dora Ali Sherif a shugabancin PDP zai karasa jam’iyyar – Yerima Abdullahi
Wani dattijo a Jam’iyyar PDP daga Jihar Gombe kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Malaysiya, Ambasada Ibrahim Yerima Abdullahi, ya ce dora tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sherif a matsayin shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa koma baya ne ga jam’iyyar.Alhaji Ibrahim Yerima Abdullahi, wanda har wa yau shi ne Sarkin Bai na Gombe […]
Wani dattijo a Jam’iyyar PDP daga Jihar Gombe kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Malaysiya, Ambasada Ibrahim Yerima Abdullahi, ya ce dora tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sherif a matsayin shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa koma baya ne ga jam’iyyar.
Alhaji Ibrahim Yerima Abdullahi, wanda har wa yau shi ne Sarkin Bai na Gombe ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe inda ya ce a matsayinsa na dattijo a PDP kuma mai kishin jam’iyyar bai kamata a ce mutane suna sane da zargin da ake yi wa Ali Sherif, amma su yarda ya zama shugaban jam’iyyar.
“Ya kamata a samu mutum kwarrare mai gwazo wanda ya cancanta ya shugabanci Jam’iyyar PDP ba irin Ali Modu Sherif ba wanda ba asalin cikakken dan PDP ba ne, rana tsaka ya shigo daga wata jam’iyyar,”inji Yerima Abdullahi.
Ya ce yaushe ne ya baro Borno ga kuma abubuwan da suka faru a Borno da ake zargin a dalilinsa aka yi ta yake-yaken Boko Haram sannan a ce yanzu shi ne zai zama Shugaban Jam’iyyar PDP, jam’iyyar mutanen Najeriya, kuma su yarda.
Jakada Yerima Abdullahi, ya ce yana da kyau mutanen Najeriya su gane fa duk wahalar da aka sha a wannan shiyya ta Arewa maso Gabas da Najeriya kan rikicin Boko Haram ana zargin cewa Ali Sheriff ne sila ko da hannunsa a ciki.
Ya kawo misali da zargin da ake yi masa cewa bayan kulle filin jirgin saman Maiduguri, an hana kowa sauka da tashi ciki har da Gwamna mai mulki amma da yake na kusa da tsohon Shugaban kasa Jonathan ne aka ba shi dama har sau biyu yana sauka da tashi.
Sai ya yi amfani da wannan dama wajen jan kunnen ’ya’yan Jam’iyyar PDP cewa idan har suna son su sake cin zabe nan gaba, to su nemi mutumin arziki mai kima ya zama musu shugaba.