahi ban taba sanin Kazaure ba. Amma sai aka kai labari cewa duk Asabar din duniya ina Kazaure.
Aminiya: To so suke yi a dauke ka ke nan?
Halilu: To daga karshe an dauke ni, aka mai da ni Kaduna, a 1973 aka bar ofishin na Kano babu kowa. A 1974 kuma sai aka tura ni kasar Holland a yankin Netherland a wata makaranta da ake kiran ta “Cibiyar Horarwa ta Rediyo Netherland,” a wani kauye da ake kira Helbersom. A daidai lokacin kuma na rubuta wa Rediyo BBC ina so su dauke ni aiki, sai ga amsar BBC sun aiko sun dauke ni, ga kuma takardar kwas zuwa Holland daga wajen aikina. To a nan fa shugabannina suka ce sai dai in zabi daya, kuma idan na zabi BBC to na tafi ke nan, don ba za su yarda idan na gama da BBC na komo wajen aikina ba.
A kan haka na yi shawara, kuma shawara ta nuna gwanda na tafi wannan kwas din, domin shi mai wucewa ne amma aikin BBC yana nan ko daga baya zan iya zuwa. Saboda haka sai na fasa tafiya BBC, na tafi kwas. Bayan na je na gama kwas lafiya lau. To suna da wani tsari na ba duk wanda ya gama kwas damar za a biya masa ya zabi duk wata kasar Turai da yake so ya kai ziyara. Sai na zabi za ni Landan, na yi wa wani abokin aikina da ya samu zuwa can, Lawal Yusuf Saulawa waya, na ce zan je wajensa ziyara a BBC, sai ya ce “Ka taho.”
Na je Landan muka hadu da Saulawa na kwana kamar uku a can, muka yi zumunci da shi da sauran ma’aikatan sashen Hausa na BBC. Bayan na dawo Najeriya ne kuma, sai ake sake wani sabon tsari a wajen aikinmu, kuma zuwana Landan mun yi magana da shugabannin sashen Hausa, sai suka ce su dai suna da bukata in zo in yi aiki da su. Ko me ya sa suka tsananta dai ban sani ba, ni ma kuma ina son aikin. Ka san lokacin akwai yarinta kuma a wancan lokacin an dauki Ingila din wata aba ce. To sai na dauki alkawarin cewa zan je BBC in fara aiki, amma a shekarar 1976, shekara biyu bayan dawowata daga kwas na kasar Holland ke nan.
Sai BBC suka rubuto mini takardar daukar aiki, na tafi duk sanda na shirya. Na je na kai wa shugabanmu na sashen shirye-shirye na lokacin, marigayi Alhaji dahiru Modibbo, shi kuma Abba Zoru a lokacin shi ne Babban Manajan Zartarwa. Sai aka sake ba ni zabi ko dai in tafi BBC, shi ke nan na rabu da Rediyo Kaduna ke nan, ko kuma a bayar da ni aro na tsawon shekara daya da rabi ga BBC. Sai na dauki zabin na tafi a matsayin aro kuma na saka hannu a takarda a kan haka.
Da na je ma a daddafe na yi shekara daya da rabin, don har gani na yi ma ta yi mini yawa, na samu al’amura wadanda ba haka na zata ba. Fasalin rayuwa ba dadi, yadda ake rike ma’aikata haka da dan alamar wulakanci, duk sai na ji dai Ingilan ni ba ta yi mini ba. Saboda haka ban ma karasa shekara daya da rabin ba, saura kamar wata uku haka na baro can Landan. A taaaice dai da na dawo Kaduna a jefa ni can, a kai ni can a tsakani sashen shirye-shirye da na labarai, har Allah Ya kaddara na gama aiki.
Aminiya: Idan muka dauka tsakanin kwas da ka je Holland da kuma aikin BBC da gwagwarmayar da ka yi a Rediyo Kaduna dai aika rahotanni da ka yi daga nan Kano, wanne ne kake gani ya fi fito da kai, kuma ya fi ba ka gogewa?
Halilu: Zamana na Kaduna, ai ka ga zaman da na yi a Kaduna tun asali da ma sun nemi su dauke ni aiki, su ne iyayen gidana na farko, su ne iyayena na karshe ma. A dalilinsu na yi fice har BBC ta san ni, a dalilinsu har na tafi wancan kwas kasar Holland. Kuma zamana na BBC gaba daya in ban da ka fassara labarai a karanta, ko kuma a fassara jawabin bayan labarai, ai babu wani abu da muka yi. Shiri daya kawai na yi a can BBC. Na yi wani shiri da ake cewa da shi “manta sallah, mai rubutu a tsaye.”
Aminiya: Yaya wannan shirin yake? Kai kadai kake gabatarwa ko tare da wani?
Halilu: Ni da wani muke gabatar da shi. Ni nake rubuta jadawalin abin da tsarin zai kunsa, kuma tunanina ne da fahimtata kuma ilimina ne, idan kuskure ne ma nawa ne. To akan ba ni wani daga cikin ma’aikatan sashen Hausa mu gabatar tare. Wata rana mu gabatar tare da Ahmad Aminu, wata rana kuma da Bashir Sama’ila Ahmad.
Aminiya: Daga jin taken shirin kamar wani hannunka mai sanda ne. To shi shirin na fadakarwa ne ko na ilmantarwa ko kuwa na nishadantarwa ne?
Halilu: Babu abin da bai kunsa ba. Ya kunshi ilmantarwa da fadakarwa da kuma nishadantarwa. Jimlar gaba daya abin da na kunsa a cikin shirin shi ne fasalin rayuwar Turawa a kasashensu. Komai da komai da ka sani game da Turawa, shi ne wanda nake ba Hausawa da suke nan gida suna sauraron labari.
Aminiya: To yaya ka ga sha’awar masu sauraro ga wannan shirin, duk da yake a wancan lokacin watakila babu buga waya daga masu sauraro, sai dai su aika da wasiku?

Cigaba a shafi na 5

Halilu: To kamar yadda nake ji haka a boye, an rubuta takardu na masu sauraro, wasu daga cikin Turawan da muke tare da su suna gaya mini cewa ba a taba yin shirin da ya samu yawan wasiku daga masu sauraro irin wannan shirin da na yi ba. Amma kuma ya hada ni rigima da wadansu don ta kai matsayin da wani daga cikin Turawan, ya je ya sare ni a wajen shugaban sashen Afirka ma gaba daya ba na Hausa ba.
Shi kuma shugaban sashen Afirka ya dauki maganar ya kai ta ofishin Ministan labarai da kuma Ministan al’amuran cikin gida. Daga karshe sai da aka zo aka dauki wasu daga cikin shirye-shiryen guda 13 da na yi, aka fassara su da Turanci. Shi wanda ya je ya sare ni din aka ce ya fassaro ya kawo. Ya fassara ya je ya kai, ga na Hausa, ga na Turanci. Aka je aka duba, sannan aka dawo da shi aka ce ba a ga wani aibu ba, don haka in ci gaba. Amma shi ya je yana fadar cewa ina cin mutuncin Turawa, na ci zarafinsu.
Aminiya: Kai kuma kana yi ne don ka ba sauran masu sauraro da ba su je Turai ba, don su ji yanayin yadda Turawa suke rayuwarsu, su samu nishadi?
Halilu: Ina fadakar da mutane yadda suke tunanin Turawa na yin abubuwansu, to ba yadda suke tsammani ba ne. Kuma Allah na tuba dan Adam ne ba ya so a fadi aibunsa. Amma da yawa daga cikin abubuwan da na fada ai akwai inda nake cewa “mu karyar Musulunci muke yi,” amma idan ka je Turai kamar yadda kai ka sani, wani abin za ka ga cewa Musulmi ma da suke kiran kansu Musulmi ba sa yin haka. Akwai cika alkawari, akwai tsare lokaci, akwai rikon amana, akwai kuma gaskiya.
Wani lokaci ma mutum laifi zai yi, shi da kansa zai zo ya ce “ni ne na yi.” Na fadi wannan ba daya ba, ba biyu ba, kuma na ba da misalai da yawa. Har na bayar da misali da inda na je na yi sayayya, na ba da kudin takardu aka yi lissafi abin da na saya da kaza da kaza, sun kama kaza. Aka ba ni canji tsaba, canjin nan da aka ba ni sai ya gaza da anini daya. Amma bayan kwana 7 na sake komawa wannan shagon zan yi sayayya, tarar da aninina an saka shi a takarda, an nade an ajiye. Ina zuwa aka ce “kai ne ka zo nan ka sayi abu kaza da kaza rana ya ta yau?” Na ce “ni ne,” suka ba ni aninina.
Aminiya: Akwai kuma wani shirin siyasa da ka sahara da shi a nan gidan Rediyon Kaduna. Ka samu gamsuwa da wannan shirin, kuma yaya karbuwarsa wajen jama’a?
Halilu: To ni gaskiya duk wani shiri da na yi, ba na yin sa don in ji ni da kaina na gamsu. Ni dai ina yin iyakacin kokarina, na yi shirin yadda idan ya fito, masu sauraro idan suka ji za su ce Alhamdulillahi, mun amfana. Idan akwai abin nishadantarwa a ciki, su ce an nishadantar da su. Idan akwai abin ilmantarwa a ciki, su ce sun gode, an ilmantar da su. Idan akwai abin nasiha a ciki, su ce “Eh mun ji wannan nasihar kuma mun dauka.” Amma ni ban taba auna wani shiri a sikelina na kaina na ce na gamsu da shi ba. Don ba don gamsar da kaina nake yin shiri ba.
Aminiya: A irin siyasa ta wancan lokacin, yaya shirye-shirye biyu da ka yi na “Dandalin Siyasa” da na “Alkawari kaya ne,” wane kalubale ka fuskanta wajen gabatar da su, ganin akwai wayar da kan talaka da yiwuwar bakin jini a wajen mahukunta?
Halilu: Sanda na dawo daga BBC a 1977 ai wani shirin na fara yi, kafin wadannan guda biyun. A lokacin ne aka kirkiro wasu sababbin shirye-shirye, kuma ni sai aka ba ni na siyasa, cewa in gabatar da shi, don in rika wayar da kan mutane a kan siyasa. Duk da cewar da na yi ba ni da cikakkiyar masaniya da siyasar lokacin Sardauna, aka ce in rika zuwa ina hira da dattawa da suka yi lokacin Sardauna don in gabatar da shirin. Domin a lokacin sojoji na shirin mayar da mulki a farar hula, don a tuna wa jama’a harkokin siyasa.
Da na tashi sai na saka wa shirin suna “Mece ce siyasa?” Na zagaya garuruwa na yi hira da mutane, kamar nan a Kano na yi hira da mai girma Magajin Garin Kano, Alhaji Inuwa Wada. Na yi hira da Sarkin Fadar Kano, Alhaji Sule Gaya da dan Masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule da su Malam Aminu Kano, su marigayi Alhaji Lawan Dambazau da Sabo Bakin Zuwo. A Daura na yi hira da marigayi, mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Muhammadu Bashar. A Bauci na yi hira da irin su marigayi Ibrahim Tahir, su Dimis dan Sardauna. A Neja na yi da wani ana ce masa Alhaji Muhammadu, ba zan iya tuna daya sunan nasa ba. Bayan an gama wannan ne kuma muka zo kan “Dandalin Siyasa.” An fara shirin ne a lokacin soja sun cire takunkumin da suka yi wa ’yan syasa. An bada dama a je a kafa kungiyoyi su zagaya su nemi jama’a, kafin su zama jam’iyyu. Wakilanmu na garuruwa suna aiko da rahotanni na siyasa muna sakawa. Haka muka yi ta tafiya, har aka zo aka shiga fafatawa a fagen neman mutane da kuri’a, har dai aka yi zabe aka bayyana wadanda suka ci zabe.
To an gama wannan, ka ga ya kamata a ce ni aikina ya kare, sai kuma aka ce ai kuma yanzu bai kamata in yi shiru ba, na zo na kirkiro wani shirin da zai sake tafiya da wadannan ’yan siyasa don bibiyar alkawuran da suka yi wa mutane a lokacin yakin neman zabe. To sai in zo da shirin “Alkawari Kaya Ne.”
Aminiya: Mene ne bambancin shirye-shiryen siyasa da ake yi yanzu da irin wanda ka gabatar a wancan lokacin?
Halilu: Akwai bambancin da yawa. Na farko su ’yan siyasa su ne suke tafiya da gishirinsu da yajinsu da mansu a fagen siyasa, inda za a je a yi lacca ko makamantan haka, ko a yi wasu hikimomi na siyasa. A yau yawanci ba ’yan siyasa muke da su ba, munafukai muke da su, maciya amana da kuma sarakan fadanci. A ce wai mutum yana Gwamna kai kana kwamishinansa idan za ka shiga ofishinsa sai ka cire masa takalma. Wane ne shi? Gwamna! Kuma ka shiga yana kan kujera, kai ka lafe ka kwanta a kan shimfida. Ai ka ga wannan ba siyasa ba ce, mulki ne wanda ba a yi shi ba a wancan lokacin.
Bayan haka ita siyasa ’ya’yanta ne suke tallarta, suke sayar da ita. Yanzu yau duk fadin Kano ka kawo mini mutum daya wanda za ka ce ya iya karya lafazi, ya yi maganar da za ta jawo hankalin mutane irin marigayi Sabo Bakin Zuwo ko Lawan Dambazau ko Abubakar Rimi. Duk wadanda muke da su yanzu yawanci Bebaye ne. Ko kuma a Katsina ka kawo mini wanda zai kamo kafar Musa Musawa; babu shi. Duk dai ana yi ne kawai, sai kuma kowanne da irin zamaninsa da yadda Allah Yake kawo shi. Shi ne na ce maka siyasa yanzu ta tashi daga siyasa ta koma cin mana da cin mutunci da bambadanci. Ai idan dai siyasa ce wacce na sani ake yinta ta rediyo, an yi ta ta kare, ta tashi.
Aminiya: Wato wannan yana kara armashi?
Halilu: Abin ai ba a ma fada. Ai shi ya sa na ce da kai an daina siyasa yanzu, fadanci ake yi da rashin kunya kawai. Wannan illar ta siyasa ta shafi gabatar da shirin siyasar shi kansa a waje da yawa. Kuma in ka tuna tun dazu na fada maka fa cewa idan kana sauraron gidajen rediyo a yanzu ko na kasashen waje ko na cikin gida, ka san cewa aikin rediyo fa yanzu ana yi ne kawai don a ci abinci. Amma ba a yi don kishin harshen, domin ba yin amfani da harshen a yadda yake. Haka a lokacin da aka yi hadarin jirgi ya yi barin mai a teku a watannin baya, sai na ji wani yaro a wani rediyo yana labarai yana cewa wai masu kamfanin man sun ce za su wanke teku, inda aka yi barin man. Sai na yi masa waya na ce da shi “tun da nake ban taba jin inda ake wanke teku ba, don Allah Ya ba ni labarin yadda ake yi.” Har gobe ban samu amsa ba.
Ka ga Hausar ma ba ta ishe shi ba. Ga su nan da yawa sunayen garuruwanmu da na mutane da na unguwanni, ba ma iya fada daidai. Kai hatta abincin da muke ci a kasar Hausa, da yawa ga yaranmu nan suna aiki a gidajen rediyo, ba su san su ba. Kana maganar abinci sai ka rubuta “Wasa-wasa,” sai yaro ya ce maka “wasa-wasa.” Kuma ba zai tambaya ba, kai zancen abinci fa kake yi. To misali ne wannan kawai na ba ka. Haka ita ma siyasar ta yanzu da ka ji ta ka san wadanda ba su nakalci siyasar ba ne suke yinta, lami salam babu gishiri babu yaji, idan kana so ka ci sai ka dan zuba mata gishiri ko yaji.
Aminiya: Yaya aka yi ka shugaban gidan Rediyon Tarayya na Kaduna?
Halilu: Yardar Allah kawai, haka Allah Ya kaddara. Ai na gaya maka dazu na ce burina bai wuce idan na je gidan rediyo in gabatar da zabi-sonka ba. Ka ga ban tafi da buri mai yawa ba, ko kuwa in je nema ina zuwa wurin kuma da yardar Allah sai na karke na tashi da masaki a hannuna. Ni dai na san na yi aikina gwargwadon iko, duk abin da aka sa ni. Wanda ba zan iya ba ina cewa ba zan iya ba ku ba ni wani. Wanda zan iya ko ba a ba ni ba, sai in nuna ina so a ba ni in yi. Da haka na zauna tun ina mataimakin mai tsara shirye-shirye. Abin da aka fara dauka ta a kai ke nan, kuma albashina a wata yana daidai da Fam 25 ko daidai da Naira hamsin din yau. Da haka na yi ta samun daukaka har na kure.
Aminiya: Ka dade a aikin jarida me ka samu dalilin aikin Jarida?
Halilu: To na tsira da abubuwa guda uku zuwa hudu ko biyar. Na farko na shiga da mutuncina kuma ina kyautata zaton na fita da shi. Da mutuncina da na addinina da na iyayena da suka haife ni. Saboda har na yi na gama, babu wanda ya taba kawo kara gidanmu cewa wane danka ya yi mana abin da ba daidai ba. Na biyu duk gatan da wani aiki zai yi wa mutum a duniya aikin rediyo ya yi mini. A ciki na yi aurena na farko da na biyu da na uku da ma na hudu. Na shiga daga ni sai matata daya, na fita ina da mata hudu, kuma ina da ’ya’ya ashirin da wani abu. Kuma a nan na fara samun damar tafiya kasar Saudiyya na sauke farali, inda na je Saudiyya har sau goma sha wani abu, a tsakanin aikin Hajji da Umrah.
Kuma duniya iyakar inda dan Adam yake son zuwa ke nan. karyar dan boko a Najeriya ya ce ya je ya ziyarci Ingila. To ni ba ziyara na je ba, aiki na je na zauna a cikinta har shekara daya da wani abu. Idan ka yi nan yamma na je Amurka. Idan ka yi nan gabas na je har Sin (Chaina). A nan kudu kuma na je gabar Tekun Atalantika, na je Afirka ta Kudu.
Sannan kuma na je da burin in yi zabi-sonka, sai kuma na zama ni ne ma shugaban kowa da kowa, har masu zabi-sonka din. Kuma ya zama ba iyakacina Kaduna ba, har Legas an kai ni a matsayin babban Daraktan Zartarwa. Haka na dawo Kano na yi Daraktar Gudanarwa a Rediyon Jihar Kano. Saboda haka ni a wurina biyan bukata ba shi ne ka fita da mota da gidaje da kudi ba. Wallahi ranar da na rubuta na bar aiki, ba ni da Naira dubu 40 tawa a duk duniya, kuma motata tsohuwa ce.
Amman na fita ina jin dadi a cikin zuciyata, kamar yadda ka zo ka same ni yanzu ina cikin gonata. Ka ga wannan zaman, idan za ka ba ni miliyoyin kudi don ka raba ni da zama a wannan gonar ba zan iya barin sa ba. Ya fi mini kwanciyar hankali, babu mai bi na bashi kuma ni ba na bi. Kuma idan na je wuri, ina yin na Dila. Idan na ga abincina a wajen da ba safai ake samunsa a wajen ba, to ba na zuwa. Saboda ba na son abin da zai taba mutuncina.
Aminiya: Mece ce shawararka ga ’yan baya, ma’aikatan rediyo da sauran ’yan jarida na yanzu?
Halilu: To ka san tushen kowane aiki na duniya, ko aikin kwashe kashi za ka yi, to ka je ka nakalce shi a wajen wanda ka tarar yana yi. Babu abin da yake cutar da aikin rediyo a yau, illa abubuwa guda uku. Na farko yaran da ake dauka suna aikin rediyo hori suka yi ba su gasu ba. Idan gasawa ake yi, ba su gasu ba. Idan dafa wa ake yi, danyu ne ba su dahu ba. Idan nuna ake a jikin reshe, to su ba su nuna ba aka tsinko su. Yaro ne bai san komai ba, bai iya komai ba, sakandire ya yi, ko ya yi Gired-tu ko ya yi Difloma a aikin jarida, sai ya fito yana hura hanci. Kana daukar sa kana saka shi a gidan rediyo, abu na farko da zai fara so shi ne a ji sunansa. Yau ga wane a gidan rediyo yana magana, kun ji ma yanzu ya fada mana sunansa. Tallar suna da son iyawa da gwadare. A jimla daya sai yaro ya hada karin magana biyu ko uku amma duk ba su da alaka da juna. Sai a fadi karin magana a gabar da ba ta dace a inda bai dace ba, kuma ba a daidai ba. Sannan kuma akwai girman kai na kin yin tambaya.
Da Hausar da komai ma bai ishe su ba. Yanzu da yawa yaran da suke aikin Rediyo a nan kasar, wadanda ake dauka, ko abin da ake kira ilimin sanin kasa, ba su sani ba. Muna nan yanzu da kai yaro zai nuna inda dambatta take, nan zai nuna (Kudu). Ka san kuwa ba nan wajen take ba ko? To idan ana magana sai ka ji ya ce “wata rana na je nan dambatta.” Kai daga ganin wannan ka san bai san dambatta ba, bai san inda take ba. Ai da kunya kana Bakano, kana zaune a Gwarzo, za ka nuna inda dambatta take, kuma ka nuna Kudu. To irin wannan girman kan ga shi ba karatu, ko na jaridar nan ma da ake bugawa yau da kullum, ta Hausa da ta Turanci, yaran nan ba sa kokarin karantawa. Kuma akwai ilimi mai yawa a ciki. Duk inda ka kai da sanin wani abu, wallahi idan kai ma’abucin karatun jaridu ne da littatafai yau da kullum sai ka tarar da abin da ba ka sani ba, ko a jaddada maka sanin abin da ka sani. Yaran yanzu babu ruwansu ba sa yin wannan.
Sannan na uku hakuri. Wanda duk ba shi da hakuri a al’amarin duniya to karshenta za ka ga rabonsa ba shi da yawa. Suna da ci da zuci yaran yanzu. Sauri suke gaf gaf gaf. Jiya-jiyan nan yaro yana makaranta, bayan ya gama ya fito da wata hudu, jihadin da yake yi shi ne a gan shi da mota. Bai tsaya ma ya koyi aikin ya yi shi yadda ya kamata ba, amma kulle-kullen da yake yi, shi dai ya yi mota dai. A gan shi dai a ce “yau wane shekararsa daya da kama aiki, ka ga har ya yi mota.”
To wannan yana daga abin da yake cutar da kowane aiki, kamar yadda na fada maka. Ba aikin rediyo ba ko aikin kwashe kashe, wallahi sai an saka wata godiya da wadatar zuci. A rika ba zuciya hakuri ana taka mata birki. Can kake so ka je? Tafi a hankali, ka daina garaje. Idan Allah Ya yarda za ka je.